*MATAR DA ZAN AURA*
BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula tagari]_Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap
Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7
Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
Page 17&18
__________📲 Annur da kike tunani yaro ada yanzu fa ba haka bane, Dan kamar Annur in a garinmu ne yayi aurensa, mubar maganar kawai,
Mai wanki da guga na gidan yazo ya same su, yace suje hajiya tana Kira
Anty hadiza tace "mu tashi muje yanzu kar mu jawo matsala"Abida tace "to Anty hadiza labari na fa".
"Kinsan dai tunda tai kiran mu dole muje, labari Kuma in mun samu lokaci zan fad'a miki,idan Kuma bamu samu lokaci ba to abin da zan ce miki shine ki rik'e wannan "a kan rayuwar Annur kar ki yarda da kowa kaf gidan nan sai mustapha direban gidan, Idan daddy akai sa'a ya waiwayi gidan nan ba kowane umarni nashi zaki bi ba, Dan ba a hayyacin sa yake ba, Idan al'amura sun yi tsanani, ba fata nake ba, mutum d'aya zaki nema kakan Annur Wanda ya haifi momynsa, akwai number sa a wayar Annur dan suna waya wani lokacin".
Magana ta k'arshe ki daure ki sayi waya ko ta dubu biyu ce zan baki number ta a takarda kafin ki tafi,"
"Anty hadiza nagode Allah ya bar zumunci" "Amin" tace, sannan suka nufi hanyar cikin gida
Suna shiga falo suka risina gaban hajiya sai da ta d'au lokaci tana danna wayar ta sannan ta d'ago ta kalle su Kamar bata da niyyar magana sai Kuma tace d'azu naga kamar anyi snacks a gidan nan ko, cikin sauri Abida tace "eh dama Annur nayi wa ko zai buk'ata kafin na dawo".
Ko kallo basu isheta ba tace "je ki d'auko min shi""to"tace tare da barin wajen.
Stairs ta hau ta nufi d'akin Annur da k'arfi ta tura k'ofar a tunaninta Annur baya d'akin.
Zaune ta sameshi kan gadonsa, bata yi masa magana ba ta nufi fridge d'in d'akin cake d'in ta d'auka gabad'aya zata fita Annur yace "Ninah zo" kusa da shi taje ta tsaya tace "gani".
Me zaki da wannan ya nuna hannunta dake d'auke da tray d'in cake,
Hajiya ce tace a kawo mata shi, "ok kije ki dawo ina jiran ki zamu yi magana" .
"to" tace tare da barin wajenTana zuwa ta ajje tray d'in a gaban hajiya tace "gashi na kawo" d'aya ta d'auka ta kai bakinta sannan tace "uwar mugun hali duk wannan ki d'auka ki kai masa shi kad'ai to baku isa ba"
Wani ta sake d'auka sannan tace "kai min tray d'in cikin fridge d'ina na d'aki" ranta ba k'aramin b'aci yayi ba amma babu yanda zatayi haka ta kai mata d'aki sai a lokacin taji hawayen takaici na sauka saman fuskarta.
Tunani take yanzu duk wahalar da ta sha wajen had'a special cake d'in ya tashi a banza kenan.
jiki a sanyaye ta koma d'akin Annur.Yana zaune a wajen da ta barshi, ita ta fara magana tace masa "Annur cake d'in da nayi maka hajiya ta kwace yanzu ban San ya zanyi ba"
Annur yace "Wannan ba matsala bane kar ki da mu, amma inaso ki kwana biyu ba uku ba, saboda time table na waec ya fito Kuma jibi zamu fara, sun canja timetable na farko, ina son ki kasance tare dani har na kammala exams d'ina"
"Amma kasan ko na dawo jibi ba zan shigo gari da safe ba sai yamma".
"Eh naji ai paper farko ce jibin Kuma d'aya zanyi, morning paper".
"Ok shikenan" ta fad'a tare da tafiya,
In a silent voice yace "thank you so much my Ninah Annur cares alot"(cikin sanyin murya yace ina matuk'ar godiyaNinah ta, Annur yana yinki sosai.)