page 41&42

15 0 0
                                    

*MATAR DA ZAN AURA*
    BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7

Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

Page 41&42

__________📲Sai da yaga tashin jirgin da Granny ke ciki sannan ya koma zuwa Asibiti.

Yana shiga d'akin da Annur yake, ya tarar ya tashi daga baccin, Abida na ta fama da shi akan ya sha tea da ta had'a masa amma ko inda take tsaye bai kalla ba.

Mustapha ya d'an dad'e a bakin k'ofar Yana kallon su, Abida na ta faman rok'on sa ya amsa ya sha , da ya gaji ma sai ya saka fuskarsa cikin kafafunsa.

Lokacin Mustapha ya k'araso bakin gadon.

Tea d'in ya amsa daga hannun Abida ya zauna gab da Annur d'in, yace "Haba uband'aki na, d'an uwana Kuma k'anina da nake tsananin k'auna, dan Allah ka taimaka ko kad'an ne kasha".

Da k'yar Annur ya bud'e baki yace "I want to be alone, please leave".

Murmushi Mustapha yayi yace "Ok ba damuwa idan hakan zai faranta maka".

Tashi yayi ya kalli Abida yace "Muje na sauke ki gida" ya wuce ta bishi a baya.

Sai da suka biya ta office d'in likita Mustapha ya fad'a masa suna son sallama a yau don gobe Annur na da jarrabawa.

Likita ya tabbatar wa da Mustapha cewar hakan ba zai samu ba, Sai dai yaje makarantar ya musu reporting.

Godiya suka masa sannan suka tafi.

Mustapha tuk'i yake cikin nutsuwa yayin da Abida ke zaune a gefenshi ta kafe shi da Idanu.

Sun d'au lokaci a haka  Mustapha "Yace kallon fa", Abida tace "Ba kallon so bane na mamaki da Kuma takaici ne"

Murmushi yayi yace "Da na miki laifin me?"

Abida tace "Kafi kowa sani ai, na samu nagartattun mutane zasu aure ni amma saboda bak'in cikin kar na bar ka a k'angin bautar Hajiya, shine ka korar min su, na samu wani a garin mu kabini har can ka rushe d'aurin auren, Allah kad'ai yasan ya kayi".

A daidai lokacin da ya yi parking a k'ofar makarantar su Annur, juyawa yayi ya kalle ta sannan yace "A ganinki ni ba nagartacce bane ko"

Sauke kanta tayi k'asa don Mustapha ba k'aramin kwarjini yayi mata ba " Ni ba haka nake nufi ba"cewar Abida

Mustapha yace to me kike nufi ina sauraren ki.

Abida tace "bana jin dad'in Sai na samu saurayi na fara  son shi sannan ka raba ni dashi"

"Har yanzu zuciyar ki bata San mene so ba".

Abida dagowa tayi ta k'ureshi da Idanu.

Mustapha yace "Abinda na fad'a haka nake nufi, domin duk wanda yayi miki tayin soyayya amsar shi kike shi ko so mutum d'aya rak yake amsa".

Mustapha ya bud'e mota yace ki jirani a mota ina zuwa sannan ina so ki zauna ki nutsu ki fahimci bayani na".

        *******************

Zaune suke a falon, su biyu suna hutawa bayan sun gama gyara gidan tsaf, Mama tace " Dama haka taro yake ko ina Sai ya b'aci",

Anty Maryam tace Ai kad'an ma ne wannan".

Mama ta sake cewa "Maryam nagode da kika bani masauki a gidan ki har kika ban damar nayi taro, Allah ya bar zumunci, ki taya ni yiwa maigidan ki godiya".

MATAR DA ZAN AURAWhere stories live. Discover now