page 59&60

21 0 0
                                    

*MATAR DA ZAN AURA*
    BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7

Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

     Page 59&60

__________📲Kafin Abida ta k'arasa cikin falo Fadila ta iske ta.

Hannun Abida ta kama ta ja ta zuwa garden d'in gidan, kujera ta ja ta zaunar da Abida sannan ta koma ciki ta d'ebo ruwa cikin kofi ta ba Abidar, ba musu ta amsa ta shanye tas ta ajje kofin akan table d'in da ke gaban ta sannan ta sauke ajiyar zuciya.

Fadila tagumi ta yi tana kallonta na wani lokaci sannan ta fara magana "Abida nayi mamaki sosai da kika nuna damuwar ki akan aurena da Mustapha, tun had'uwa ta ta farko dake naji ina k'aunar ki kamar 'yar uwata ta jini, kuma ko miji muka had'a ba zan canja miki ba sam amma ke naga sab'anin haka daga gareki".

Hawaye ne suka zubo daga Idanun Abida tasa hannu ta goge sannan cikin sanyin murya tace "Ina miki murna da auren ki da aka d'aura a yau, Allah ya sanya alkhairi, nima Fadila ina k'aunar ki sosai kuma ni bana k'in auren ki da Mustapha kawai dai ina tunanin yanda rayuwa ta zata kasance, kina ganin Mustapha baya shiga sabga ta kuma baya son nima ina shiga tasa, ya auro ni ya maida ni ba a bakin komai ba wannan abin shi ke damuwa amma ke naga yana son ki sosai kinyi sa'a".

Sosai Abida ta ba Fadila tausayi don an bar ta cikin duhu tsawon lokaci.

Tashi tsaye Fadila tayi tace "Gaskiya hak'uri na ya k'are a yau zan fasa k'wan sai dai duk abinda zai faru ma ya faru".

Cike da mamakin furucin Fadila Abida ma ta mik'e tsaye yayin da Hajiya Naila da ke jikin wata bishiya manne da waya a kunnenta zatayi maganar sirri ta kat'se kiran ta matsa bishiyar dake dab da su ta lab'e cikin duhu don jin wannan sirri da Fadila ke Shirin tonawa.

Anty Hadiza ta tashi ta d'ebo ruwa a jug ta had'o da cup ta ajje a gaban Mama tace "Ga ruwa kisha, Matar gidan ta rufe mana store ta chanja sabbin masu aiki kuma ta bada umarnin kar a sake bamu a abinci a gidan, nima  d'azu na je kitchen zan d'ora girkin rana na samu wannan labarin, gashi mijina da Mustapha suna wajen d'aurin aure shi kuma Annur ban sashi a idona ba".

Mama tayi murmushi tace "Kar ki damu ai ba komai", Salima tashi tayi ta bar musu d'akin.

Tsakar gida ta samu farar kujera ta zauna tana matsar k'walla tana gogewa, wani irin murd'awa cikin ta yayi ta rik'e wajen ta kifa kanta a  cinyarta.

Annur ne ya zo gaban ta yace "K'anwar mu" d'ago wa Salima tayi sannan tayi saurin goge hawayen nata.

"Subhanallah baki da lafiya" Annur ya furta yana kallonta.

"A'a kai na ke ciwo" cewar Salima babbar ledar dake   hannun Annur ya mik'a wa Salima yace "Amshi wannan ki kaiwa su Mama bari naje d'aki sai na d'auko miki paracetamol, Allah sawwake".

Amsa Salima tayi sannan tace "Amin Nagode" tashi  tayi ta nufi d'akin Anty Hadiza.

Tana shiga ta ajje ledar tace "gashi nan Annur yace na kawo".

Anty Hadiza ta bud'e ledar ta ga kaji ne manya har guda uku sannan takeaway pack guda shida, tashi tayi taje wajen kayansu ta d'auko babban tray.

Takeaway d'aya ta d'auka ta d'ibi naman mai d'an yawa ta ba Salima "Amshi wannan maza ki ba Abida ta kai wa Annur idan baki ganta ba ki kai masa ai kin san d'akin ko" Mama tace " d'akin da muka baro yanzu ki kai masa ki dawo sai ki ci" Salima da ranta ya gama b'aci ta figi sak'on tayi gaba, Mama ta bita da Idanu tare da fad'in "Allah ya shirya mana".

MATAR DA ZAN AURAWhere stories live. Discover now