page 75&76

14 0 0
                                    

*MATAR DA ZAN AURA*
    BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7

Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

      Page 75&76

__________📲Fadila ta tashi da niyyar dubawa Annur yace "ki zamanki" sannan ya tashi ya fita.

Yana bud'e gate ya ga dattijuwa.

"Bani hanya in wuce" cewar matar.

"Hajiya wa kike nema" cewar Annur.

"Kai nake nema ai ba b'atan kai nayi ba, ke fito daga motar mana". Cewar tsohuwa.

Motar Annur ya k'ure da Ido ya ga wa zai fito.

Cikin mamaki yaga Hibbah ta fito rik'e da makullin mota a hannun ta.

"Yaran yanzu sai Allah nace ka ban hanya, na wuce ciki" Kaka Hajjo ta sake fad'a.

Annur matsawa yayi ta wuce Hibbah na biye da ita a baya sannan shima ya bi bayan su.

Suna shiga cikin falon Kaka ta nemi waje ta zauna ganin shekarun ta yasa Abida da Fadila suka koma k'asa suka zauna, gaida ta suka yi ta  amsa.

Fadila da Hibbah sai aikawa juna harara suke yayin da Abida kanta ke k'asa.

Annur tun shigowar sa ya shige cikin d'aki laptop d'insa ya d'auka ya sa a jaka ya goya ya tsaya bakin madubi yana fesa turare.

"Wannan yaron bai san wajensa muka zo ba ya d'ebi jiki ya shige ciki". Cewar Kakar Hibbah.

"Bari na kirashi Kaka, naga hanyar da ya bi" Cewar Hibbah

Kaka tace "Ke bana son rawar kai koma ki zauna ko zai shekara a ciki dole ya fito ya same mu anan".

Abida ta tashi ta ce "Bari na kira muku shi" tana fara tafiya Hajjo ta kalli yanayin yanda Abidar ke tafiya ta tab'e baki.

Annur ya fito daga d'aki sukanyi karo da Abida da ke k'ok'arin shiga d'akin

"Am sorry Ninah" abinda ya iya furtawa kenan ya wuce ta bi shi a baya

Fadila ya kalla yana gyara zaman  school bag a bayanshi yace  "Ku tabbatar kun gama abincin nan da wuri zan je makaranta an kirani yanzu".

Hajjo tace "Haba d'an nan yau aka haife ni da zaka nuna min wayo kaje ka dawo ko kwana zaka yi muna nan muna jiranka".

Annur ficewa yayi batare da ya sake magana ba, Fadila tace "Abida tashi mu je kitchen mu fara aikin nan tun yanzu kar mu makara".

Abida rusunawa tayi tace. "Hajiya zamu shiga kitchen kar mu barku ku kad'ai".

"Hajjo nake ba Hajiya ba sannan kuna iya barin gidan ma ba matsalar mu bace wanda muka zo gani muke Jira".

Kitchen suka wuce ba tare da sun sake cewa komai ba.

Suna shiga kitchen Abida ta sa kuka, Fadila ta juyo ta rungume ta tana goge mata hawayen.

"Don Allah Abida kar ki b'ata hawayenki a banza, ai kin yi sa'a Annur yana miki fighting, shiyasa tun tuni nake ta fad'a miki ki kama mijinki hannu biyu ki kula da shi tun kafin ki samu 'yan tayi, Alhamdulillah kin yi saurin fahimta lokaci bai k'ure mana ba".

"Abida Ina so ki cire kunya ki nuna mata Banbancin aure da kuma nema, tunda har ta kawo kanta gidan nan, har kakan ma idan da hali kiyi a gabanta kin ga gobe ba zasu dawo ba".

MATAR DA ZAN AURAWhere stories live. Discover now