*MATAR DA ZAN AURA*
BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula tagari]_Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap
Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7
Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
Page 49&50
__________📲Granny na zuwa ya tarar yaranshi maza na fad'a akan company sa dake California, yayi k'ok'arin sasanta abin amma sun k'i sauraren sa hakan yasa ya yanke jiki ya fad'i.
Cikin gaggawa akai asibiti da shi, sosai likitoci ke kula dashi tsawon kwana d'aya shiru bai farfad'o ba.
Suna hanya Fadila ta juyo tace wa Annur "Ya jikin naka".
"Na samu lafiya" Cewar Annur.
Abida tayi saurin cewa "Da sauk'i dai muna fatan ka samu lafiyar".Annur bai kula ta ba ya cigaba da danna wayar sa, Mustapha na dariya ciki ciki.
Fadila tace "Allah ya baka lafiya" Abida ta sake cewa "Amin yanzu kikai magana".
Mustapha k'asa had'iye dariyarsa yayi sai da yayi mai isarsa, can yace "Amin".
Annur duk yana jinsu bai sake tankawa kowa ba.
Fadila tace "Yaya Mustapha wai yaushe aka sa bikin mu ne"
Abida gabad'aya ta fiddo idanunta waje ta kuma kasa magana daidai lokacin Mustapha ya tura kan motar cikin makarantar tare da yin parking.
Annur ya juya zai wa Abida magana yaganta a haka, girgiza ta yayi, take tayi ajiyar zuciya tare da fad'in "Me kake cewa"
Harara ya watsa mata sannan yace idan kin gama jin gulmar sai ki d'auko school bag d'ina mu tafi kar ki makarar da ni, tsabar b'acin rai ko tsayawa ya taimaka mata da d'aukar jakar Annur bai yi ba.
Fita yayi ya nufi hanyar hall, Abida daukar jakar tayi sannan tace wa fadila 'Ki fito muje".
Fadila tace "Ki je ina nan zan taya yaya Mustapha zama sai kun dawo".
Abida ta k'ure Mustapha da ido shi Kuma ya d'auke kai kamar ma bai san tana wajen ba.
Hakan da Mustapha ya yi ya tab'a mata rai sosai cikin fushi ta ja jakar ko nauyin ma bata ji ba tabi bayan Annur.
Yana shiga hall suka fara ihu, yana zama wasu daga cikin yan class d'in suka zo suka fara masa magana wai suna so su ji gaskiyar lamari.
Abida dake tsaye ta ajje jakar kusa da shi ta juya zata fita yace "Ninah dawo ki d'auka ba'a shiga exams da jaka".
Dawowa tayi ta d'auki jakar amma da ka ganta kasan ranta b'ace yake.
D'aya daga cikin student d'in ya sake cewa "Kai fa Annur matsalar ka rainin wayo ka fad'i abu mun ce kayi proving amma ka share mutane"
Ta shi yayi tsaye daga seat d'in da yake yace "Ninah".
Har ta kai bakin k'ofa ta tsaya yana zuwa gaban ta yayi hugging (runguma) d'inta ya bata peck(kiss) a cheeks(kumatu) d'in ta.
Gabad'aya hall d'in ya d'au ihu har da masu buga desk.
Jakar Annur ya d'auka ya kama hannun Abida suka bar hall d'in yayin da hawayen bakin ciki ya sauka akan fuskarta.
K'ark'ashin bishiyar da suka saba zama ya kai ta Sai da ta zauna sannan ya d'auko hankici daga aljihun uniform d'insa ya tsuguna ya hau goge mata hawayen.
Shiru yayi na wani lokaci yana kallon k'asa kamar mai tunanin abinda zai ce, Sai can ya d'ago ya kafa mata Idanu kamar Wanda baison magana yace "Ninah I am very sorry hakan ba zai sake faruwa ba, mistake ne ki hak'uri kinji".