*MATAR DA ZAN AURA*
BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula tagari]_Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap
Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7
Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
Page 51&52
__________📲Suna komawa gida, Fadila ta nufi part din Anty Hadiza, yayin da Abida ta nufi d'akin ta.
Tana shiga taga mace ta baje a katifarta tana bacci cikin kwanciyar hankali.
Bakin k'ofa ta maida kallonta inda taga kayan sawar ta zube a k'asa, drower ta kalla wani takaici ya zo mata, ta san mutum hud'u ma zasu iya sa kaya ba tare da drower ta cika ba.
Jaka ta d'auka ta zuba kayan nata a ciki sannan ta d'aura zani da hijab ta shiga band'aki.
Bayan ya huta yayi wanka ya fita daidai fitowar Annur suka jera suka tafi masallaci.
Ana idar da sallah Mustapha ya tashi zai tafi Annur ya tambaye shi inda zashi da ba zai jira ayi sallah isha ba.
Mustapha ya sanar dashi yana da wani uziri me k'arfi bayan sallah magrib d'in.
Musabaha sukai da Annur ya bar masallacin, yana shiga gidan ya wuce k'aramin falon Hajiya kamar yanda sukayi da ita a waya sai dai bai sameta ba, don haka ya zauna zaman jiran fitowarta.
****************
Humaira zaune gaban Umar tasha kwalliya sosai dama hakan a jinin ta yake.
"Love Muje ka ci abinci an had'a table kuma yau special ne, abincin tarba nasa akai maka a part d'in su momy" cewar Humaira.
"OK Muje, kice yau zan sha dad'i" dariya suka yi cike da nishad'i suka nufi dining area.
Umar ya riga d'auke hannunsa daga abincin don haka ya ajje spoon yayi tagumi tare da kafe Humaira da Idanu, zuciyarshi na yaba kyaunta amma akwai d'unbin matsaloli tattare da ita, sannan zuciyarshi har yanzu Abida take muradi duk da yasan tayi masa nisa.
Humaira ta d'ago ta kalleshi ta ce"Kallon fa" shiru ba amsa, sai da ta taso tazo gab dashi ta hura masa iska a fuska sannan ya sauke ajiyar zuciya ya zuba idanunsa cikin nata murmushi ta masa ta sake cewa "wannan kallon fa".
"Kinyi kyau" ya fad'a a tak'aice.
Fari tayi da Idanunta sannan tace "Haka daddy da momy ma suka ce d'azu".
Komawa tayi wajen zamanta ta cigaba da cin abincinta hankali kwance, yayin da Umar yake tausayin rayuwarsu shi da ita.
Tashi yayi Humaira tace " love ina zaka je haka"
Umar yace "Falo zan koma idan kin gama ki sameni akwai wata magana mai muhimmanci da zamuyi"
"Ok" Humaira ta amsa ta cigaba da cin abincinta.
****************
Mustapha ya kai kusan minti talatin yana zaune yana jiran fitowar ta.K'amshin ta ne ya bashi amsar fitowar ta.
Zama tayi a kujerar dake fuskantar ta Mustapha, gaidata yayi ta amsa cikin shan k'amshi.
"Zan fara magana ta kai tsaye tunda kasan komai ba sai na maimaita ba, wannan aikin da muke yi gaskiya baya sauri tafiyar hawainiya yake, ga Alhaji a can ya k'i bada had'in kai sam, don haka a yau na canja wasu daga cikin masu aikin gidan nan Wanda sam ban yarda da su ba nasa wasu, gaba ma zan sake canja wa"