matar da zan aura 11&12

33 1 0
                                    

*MATAR DA ZAN AURA*
    BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7

Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

        Page 11&12

___________📲Ba k'aramar nutsuwa bace tazo mata lokaci guda "Alhamdulillah! Allah na gode maka da dukkan jarabawar ka akai na, Allah ka bani ikon cinye wannan jarrabawa taka", iya abinda ta iya fad'a kenan ta juya ta nufi d'akin da take, ta shirya mu ta d'auko hijab d'inta tasa muka fito tsakar gida.

Baba ne ya mik'a mata takardar sakin ta tasa Hannu ta amsa ta d'au k'anina ta kama hannuna.

Baba yace "Ina zaki dasu?  ki ajje min yarana, Anty dija tayi saurin cewa "Da kabar mata k'aramin kasan k'ananun yara sai da uwarsu, Idan yayi wayo sai ka amso shi"
"To shikenan" ya fad'a tare da shigewa d'akinsa.

Ina kuka haka Mama ta tafi ta barni cikin wahala, babu irin aikin da Anty dija bata sani har wanda ma yafi k'arfi na ga bana samun isashshen abinci

Makaranta kam tuni ta cireni tace wa Baba kaina baya d'aukar karatu, yanzu ta k'arshe nake a ajin mu,

Ya barni in zauna a gida ta koya min sana'ar dogaro da kai shi yafi,
a haka babana ya amince

Kullum ina yawon aikenta lungu da sak'o, duk na rame nayi bak'i nayi datti, ina yin sati banyi wanka ba wani lokacin wannan matar da take zuwa amsar kud'in aikina, ita ke sakani nayi wanka a gidan ta.

k'awar Anty dija ce amma tana tausayi na sosai, tana ganin rashin imanin Anty dija yayi yawa

Saboda haka ne ma tayi mata wayon a sama min aikatau,tana ganin gidan aiki idan na dace sai ya fi min kwanciyar hankali.

Kuma gaskiya ce ta fad'a tabbas nan d'in yafi min, saboda na huta da dukana da take kullum sannan ina cin abinci anan har na k'oshi.

Wata rana da safe matar nan tazo gidan mu ina ta faman wanke-wanke ko karyawa banyi ba, Anty dija na kan tabarma tana shan tea, matar sunanta Binta ta kalle ni hawaye ya cika mata ido tayi saurin had'iye wa.
  Waje ta samu ta zauna, suka gaisa take cewa "k'awata ta samu fa"
"ke dan Allah fad'a min ina jinki"
"Ina matar nan makwabciya ta da nake baki labari to tana neman yarinyar aikatau amma tace min wai kula da yaron ne, kin ga kamar reno, tace min dubu ishirin ne a wata za a ke biya, sai naga ke ya dace ki samu wannan kud'i amma yarinyar nan taki kamar ba zata iya raino ba.

"Anty dija tace tab ai wallahi dolenta sai ta iya zata je kam kuma tayi shirme su korota wallahi yanka ta zanyi"

"Duk hirar da suke ina wanke-wanke amma hankali na gaba d'aya yana wajensu, ina jin wannan na saki fitsari a jikina saboda tsoro"

Anty binta tace "zata iya ma shine dalilin zuwa na domin na bincika ba k'aramin yaro bane zai kai shekara 9"

"Aiko jariri ne sai taje dubu ishirin wasa ce"

"to shikenan k'awata yanzu nawa ne kaso na"
"zan baki dubu biyu duk sanda aka kawo min kud'in aikin nata"

"Gaskiya k'awata ban yarda ba dubu biyar nake so in kin amince, in Kuma ba haka ba shikenan"

Anty dija tace "dad'ina da ke kin fiya son k'udi amma shikenan na amince a haka" "to yayi ki sanar da babanta gobe matar zata tafi da ita amma zan bita inga waje"

"Ai ko yanzu ne suna iya tafiya shi babanta ba wani ruwan sa ko bai sani ba, ba wata damuwa, ke kuma mene naki aciki da zaki wani je ganin waje, yarinyar shekara sha biyu har sai an bi diddiginta, barta ta tafi tayi ba daidai ba na d'au kwa'kwa'ran mataki kanta"

" Ke k'awata ni kud'in mu kawai zan bi kin san idan na bar ta tana amsowa ita sai ta cuce mu"

"Kuma fa haka ne k'awata kin yi tunani mai kyau, Allah ya kaimu goben"

"Amin" tace tare da yi mata sallama ta tafi.

Ina kammala wanke-wanken na shiga band'aki na gyara jikina naje kitchen bayan k'ofa na d'au wasu kayan na canja cikin sauri,dama tunda Mama ta bar gidanmu Anty dija ta maida ni kitchen, kwana ma anan nake.

Washegari da yamma Anty Binta tazo ta tafi dani gidanta, bayan ta bani abinci naci, tayi nasiha akan hak'uri da rayuwa duk yanda tazo min tace kuma na kasance me gaskiya a dukkan al'amura na zan samu ribar rayuwa a gaba, sannan tace, dubu biyar da zata ke cirewa a albashi na zata ban dubu uku saboda bukatuna kuma saboda ni tace dole Anty dija zata ke biyanta, dubu biyu Kuma ita zata rik'e saboda kud'in mota, godiya nayi mata sosai, tace "ba komai shi d'a na kowa ne"

A gidan Anty Binta na kwana, da safe bayan na karya matar tazo na d'auki ledar kayana, muka je tasha muka hau mota.

Shine Asalin zuwa na nan gidan, lokacin da aka kawo ni kina falo kin san komai.

Batun koyon girki kuma
Lokacin da nake raka Annur makaranta, wata ranar haka muke tafiya bamu karya ba, to idan anyi break yana amso kud'i a wajen malamin su amma ni ban san mutumin ba, naji dai yace abokin dadyn sa ne kuma dady ke bada kud'in ana bashi duk lokacin break.

Haka Annur ke saya mana snacks muna ci, bani kad'ai ba har da wata Sajida 'yar class d'in su ce tare muke ci, tana kawo nata lunchbox da take zuwa dashi amma Annur baya son tana zuwa wajen mu,ni kuma sai naji ina k'aunarta.

Saboda halin sa d'in nan na share mutane ba wanda ke kula sa ita kad'ai ce ke bibiyar sa ganin ta iya hak'uri da halinsa shiyasa nake sonta.

Idan Annur bai ci abincin ta ba ni ina ci a haka ya hak'ura yayi joining d'in mu.

Annur na shiga SS1 suka raba class da Sajida, shi Science class ita kuma Commercial class, a class d'in da Annur yake yayi wani friend mai suna Haisam shine wanda yake zuwa gidan nan Shima sai da yayi da gaske sannan Annur ya saki jiki dashi.

Idan an fito break muna had'uwa da Sajida da Haisam muyi break d'in tare, daga baya abokin daddyn Annur ya samu transfer ya bar makarantar, shikenan muka koma rayuwar yunwa domin Annur baya yarda ya ci abincin su,sai ma ya daina fitowa daga class har sai an tashi, nima ganin haka na daina ci muke hak'uri da yunwar har a tashe su mu dawo gida.










📝 Comments d'in ku a kullum shi ke bamu k'arfin gwiwa📝

MATAR DA ZAN AURAWhere stories live. Discover now