SHAFI NA DAYA

2K 100 7
                                    

©️ HASKE WRITERS ASSOCIATION
_(Home of expert & perfect writers)_

*GARIN DAƊI.........!*
(Based on a true life story)


*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

*Wattpad:ummishatu*

بسم الله الرحمن الرحيم، رب اشرح لي صدري ويسر لي أمري، لا إله إلا الله وحده لا شريك له، اشهد ان لا اله الا الله محمد رسول الله.

_Gaisuwa mai tarin yawa gareku masoya masu karanta littattafan na,labarin garin daɗi labari ne da ya faru a gaske wanda tun lokacin da naji labarin ya tsaya min rai, ya zauna cikin zuciya ta daga ƙarshe naga ya dace in raba wannan labari ga masoya na suma su ji abinda naji duk da na fara sabon littafina a wattpad mai suna baƙo ayi min afuwa na ajiye rubuta baƙo har sai na kammala wannan da yardar Allah, asha karatu lafiya._

1

~~~Alhaji Mukhtar Garzali shine cikakken sunan mahaifinmu, mahaifinmu alƙali ne kuma mai shari'a a wata babbar kotu dake cikin garin Kanon dabo tarin Allah, mu bakwai mahaifinmu ya haifa hudu mata uku maza, yaya Abdallah shine babba sai mai bimasa yaya Abdurrahman, daga nan sai Anty khadija sai yaya Abdul hakim dake bi mata, sai Anty Salaha daga nan sai ni Maimunatu wadda ake kira da (widat) sai ƴar autar mu Bishra. Mahaifinmu sanannen mutum ne kuma ana ganin girman sa da mutuncinsa a ko ina, matansa na aure guda biyu hajiya Aisha (mama) da hajiya Fatima wadda muke kira da Annie, dukkaninsu haifaffun cikin garin Kano ne, shi Abba ɗan asalin garin takai ne wanda aikine ya kai kakansa wato mahaifin babansa zama kasancewarsa alƙali, itama mama ƴar asalin garin takai ce Annie ce kaɗai haifaffiyar garin wudil. Hajiya Aisha itace uwar gida kuma duk hannunta muka taso kasancewar Allah bai bata haihuwa ba, zaman lafiyar da suke yi yasa baƙo baya iya gane ko ƴayan waye mu, duka mazan gidanmu lauyoyi ne domin gaba ɗaya ra'ayinsu kenan na son gadar babanmu, haka a mata ma babbar yayar mu anty khadija lawyer ce, anty salaha ce kaɗai ma'aikaciyar jinya sai bishra dake da irin nata ra'ayin na karantar fannin lafiya domin a yanzu haka tana can makarantar koyon ungozoma da aikin jinya dake garin azare. Nikam dama tun ina ƴar ƙarama nake da sha'awar kutse cikin na'ura mai ƙwaƙwalwa wato (computer) a turance, tun ban iyaba nake shiga ɗakin mazan gidanmu duk wadda naga yayi wasarere da tasa ko ya saka a charge haka zan buɗe inyita yi masa bincike a ciki, duka kam na shashi babu iyaka banda punishment kala kala da suke sakani musamman yaya Abdurrahman da yaƙi jinin ya ajiye abunsa yazo ya iskeshi ba daidai ba ancanja masa matsugunni ko an taɓa masa, duk da irin duka da punishment ɗin da ake sakani hakan bai hanani cigaba da tattaɓa musu laptop ɗinsu ba har saida ta kai ta kawo sun daina ajiyewa acikin ɗakinsu kowa ya canja maɓoya, cikin haka kwatsam sai muka yi baƙo yaron aminin abbanmu wanda yasamu gurbin karatu a jami'ar bayero dake cikin garin kano, sunansa faisal kuma shima harda laptop ɗinshi yazo nan fa na samu aikin yi dan hatta makarantar islamiyya sai su Annie sunyi dagaske nake tafiya lokacin ina aji biyar a makarantar secondary ta jeka ka dawo, shi yaya faisal baida matsala koda yaushe barmin laptop ɗinshi yake yi inyita bincike na da games har sai idan abu mai muhimmanci zai yi sannan zai karɓa shi ɗinma yana gamawa zai dawo min da ita shiyasa laptop ɗin ta zama kamar wata tawa, cikin ƙirƙire ƙirƙire na wata rana na ƙirƙiri wata manhaja ta makarantar mu wadda kowanne ɗalibi za asaka bayanansa da suka shafe shi kama tun daga sunansa, jinsi, aji, report sheet da sauransu harda tambarin makarantar mu a tsakiya, wannan abu da nayi shi ya sake fito da baiwata a