*MATAR DA ZAN AURA*
BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula tagari]_Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap
Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7
Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
Page 61&62
__________📲K'aran ruwa ta jiyo daga toilet "Annur", abinda ta furta a fili.
Zaro Idanu tayi ta dafe kirji tace "Ba dai a nan ya kwana ba, aa banga dalilin da zaisa ya kwana anan ba".
K'ofar toilet ya bud'e ya fito sanye da jallabiya, bin shi tayi da kallo fuskar ta d'auke da mamaki.
"Ki je ki alwala kin tsaya kallo na har sai kin makara" Abinda Annur ya fad'a kenan ya bud'e kofa ya fice.
Abida tace "Tab lallai ji wannan yaron ni zai fad'awa magana, to ni mi ma zan kalla Allah na tuba" tab'e baki tayi ta mik'e ta shiga toilet.
Cikin sauri tayi wanka ta d'auro alwala, bayan ta shirya tayi sallah sannan ta nufi b'angaren su Anty Hadiza.
A zaune ta same su sun idar da sallah, su Mama har sun yi shirin tafiya.
Gaida su tayi sannan tace "Mama ba dai har tafiya zakuyi ba".
Mama tace "Yanzu ko insha Allah, amma zan bar Salima a nan sai zuwa next week zata koma".
Cikin sauri Salima tace "Tab k'afa ta k'afar ki, gida zan koma gaskiya".
Mama murmushi tayi bata ce komai ba, Fadila ta ce "Haba sisto ki d'an yi mana one week d'in".
Salima tace "Aa gaskiya ina da lecture cikin week kuma fashin zai iya zamar min matsala".
Fadila tace "To shikenan amma dai ba haka muka so ba".
Annur ne yayi sallama a bakin k'ofa, "Shigo daga ciki" cewar Anty Hadiza.
Bakin k'ofa ya zauna ya gaida Mama da Anty Hadiza, amsawa suka yi sannan Mama ta kalli Abida da Salima da Fadila taga basu da niyyar gaida shi.
Mama tace "Sannu Manyan Hajiyoyi kuna jira ya gaida ku ne".
Fadila tayi saurin cewa "Ayya Mama ki yi hak'uri jira muke sai kun gama gaisawa sannan mu gaida shi, bro noor ina kwana".
"Lafiya" yace, sannan sauran ma suka gaida shi.
Ledar hannunsa ya ajje yace "Ga breakfast nan, am sorry ban kawo da wuri ba nayi dropping Mustapha a airport".
" Ba komai da ma baka yi wahala har haka ba, shi kuma Mustapha Allah ya sauke shi lafiya" cewar Mama.
Gabad'aya suka amsa da "Amin".
Tashi Annur yayi yace "Zan je in shirya kafin ku gama".
"Ok mungode Allah maka Albarka" Cewar Mama.
"Amin" Annur yace sannan ya fice daga d'akin".
Bayan sun gama break, suka yi sallama da Anty Hadiza suka fito harabar gidan.
Annur suka gani jingine jikin mota, da alama su yake jira, k'ofar baya ya bud'e wa Mama ta shiga ta zauna, Salima ta bud'e d'aya side d'in ta shiga.
Da sauri Fadila ma ta shiga ta zauna kusa da Salima, ganin haka Abida ma tayi kok'arin shiga ganin irin Kallon da mama tayi mata yasa tayi saurin barin wajen ta bud'e gaban motar ta zauna tana turo baki.
Anty Hadiza ce ta lek'o tace ku kuma ina zaku bisu, ke mijin ki ya baki izinin fita duk lokacin da Kika ga dama ne".
Fadila tace "Mami cewa yayi duk sanda nake buk'atar fita na tambayi bro noor kuma naga yanzu da shi zamu fita please kar ki hana ni".