*MATAR DA ZAN AURA*
BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula tagari]_Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap
Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7
Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
*A page 15&16 malaminsu Annur na fad'e shi da Uncle Ahmad, yanzu na canza shi zuwa teacher Ahmad saboda wannan shi yafi daidai, ina neman afuwan readers kan canji da aka samu*
Page 21&22_________📲Ana gama packaging abincin Abida ta amsa ta fito Dai-dai da isowar Mustapha, tare suka shiga motar da Annur, Mustapha ya ja motar suka nufi gida.
Suna zuwa gate driver ya fara hon, juyawar da Annur zaiyi ya ga malamin su na school a wajen gate d'in nasu.
Lokaci guda mamaki ya kamashi ko an chanja time table ne ya zo ya fad'a masa, bai tab'a zuwa ba yasan abinda zai kawo shi will be very important (mai matuk'ar muhimmanci ne).
Sauka yayi daga cikin motar ya ba Mustapha umarnin su shiga gida zai taho daga baya.
Teacher Ahmad na ganinshi ya taho da sauri kafin ya k'araso inda Annur yake motar har ta shiga gida.
Annur ne yace "good evening sir" teacher Ahmad murmushi yayi ya mik'a masa hannu sukai musabaha tare da fad'in "My boy kana lafiya ya karatun exams" "Alhamdulillah" cewar Annur.
"Dama na zo wajen yayar ka ne akwai maganar da nake so muyi da ita sai aka ce mun kunyi tafiya, yanzu ma zan wuce kenan naga dawowar ku tare da ita, Dan Allah d'an shiga gidan sai ka turo min ita"
Tuni Annur ya had'e Rai, lokaci guda bak'in ciki ya ziyarci zuciyarshi, ga ba damar yace ba za shi ba.
Sake had'e rai yayi domin Idan ya bud'e baki ya k'ara magana a wajen matsala za'a samu.
Dan haka ya juya ya tafi ba tare da ya amsawa teacher Ahmad ba, shi Kuma ya San halin Annur na miskilanci don haka yayi tunanin ko halin ne ya motsa amma yana da tabbacin zai turo ta.
Annur na shiga compound (farfajiya) d'in gidan su, Mustapha dake zaune kan benci ya ta so da sauri yace "Ko a shigar da kayan Abida ciki ta manta su a butt"
Da farko shiru yayi bai kulasa ba, Mustapha ya gane b'acin rai tsantsa a fuskar ubandakin nashi.
"Kamar bazai magana ba sai can yace ka Kira ta ka fad'a mata tana da bak'o amma kar su tsaya a waje su zauna a compound tunda akwai kujeru.
Da ga haka yayi gaba ya bar Mustapha tsaye, murmushi Mustapha yayi tare da fad'in "Allah ya ja kwana uban d'aki nah"
Ta baya ya zagaya kitchen ya samu Anty Hadiza yace ta fad'awa Abida tana da bak'o a waje Kuma Mai gida Annur yace su shigo daga ciki kar su tsaya a waje.
Anty Hadiza tace bari taje ta sanar da ita yanzu.
Juyowa tayi ta tambayi Mustapha cewar ko Abida ta fasa zuwa ganin gida ne, amsa ya bata da aa labarin me tsawo ne amma Abida zata fad'a mata daga haka ya fita daga kitchen d'in ita ma Anty hadiza fita tai ta nufi d'akin Abidar don sanar da ita sak'on.
Annur na shiga d'akin sa band'aki ya wuce ya sakar wa kansa ruwa, sai lokacin yayi ajiyar zuciya me k'arfi amma har yanzu k'unci da takaici na damunsa cikin zuciya, kirjinsa har wani zafi yake shi abin har mamaki yake bashi, duk abinda ya faru a yau ke dawo masa k'wak'walwa kamar yanzu yake faruwa.
Tunawa da yayi da malamin su a bakin gate shi ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi cikin sauri yayi wanka ya d'aura alwala sannan yasa towel jikinsa ya fito.
Shirin ma cikin sauri yayi, sa kayan ma bai wani tsaya zab'e ba na saman drower ya d'auka yasa.
Study area nasa dake cikin d'akin yaje ya d'auki kujera ya bud'e k'ofar da zata sada shi da balcony kujerar ya ajje ya zauna yana jiran ya ga me ya kawo teacher Ahmad wajen Ninah.
*************
Abida suna shiga ko tsayawa ba ayi ba ta bud'e k'ofar motar ta fita kai tsaye d'akin ta ta nufa tana shiga ta fad'a kan katifar ta, wasu sabbin hawaye masu zafi ne suka zubo daga Idanunta.Kuka tayi mai isar ta shikenan ita rayuwa haka ta zo mata, cikin maraici alhalin iyayenta na raye cikin k'oshin lafiya.
