Matar da Zan Aura 19&20

21 0 0
                                    

*MATAR DA ZAN AURA*
    BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7

Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

      Page 19&20

  📲__________Annur ne ya k'arasa inda suke da k'arfi ya fisgi hannun Abida yayi wajen mota da ita murfin motar ya bud'e ya tura ta ciki sai da ta d'an bige amma da ke ransa ya b'aci bai ma San ya buga mata kai ba, da k'arfi ya maida k'ofar ya rufe ya bud'e seat d'in gaba ya zauna tare da dafe kansa.

  Mustapha ne ya d'auki jakar kayan Abida yasa a butt sannan ya shiga ya tuk'a suka hau hanya.

              *********

Umar sai a lokacin ya dawo hankalin sa ya tuna da aiken da aka masa, butt d'in lipan d'insa ya bud'e ya d'auko wata bak'ar leda, juyawar da zai yaga Anty Dija bata wajen,ta koma cikin gida.

K'arasa wa yayi tare da yin sallama, "ka shigo"amsar da aka bashi kenan, yana shiga ya tarar an shimfid'a masa tabarma, zama yayi suka gaisa.

Ledar ya mik'a mata gashi inji baba malam yace akwai bayanin da yake so ya miki ki samu lokaci ki je ko ki Kira sa a waya.

To shikenan Umar ka gaida malam d'in, ledar ta d'auka tana fatan kar yayi mata maganar Abida.

"Magana nake so muyi dake kafin na tafi Hajiya Dija" cewar Umar, badan ranta ya so ba ta koma ta zauna.

"Na dad'e Ina son wannan 'yar taki tun wata rana da Baba Malam ya aiko ni na kawo miki sak'o ina zuwa nan ita Kuma ta shiga keke napep naso yi mata magana a lokacin amma kafin na k'arasa wajen har me keken ya ja sun tafi, nan nazo nayi maki bayani kika nuna baki ganeta ba amma na barshi a haka nasan rana irin wannan tana zuwa"

   Zan sake tuna miki Kamar yanda na fad'a a wancan lokacin d'iyar ku Abida ita ce *matar da zan aura* ina son ta sosai  ki sanar da mahaifinta zamu zo ni da nawa mahaifin na bar ki lafiya" daga haka yayi ficewar sa ya bar ta zaune cikin tashin hankali da damuwa.

    Su Annur sun yi nisa sosai har sun kusa shiga gari wayar sa tayi k'ara d'auka yayi tare da fad'in " salam granny kana lafiya" sun dad'e sosai suna magana a waya daga k'arshe sukai sallama.

Annur ne ya cewa mustapha ya ajje su a Nasmir restaurant, suna shiga ya sake cewa mustapha ya amshi abinda yake so ya tafi shi anan zasu ci idan sun gama zai Kira shi ya maida su gida.

Mustapha order sa ya amsa yayi musu sallama, Abida na tsaye ta kasa ko motsin kirki, Annur ne yace "muje VIP side mu zauna, "I need privacy"(I na son sirri/keb'ewa) gaba yayi tabi bayansa.

Wasu lafiyayyin throw pillows ne masu yawa zube akan carpet d'in, zama sukai kowa yayi shiru yana faman tunani

   Annur ne ya kauda shirun ya tambayi me zata ci, tace komai ma akai order zata ci, waiters d'in wajen ya Kira ya basu order,

Facing(fuskantar) Abida yayi alamar yana son magana da ita, tattaro hankalinta tayi tana sauraren sa.

"Mutumin da yazo a lipan waye shi"Annur ya jefa mata tambayar bazata

Abida tace "ban San shi ba ina dai ganin sa yana kawo wa Anty Dija sak'o amma dai ba d'an uwan ta bane"

Annur ya sake cewa "ok dama kuna son juna ne" tambayar ta b'atawa Abida rai, k'aramin yaro da ko secondary bai gama ba yake shiga cikin love appears(al'amuran soyayya) d'in ta, shiru tayi ba amsa.

Abincin su ne aka kawo, Annur ya d'au nasa ya fara ci bata tare da ya sake magana ba.

Abida ko tunani ya mata yawa ko kallon abincin bata yi ba, sai da ya kusa cinye wa ya kalli nata da ko tab'a wa ba tayi  ba.

"Ninah your food is getting cold ( abincin ki zaiyi sanyi ) me ke damunki ko kina da matsala".

Hawaye ne suka zubo kan fuskar ta tayi saurin sa hannu ta goge, sannan tace "Anty Dija ta samu kud'i a jaka ta har dubu shida da turare ta kwashe su sannan ta min sharri wai satar su nayi.

Ban tab'a d'aukar kayan kowa ba sai abinda aka bani" cikin muryar kuka ta cigaba da cewa hakan bai ishe ta ba sai da ta had'a da duka ta koro ni Kuma tace kar na sake zuwa.

shike nan ta raba ni da babana ko ganinsa ba ta bar ni nayi ba".

Tissue ya mik'a mata yace "Kukan ya isa haka, kud'i ni na ajje miki ko zaki amfani da su, baba Kuma insha Allah bayan exams zamu dawo sai ki gaidashi, amma wannan Umar d'in bai dace dake ba kar ki kulashi".

Abida da ranta ya k'ara b'aci tace " Ina ruwanka da Wanda zan so da Wanda ba zan so ba, kai me ka sani a wannan fagen."

"Oh really, amma fa kina da gaskiya ina d'an secondary me zan sani a wannan fagen".

ki ci abincin ki yanzu mustapha zaizo daukarmu"Annur ya fad'a yayin da yake danna wayar hannunsa.

"Na koshi" Abida tace, wata waiter ya gani kusa da su ya bata umarnin tayi masu packaging abincin Abida zasu tafi dashi.

Kallon Abida yayi yace "zan fita waje idan ta had'a abincin ki amsa ki fito, amma zan k'ara fad'a miki idan har kina son mutumin nan ki  daina domin baku dace da juna ba".

Ya kama handle d'in k'ofa zai fita, Abida tayi sauri tace "idan ban dace dashi ba da kai na dace?"

Da farin cikin sa ya dawo yace "wannan itace cikakkiyar amsa, yanzu kika dawo hanya".

cikin sauri ya juya zai bar wajen amma duk da haka kunnensa ya jiyo masa tace " Allah ya min tsari soyayya da k'anin bayana".

           *************

     Umar ne zaune gaban mahaifinsa yayi masa bayanin aiken da yayi masa, sannan yace yana da magana da yake so suyi mai muhimmanci.

Baba malam yace yana sauraron sa, nan umar ya fad'a masa komai da ya faru gaban idonsa.

Sannan yace so yake ya auri yarinyar yana neman izinin malam.

Malam ne ya tabbatar wa da umar bashi da matsala tunda har yana tsananin Sonta kamar yanda ya fad'a ya sawa ranshi ta zama matarsa.

*Please manage*


📝 comments d'in ku a kullum shi ke bamu k'arfin gwiwa📝

MATAR DA ZAN AURAWhere stories live. Discover now