*MATAR DA ZAN AURA*
BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula tagari]_Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap
Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7
Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
Page 69&&70
__________📲Salim ke nunawa mai taxi layin da zai shiga bayan sun zo unguwar.
A k'ofar gidan suka yi parking, Baba ya biya Mai taxi kud'insa sannan Abdallah ya k'arasa jikin gate d'in gidan yayi knocking.
Maigadi ya bud'e ya fito yace "Lafiya, Malam wa kuke nema".
Baba yayi saurin matsowa ya mik'a masa hannu suka gaisa yace "Mun zo ganin Abida, ni Mahaifin ta ne".
Maigadi yace "Allah sarki sannu da hanya sai dai kuma tun jiya suka fita da Annur gashi har zuwa yanzu banga dawowar su ba".
Baba yace "To badamuwa, hannu ya sa cikin aljihunsa ya fiddo Kati ya mik'awa maigadi yace "ga wannan katin ka bashi idan ya dawo sai ya kira ni a waya".
Maigadi yace "Insha Allah yana zuwa zan bashi a sauka lafiya".
Juyawa suka yi suka tafi yayin da Maigadi ya turo k'ofar ya rufe.
Abdallah yace "Yanzu ya kenan zamu yi".
"Gida zamu koma, komai dare insha Allah"Cewar Baba.
Salim yace " da ma mun d'auko mota, yanzu a motar haya zamu juya Baba ko dai mu kwana da safe mun tafi".
"Ba wanda zan iya ba tuk'i cikin ku ni kuma ba zan iya wannan doguwar tafiyar ba, ai ba zamu rasa mota mai Lodi ba muje tashar".
Ba wanda ya sake magana cikinsu har suka tsaida taxi suka hau zuwa tasha.
*****************
Babban Yaya ya kalleta yace "Abinda ya sa na kira ki shine don inji dalilin ki na k'in yarda a maida aurenki ko kin samu wanda ya fishi ne".
Maman Abida tace "Aa, auren ne ya fitar min a rai sannan lokacin da yaran ke buk'ata ta ya wuce tunda kowa cikinsu ya mallaki hankalin kansa".
"Ba wai zan takura ki ne akan ki koma ba, amma har yanzu ke d'in sutura ce ga yaranki, musamman Abida da take mace ga kuma matsaloli na rayuwa da ta fuskanta ya kamata a ce kina kusa da ita ko ta samu sassauci, nasan zaki ce min yanzu tayi aure to duk da haka idan kina gidan mahaifinta shi kanshi mijin nata zai fi samun damar kawo miki ita, amma dai na baki sati d'aya ki je ki tunani.
********
Jajirtattun security d'in k'asar Istanbul sun yi nasarar chafke accountant tare da yaransa inda suka tasa k'eyarsu zuwa sashen binciken masu aikata munanan laifuka na k'asar.
Washegarin ranar da abin ya faru da safe suna breakfast suka ji k'arar door bell, Saif ne ya je ya lek'a ganin uniform a jikin mutumin ya tabbatar da security officer ne, don haka ya bud'e k'ofar kai tsaye.
Bayan ya shigo sun gaisa da Daddy ya sanar da su ana neman su a police station na k'asar, Daddy ya tabbatar masa zasu shirya yanzu sai suje, sallama suka yi sannan ya tafi.
Bayan sun gama breakfast sun shirya, Mustapha yace "Daddy ku je police station d'in kai da Saif ni sai naje na nema mana Visa".
Daddy yace "Aa tare zamu police station idan mun gama sai ka je, idan bamu gama ba sai a hak'ura zuwa gobe Insha Allah sai kaje kai mana visa".