Sai dai wani b'angaren na zuciyar ta tana nuna mata cewar dukkan tsanani yana tare da sauk'i, duk damuwar da take ciki akwai Wanda suka ninka ta, Kuma ba wani yanayi da zai d'ore(no condition is parmanent).
Ta d'an dad'e tana kuka sai da taji zuciyar ta tayi sanyi sannan ta tashi ta shiga toilet da niyyar wanka.
Anty Hadiza ce ta shigo d'akin bata ga Abida ba har zata fita sai taji k'arar ruwa.
K'ofar toilet d'in ta k'arasa ta fad'a wa Abidar tayi sauri ta fito tana da bak'o a waje.
Kitchen ta koma ta cigaba da aikinta.
Yayin da tabar Abida da tsantsar mamaki Ita ko wa gareta da zai nemeta, Ita tasan ko madam hassana bata tab'a ba address ba, hakanan dai ta k'arasa wanka ta fito ta sa kayan ta da take ganin sune masu d'an kyau da kwari, hijab tasa sannan ta fitaKitchen ta fara zuwa tace Anty Hadiza ta d'an sammata turare ta saka.
Duk da bata san Wanda ke kiranta ba tana so ta fita cikin mutunci, Anty hadiza taja hannunta suka tafi d'akin ta.
Kayan kwalliya ta d'auko ta ba Abidar tace "Ai ba turare kad'ai zaki sa ba ya kamata ki gyara fuskar ki ma, gaskiya Abida wannan watan dole ki cire dubu da d'ari biyar ki bani a suyo kayan kwalliya ina takaicin yanda kike yawo ko powder babu kina 'yammata dake shiyasa babu Wanda yake tarar ki da sunan so, duk da ni nafi son hakan amma dai ai gara ake samun samarin ko ya ne.
Murmushi kawai Abidar tayi ta amshi kayan kwalliya tasa powder da kwalli, ta fesa turare ta mik'e tare da fad'in Anty Hadiza sai na dawo.
Kallon ta tayi tace "Ai baki isa ba sai kin sa Jan baki zaki bar wajen nan".
Dariya Abida take sosai tace "Anty Hadiza zance nace miki zani ban San fa ko wa ke nema na ba, amma dai tunda kin matsa bari nasa" Jan baki ta d'auka tasa sannan tace sai na dawo da sauri ta fice kar Anty Hadiza ta k'ara tsayar da ita.
Hamdala Anty Hadiza tayi tare dacewa Masha Allah ko ba komai na sata farin ciki Dan naga alamar yarinyar tana cikin damuwa yau, banso tayi wa wani kwalliya ba amma dai naji dad'i da hakan ya dawo mata da walwalarta, tashi tayi ta koma bakin aikinta.
Fitar Abida compound shine daidai zaman Annur a balcony, bakin gate taje ta tambayi maigadi waye ke nemanta,
Fad'a mata yayi mutumin na waje, bud'e gate tayi ta fita.
Annur dake zaune yana hango komai ransa ya b'aci wato Ninah bata jin maganar sa me yasa zata fita ba sai ta aika wani ya kira shi ciki ba,(k'arfin hali wa zata aika tana 'yar aiki), ganin sun dad'e ne yasa Annur tashi da niyyar fita ya ji dalilin zamansu waje bai bar wajen ba yaga sun shigo sun jero Kamar wasu couple (ma'aurata), sakin baki yayi yana kallonsu, musamman Ninah bai tab'a ganinta da ko powder a fuskarta ba amma yau har da make up.
Lallai ba zai d'auki wannan sabon salon da tazo da shi ba.Akwai kujeru a compound d'in amma gudun matsala sai tace masa su zauna a benci dake kusa da shukoki Wanda yawan ci direbobin gidan da sauran ma'aikata maza suke zama sai tayi sa'a,yau ba kowa a wajen.
Bayan sun gaisa ne take cewa "Teacher sai gaka kazo ko akwai wani abu da ake buk'ata ne a makarantar,
"Aa, nazo wajen ki ne domin muyi wata magana" cewar teacher Ahmad,
"To ina sauraron ka" gyara zamansa yayi tare da Sauke ajiyar zuciya sannan yace "A gaskiya tun lokacin da kika fara zuwa wajena akan batun Annur naji na fad'a soyayyar ki da farko ban Amince wa kaina ba sai da kika cigaba da zuwa sabo da shak'uwa suka taimaka wajen fahimtar kyawawan halayen ki, 'yan kwanakin da akai baki zo ba anan na tabbatar na kamu wannan shine dalilin zuwana wajenki da fatan zan samu karb'uwa"
"To da farko abin da zan fara fad'a maka shine ni ba 'yar gidan nan bace Asali ma ni 'yar aikin gidan nan ce, kuma......bata k'arasa maganar ta ba Kamar daga sama sukaji ance Kuma "MATAR DA ZAN AURA" Dan haka ka kiyaye.
📝 Comments d'in ku a kullum shi ke bamu k'arfin gwiwa📝