page 65&66

10 0 0
                                    

*MATAR DA ZAN AURA*
    BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7

Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

    
Page 65&66

__________📲"Me Kika je yi a banki, ba na hana ki fita  ba izini na ba, kina d'aukar abin wasa ko"

Abida bata sake magana ba.

Key yayi wa motar ya bar wajen, a tunanin ta gida zasu sai taga sun d'au wata hanyar daban.

"Annur ina zaka kai ni, dan  Allah kayi hak'uri na maka alk'awarin ba zan sake zuwa ko ina ba sai da izinin ka, yanzu ma tsautsayi ne da kuskure kuma zan gyara".

Annur shiru yayi yana sauraren ta bai ce komai ba sannan bai chanja hanya ba, sosai Abida ta sa kuka wanda hakan ya tab'a masa rai, at the same time ya basa dariya, parking ya sake yi a gefen titi a karo na biyu, sai da ya Gama had'iye dariyar sa sannan ya hade rai ya juyo ya fuskance ta yace " kina So na, kin amince zaki min biyayya ki haifa min yara masu hali irin naki".

"Na amince zan ma biyayya don Allah ka maida ni gida Annur".

"Amsa d'aya ki ka ban, alamu sun nuna har yanzu ba soyayyata a zuciyarki".

"Allah Ina son ka" cewar Abida dake faman goge hawaye.

"Masha Allah ba ki tab'a ban amsa me dad'in wannan ba amma fad'amin yaushe kika fara so na ko kin fad'a ne don na maida ki gida".

            ***************

Mustapha yace "Baby kina jina"  "Ina jinka Yaya Mustapha Umarni kawai zaka bani na K'addamar" cewar Baby.

"Me kike yi yanzu".

"Ina kitchen Hajiya nake had'awa abinci, kasan yanzu ta maida ni cook d'in ta tunda Annur yayi rejecting d'ina, kasan fa Yaya Mustapha cewa tayi ba zata iya cin abincin kowa ba idan ba nawa ba". cewar Baby

"Ok yayi kyau poison din nan da muke ajiya lokacin su yayi, kina ji ki ajje a kusa idan na sake kiranki to zan baki Umarnin ki zubawa Hajiya a abinci idan kuma ban kira ba nan da minti goma to ki k'yale ta kar kisa kin ji".

"To Yaya Mustapha sai abinda kace" cewar Baby

Mustapha na kammala waya ya juyo ya kalle su, gani yayi har sun saki Saif yana zaune gefe yana maida numfash. Murmushi Mustapha yayi yace "Malam accountant.
Kasan  abinda ke faruwa nasan sirrinka in and out Rabi kishiyar Maman Daddy da kake wa aiki ita ma amanar ka take ci, da ka gama biya mata buk'atar ta zata sa ai mata maganin ka don zata manta da cewar kai din cousin d'in ta ne".

Daga Daddy har chief accountant babu wanda gaban sa bai fad'i ba ambaton sunan Rabi da Mustapha yayi taya akai yasan komai.

Tashi tsaye Mustapha yayi ya fara zagayen d'akin can ya kalli accountant yace "kana mamakin ya akai na san wannan sirrin ko, to ka bud'e kunnen ka da kyau ka ji, Rabi bata yarda da kai d'ari bisa d'ari ba tana da kokonto akan ka don haka itama take binciken sirri akan ka a binciken nata ne ta samo ni, ni ban san kowa a familyn daddy ba sai yanzu a dalilin Rabi".

" Rabi ta fad'a min cewar ita ta samo maka Hajiya Naila ka aura, kuma wannan sakin da kai ma Hajiya Naila ta sanar da ni cewar duk ita ta baka plan d'in".

"Yanzu kuma kun gama morar Hajiya Naila itama signing d'inta kawai kake buk'ata na dukiyar da ke hannunta sai ku haukata ta daga nan sai ku raba dukiya kai da Rabi kaje ka auri masoyiyar ka mai jiranka inspector Aziza wadda kake tunanin zata zama garkuwa a gareka".

MATAR DA ZAN AURAWhere stories live. Discover now