page 55&56

15 0 0
                                    

*MATAR DA ZAN AURA*
    BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7

Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

        Page 55&56

__________📲Ya jima zaune a wajen ita kuma Abida tak'i fitowa, tashi yayi ya fita daga d'akin.

Garden d'in gidan ya je ya zauna,  tunanin Daddy ya fad'o masa a rai, yana ba zuciyar shi tabbacin duk inda yake ba lafiya ba, don 'yan kwanakin nan in ya keb'e ba  abinda ke fad'o masa a rai idan ba Daddy ba, shekara hud'u kenan rabonshi da gida.

  Har Mustapha ya shigo garden ya zauna Annur bai san yana wajen ba sai da yayi gyaran murya sannan ya d'ago ya kalleshi.

Hajiya Naila zaune a kan gado a d'akin bak'i tana maida numfashi, sai da ta dawo hankalinta sosai sannan ta d'au wayarta dake ajje gefenta tun shigarta, wata number tayi dialing bata dad'e tana ringing ba akai picking cikin sauri tace "Hello sweetie", daga can b'angaren yace "Hello Heart ya naji muryar ki cike da tsoro ko wani abun ya faru".

Hajiya tace "komai ma ya faru, kaga wannan d'an  nasa da muke rainawa ya fara attempting duka na gaskiya ya kamata ayi ta tak'are a kawo k'arshen al'amura nagaji shekara nawa ana abu d'aya".

Daga d'aya b'angaren ya sake cewa "ba ke kad'ai ba ni kaina na gaji, mutumin masifan taurin kaine da shi, su kansu yaran dake tsaron sa badan an musu barazana da rayuwar  ahalin su ba da yanzu sun kama gabansu amma ina miki albishir nan da watanni zamu gama da komai, ko ya bada had'in kai ko bai bada ba, yaron da kika ce zaki turo Istanbul ki tabbata ya taho jibi, sannan ki sake bincikensa kar a samu kuskure".

"Yawwa har naji dadi, bakada matsala dani kar ka damu nasan wa zan turo sai anjima, I kiss you". Cewar Hajiya Naila tare da katse wayar.

Mustapha ya tambayi Annur "Meke damun ka har yasa ka cikin wannan yanayin".

"Daddy nake tunani duk inda yake gaskiya baya cikin yanayi mai kyau ba abinda zai hana shi zuwa gida tsawon lokaci haka ko dai ya mutu kuke b'oye min". Cewar Annur.

Girgiza kai Mustapha yayi alamar aa, take hawaye suka zubo masa yasa hannu ya goge.

Kamo hannun Mustapha yayi ya damk'e  sannan yace "zaka fad'a min abinda ke faruwa ko har yanzu ban kai girman da zan sani ba".

Dariya Mustapha yayi sannan yace"Har ka wuce ma mutumin da ya rigani ajje Iyali".

Had'e rai Annur yayi ya juyawa Mustapha baya.

Kallonsa Mustapha yayi na d'an lokaci cike da tausayin kansu irin rayuwar da suka tsinci kansu.

Cike da sanyin murya Mustapha yace "Annur ka juyo yau zamu yi magana mai muhimmanci kuma zamu aiwatar da komai cikin sirri".

Juyowa Annur yayi ba tare da yayi musu ba.

Mustapha ya share hawayen da ya zubo masa ya kalli ko ina ya tabbatar babu mai tahowa sannan yace "kasan filin ball d'in nan na bayan layin mu ko, inda kake zuwa morning training".

Annur ya d'aga masa kai alamar "eh" saboda shima Mustapha ya jefa shi cikin damuwa.

Mustapha yace "yawwa to mu had'u a can k'arfe takwas na dare zan fad'a maka komai sannan anjima k'arfe hud'u na yamma za'a d'aura aurena da Fadila saboda zanyi wata tafiya itama zan sanar da kai anjima, kuma bana buk'atar kayi attending saboda da tsaro, babu wanda yasan batun cikin gidan nan daga Babanta Sai kai Sai ita da mahaifiyarta, kar ka fita daga gidan nan idan ba zuwa masallaci ba har sai bayan isha d'in".

MATAR DA ZAN AURAWhere stories live. Discover now