page 37&38

13 1 0
                                    

*MATAR DA ZAN AURA*
    BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7

Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

     Page 37&38

__________📲Isar su k'ofar gidan suka ga Kamar taro ake, cikin sa'a Salim ya fito daga gidan sai kallon agogon hannunsa yake.

Mustapha ne ya k'arasa kusa da Salim d'in ya mik'a masa Hannu sukayi musabaha.

Salim bai bar Mustapha yayi magana ba yace "D'aurin auren kuka zo ai an kusa farawa kowa yana masallaci mu k'arasa can d'in".

Mustapha zaiyi magana Granny dake tsaye kusa dasu yayi saurin cewa "Ba matsala ka wuce gaba Sai mu bika".

Mustapha da Granny cikin mota suka koma inda suka bar Annur da Alhaji Isa.

Lipan d'in sa Salim ya tada yayi gaba yayin da Mustapha ke bin bayansa.

Annur kasa hak'uri yayi yace "Granny Ina zamu"

"Ka kwantar da hankalin ka Idan muka je zaka gani" cewar Granny.

Suna zuwa harabar masallaci sukayi parking, suka fito daga motar, shima Salim ya sauka daga kan lipan d'insa.

Suna shiga masallacin, Malam Mudi da abokansa suma suka shigo.

Wani a gefe yace "Alhamdulillah, ga waliyyan ango sun k'araso,"

Annur kusa da Abdallah ya zauna ba tare da sun San juna ba.

Abokin Abdallah ne yace "Friend wallahi guy din nan da zai auri yaya Ninah ya more da samun mace tagari, amma Ita d'in naso ace a can inda take aikatau d'in ta samu miji da Sai yafi amma zab'in Allah shine zab'i".

Annur take ya gane meke faruwa, tashi yayi a daddafe jiri na d'ibansa da k'yar ya fita daga cikin masallacin, Allah ya taimake sa Mustapha bai saka key ba.

Motar ya bud'e ya kwanta lokaci guda zazzab'i mai zafin gaske ya  saukar masa.

A cikin masallacin, Malam Mudi da abokansa suka mik'a wa Baba hannu da sauran mutanen dake kusa suka yi musabaha.

Bayan an gama gaisawa Malam Mudi yace, "Malam Aliyu zuwa muka yi mu baka hak'uri kasan d'an yau ka haife shi ne baka haifi halinsa ba, rana tsaka yazo min da maganar ya fasa wannan aure, ba yanda banyi da shi ba amma ya bijire, don Allah kuyi hak'uri muma ba haka muka so ba Allah ya zab'a mata alkhairi".

Sun tashi zasu tafi yayan Baba yayi sauri ya shak'o wuyan Malam Mudi, tare da fad'in "Baka isa ba, mu za ka rainawa hankali, mu zaka kunyata gaban mutanen da muka gayyata" lokaci guda hayaniya ta b'alle a cikin masallacin.

Granny ne ya tashi ya fito waje Mustapha na biye dashi, d'an nesa da wajen suka tsaya, Granny ya tambayi Mustapha ina Annur,

Mustapha yace ya dad'e da fita daga mallacin, Mustapha ya ba umarnin ya duba mota ko Annur d'in yana nan.

Kwance ya iske Annur a bayan mota, tab'a jikin sa yayi yaji ya d'auki zafi sosai.

Dawowa yayi ya fad'awa Granny halin da Annur d'in ke ciki, Granny yace doguwar tafiya ce ta kawo masa ciwon, da ya huta zai warware.

"Yanzu Alfarmar da zaka min Mustapha shine ka ceci bayin Allah nan daga jin kunya, Ina nufin ka auri wannan yarinyar zan bada sadakin".cewar Granny

Mama ce tace "Wai ke mene matsalar ki tun d'azu nake bin kanki kije ki wanka ki shirya gashi har lokacin d'aurin aure yayi amma baki ko motsa ba"

Abida tace "Mama bani da kaya sabbi  ko kala d'aya".

MATAR DA ZAN AURAWhere stories live. Discover now