*MATAR DA ZAN AURA*
BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula tagari]_Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap
Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7
Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
Page 15&16
_________📲"Ina nufin Annur ya taso cikin kewa da maraici, tun yana k'aramin sa bai saba da kowa ba Kamar yanda ya saba dake, Kuma nasan duk macen da zai rayuwa da ita ba lallai bane ya samu Kamar ki, 'Abida Ina yiwa Annur sha'awar ki.
Waiwaye na shiga yi tare da fatan Allah yasa wani baiji ba, nace 'haba Anty hadiza ya kike irin wannan maganar, Annur k'anina ne Kuma haka na d'auke shi, Abdallah k'anina fa ya girmewa Annur da wata hud'u,
Insha Allah hakan ma ba zai tab'a faruwa ba.Akwai sajida yarinyar tana son Annur sosai kuma sun dace da juna,tana da hankali sosai, sannan Annur yanzu SS3 yake nan gaba zai karatu ni ko na San tun da ba karatu nake ba kwana kusa zan iya tafiya, na k'arasa maganar tare da rufe fuskata da tafin hannuna.
Murmushi Anty Hadiza tayi tare da cewa lokaci zai nuna, 'ina jinki k'arasa min labarin.
Tun daga lokacin na fara aiki a wajen madam hassana, sai dai na daina kaiwa Annur abinci Dan kar ya gane, mai gadin su na school na je na samu nayi masa bayanin daga gida ake aiko masa amma ba ya son ana aikoni Dan Allah ko zai taimaka ya r'ika kai ma Annur.
Mai gadin Kamar ba zai amince ba sai yace 'kin San yawan bari na a wajen nan na iya zamar min matsala amma bari na had'a ki da d'aya daga cikin malamansu.
Godiya na masa ya rakani har staff room, gaban table d'in wani malami mai suna Ahmad sadiq.
Muka gaisa da malamin nake fad'a masa daga gidan su Annur aka aiko ni zan ke kawo masa break kullum amma malamin da ake ba yanzu ya bar makarantar.
Murmushi shin sa me kyau yayi yace 'idan na fahimce ki new guidance ake so a nema wa Annur ko' 'eh nace masa, yace 'To ba matsala, komai za a ba Annur ki kawo min zan basa zan zama guidance nashi, sannan in ana neman wani abu daga gareshi zan sanar dake, dama sau ba adadi idan ana son abu sai yace babu,ko Kuma dadynsa yayi tafiya, Kin ga yanzu haka bashi da wasu text books d'in sai ki fad'a idan kin koma gida yaron miskili ne sosai.
'to malam mungode' nace har na juya zan tafi sai na dawo nace a rubuta min sunan littafan da za'a kawo masa dadyn sa zai dawo wani satin sai na basa.
Uncle Ahmad yace 'kar ki damu anan cikin makarantar ake saya wa student d'inmu books, yace min bari ya duba na 'yan ajin su Annur sai ya fad'a min yanzu.
Ina tsaye ya janyo drower dake jikin table d'insa ya d'auko wata takarda ya hau dubawa.
Zuwa wani d'an lokaci yace 'yawwa Annur Ahmad Abdallah ko' 'eh nace masa kai tsaye, yace 'guda uku ne ma books d'in da bashi dasu,. Dubu hudu da dari shida ne kud'in sa,' nace 'Uncle mungode wani satin za,a kawo kud'in insha Allah,' yace min ba matsala nan mukayi sallama na koma restaurant d'in madam hassana na cigaba da aiki.
Bayan kwana uku ranar wata lahadi na sameki nace ki bani kud'ina da kike ajje min, kin San a lokacin fad'a kika min mai zanyi da kud'i har dubu biyar da 'yan kai,
A lokacin Anty hadiza har kika ce min "ke da za ai wa sayyayar kayan sallah nan gaba kad'an, haka kike so ki sallah ba suturar kirki".
Kin San ce miki nayi wani abu ne mai matuk'ar muhimmanci ya taso har nace miki ba zan iya fad'a miki ba a lokacin sai dai ko a gaba, to wannan shine dalilin.
Hawaye ne ya zubowa Anty hadiza da tayi saurin gogewa kar Abida ta gani.
Daganan na sa kok'ari a aikin restaurant d'in madam hassana ina fatan Allah ya kawo min yanda zan ke samun kud'i kafin a sake neman wani abu a makarantar su Annur,
Zama na a wannan restaurant, Albarkar hannu da Allah ya bani yasa customers suka k'aru sosai wannan dalilin yasa madam hassana ta fara biya na salary, wani lokacin har kyautar kud'i take min haka nan,
Duk abinda aka nema a school Kamar kud'in student outing, akwai lokacin da aka canja musu sport wear ma da student clubs, Anty hadiza duk ni nake biya Kuma da kud'in aikin restaurant, da dubu ta uku ta gidan nan.
Ban San taya zan fara miki bayani ba shiyasa duk lokacin da kike fad'a baki ganin abinda nake da kud'i sai dai inyi shiru.
Anty hadiza kuka take sosai sannan tace 'tabbas Abida Annur bashi da wata mahad'ar Rayuwa sai ke, yanzu na k'ara tabbatar da hakan.
A yayin da Anty hadiza ke kuka Annur ma na can cikin garden fuskar sa ta b'aci da hawaye duk wata hira da suka yi yaji komai, silently yabi wata hanyar ya wuce cikin gida batare da ya bari sun ganshi ba.
Abida tace Dan Allah Anty hadiza ki bar wannan maganar, ni da Annur babu had'i na girme sa lokacin da zanyi aure ma Annur yana can yana karatu Insha Allah Kuma koma wa na aura zan kula da rayuwar Annur a duk inda nake.
Ni NAFSAL nace ta yaya za ai hakan , NeeNan Annur?
My fans wai ina dadyn Annur ne ya bar Abida ke d'awainiya da Annur?
Gaskiya ina jiran team Abida su nemo mana shi.
Na tsaya anan saboda bana samun comments sosai
📝 Comments d'in ku a kullum shi ke bamu k'arfin gwiwa📝