fili dan har gobe da wannan tsarin makarantar mu suke amfani dashi kuma lokacin har karramani aka yi domin na faɗawa principal cewa saboda asamu sauƙin fitar da sakamakon jarrabawa na ƙirƙiri application ɗin duba da yadda naga malaman mu na shan wahala wurin marking da harhaɗa marks har su fitar da position sannan ga yawan kuskure da ake samu duk da muna taya su da recording amma daga ƙarshe sai kaga anyi ba daidai ba, wannan abu da nayi shi ya kawo sauƙin aikin da class masters ke sha shiyasa nima darajata ta ɗagu a idon kowa ranar da aka karrama ni kuwa harda sabuwar laptop mai tsada ƴar ƙarama mai kyau principal ta bani lokacin ina zango farko a aji 6,tun daga nan na goge kuma na ƙware a harkar computer ba tare da wani ya koya min ba karambani nane kawai yasa na iya, dan tsabar karambani ni na tsara invitation cards ɗin bikin anty salaha kuma kowa ya yaba domin na ɓata lokaci akansa ina yi masa ado. Bayan na kammala makarantar secondary sakamako ya fito na tafi makarantar koyon ilmin na'ura mai ƙwaƙwalwa a garin kazaure nan na sake gwanancewa dama abune da nake so, shekara biyu na gama nadawo gida ɗauke da sakamako mai kyau, babu ɓata lokaci na faɗa jami'ar bayero dan karantar computer science, nan ɗinma nayi na gama cikin nasara nayi service na gama, lokacin ne na fara tunanin abinda yadace nayi domin samun ƴan canji duk da Annie kullum maganar aurena ce a bakinta acewarta lokaci yayi wanda yadace in fitar da miji inyi aure duk da ni har lokacin ban samu wanda hankalina ya kwanta dashi ba domin Allah ma ya sani ni ina da choice acikin maza, akwai irin mijin da najima ina yi wa kaina fata da kwaɗayin samu sai dai yawancin samarin da nake haɗuwa dasu su kuma ba hakan suke ba shiyasa soyayyar tamu bata ɗorewa sosai, a gefe ɗaya kuma yaya faisal ɗan aminin Abba wanda yayi karatu a gidanmu shima sona yake dan ayanzu haka ya jima da kammala karatunsa kuma yana aiki da wata ma'aikata ƙarƙashin gwamnatin tarayya a garin Abuja. Nidai sama sama nake kula yaya faisal bafa wai dan yayi min ba a'a sai dan kawai bana son wulaƙantashi, cikin haka naga wata sanarwa online wai wani kamfani yana buƙatar waɗanda suka iya computer zai ɗaukesu aiki, kamar wasa nayi applying cikin kwanaki biyu suka kirani interview kuma tun awurin suka ce sun ɗaukeni Monday zan fara fita aiki, wannan abu ba ƙaramin daɗi yayi min ba domin kamar irin a mazaunin trainers aka ɗaukemu mune zamu rinƙa koyar da ɗalibansu computer lokaci ƙanƙani na faso gari yanzu babu ruwana da tambayar su Annie kuɗin pads ko kuɗin powder domin albashi ake bamu mai tsoka banda allowances da muke samu, gaba ɗaya yanzu na zama wata busy kullum cikin bincike nake saboda koyarwa sai da research gudun kada students su tsuyeka ko su ƙureka, yaya faisal kuwa yau ina dawowa gida daga aiki naga saƙonsa ta kafar sadarwar Instagram wai gobe insha Allah zai shigo Kano anan ma zai yi weekend ya kira wayata bai same ni ba, shiru nayi ban amsa masa ba domin nidai bana farin ciki da wannan zuwan nasa haka kuma bana baƙin ciki, ƙawata tun ta ƙuruciya wato childhood friend mai suna Maryam ita na yi wa text massage na sanar da ita halin da ake ciki cewar ina da baƙo gobe, reply ta dawo min dashi cewa zata zo anjima inyaso sai mu san abin da zamu shirya domin tarɓarsa, kashe wayata nayi na jonata a charge sannan na saka kayan shan iska na fita, babu kowa a falon mama sai tv dake ta faman aiki ita kaɗai kai tsaye sashen Annie na wuce can na iske su suna girkin abincin dare tare da mai taimaka musu wurin aikace aikacen gida madina, zama nayi ina kallon Annie dake gyara gyaɗar miya,

GARIN DAƊI.....! Where stories live. Discover now