27
~~~Ƙurawa juna ido muka yi kamar yau ne muka fara ganin juna sai dai amma ni ba cikin idanuwansa nake kallo ba kunya bata barina in iya saka nawa idon cikin nasa,
"Mr man..... Ya kake?" na faɗa cikin tsokana,
"Baby..... Lafiya lau nake, kefa?" ya buƙata yana sake kallo na,
"nima lafiya nake"
"ok naji daɗin jin hakan.... Yau saura kwana nawa ma bikinmu?"
"ni ban san saura kwana nawa ba, bana counting" na faɗa cikin shagwaɓata da na saba yi masa ina turo baki,
"ni ina counting ɗin ai, sai anyi magana kice kina sona bayan gashi nan bama kya ɗokin zuwa kusa dani" shima ya faɗa cikin shagwaɓar, dariya na ƙyalƙyale da ita kafin nace,
"ashe dai kaima ɗin shagwaɓaɓɓe ne ban sani ba...."
"Ehh kin koya min" ya faɗa yana lumshe idanuwansa,
"ni ɗin na iya shagwaɓa ne?" na buƙata nima ina gyara kwanciya ta a gefen gado na,
"Baby ai kin iya shagwaɓa..... Yanzu ki bani labarin yau me kika yi dan ban ganki ba throughout sai yanzu......."
"yau babu abin da nayi sannan babu inda naje kawai kusan a kwance na wuni"
"Baki da lafiya?" ya buƙata yana kallona,
"lafiya ta Lau kawai dai bana jin hayaniya ne yau ɗinnan...."
"same here my dear..... Nima yau ɗinnan ina jin jikina very weak..... I don't know what's happening to me..."
"Sorry...."
"Amma baby meyasa gaba ɗaya ni dake muke jin yanayi iri ɗaya?" jin tambayar da yayi min naji gabana ya tsinke ya faɗi domin nima abin da ke kai kawo araina kenan dan kamar ya shiga zuciya ta ya gani,duk da haka ban nuna masa ba sai nayi murmushin jan hankali nace,
" ni da kai ai abu ɗayane ko ka manta ne? Hatta jinin dake gudana ajikinmu iri ɗaya ne, haka zuciyar dake bugawa a ƙirjina kai ma itace ke bugawa a naka ƙirjin... Kaga kuwa idan haka ne to ya zama dole mu rinƙa tsintar kanmu cikin yanayi guda" murmushi naga yayi tare da lumshe idanuwansa, a hankali naji ya furta,
"my clever baby..... You know what? Am eager naga munyi aure ina ganin ki kusa dani kina yimin irin waɗannan sweet sweet words ɗin"
Rufe fuska ta nayi da hannuna guda ɗaya cike da kunya,
"Yaushe zaka zo?" na tambaye shi bayan na buɗe fuskar tawa,
"kina nemana ne?"
"Ehh mana"
"to yaushe kike son ganina?" ya sake tambayata bayan ya miƙe daga zaunen da yake yana tafiya gefen titi,
"ko gobe ma...."
Ɗan shiru yayi alamar tunani zuwa caan naji yace,
"banda gobe..... I have a lot of things da zanyi gobe but insha Allah next tomorrow zan zo Kano...."
"Me zan dafa maka?"
"komai ma baby...."
"zaka sake zuwa idan ka tafi?"
"no, sai munyi aure sannan zan zo"
"baka da zance sai na aure..... Aure dai aure dai"
"to me kike so in ambata wanda ya wuce wannan? Shine a raina yanzu"
Har ya ƙarasa masallacin unguwar su muna hira kuma wani abun mamaki yau gaba ɗaya daga ni har shi kamar bama son yin sallama da juna dan sai munyi sallama sai mu sake ɗauko wata sabuwar hirar, da haka har aka kira sallar isha nan ya shiga salla, nima tashi nayi nai sallar har lokacin jikina a wani sanyaye yake kamar an aiko min da saƙon mutuwa,
Sake kirana yayi misalin ƙarfe 9 na dare yana sanar da ni ciwon kan dake damunsa addu'ar samun lafiya nayi masa sannan na ƙara da,
"wannan Hisnul Muslim ɗin da na faɗa maka wanda ka ɗauko a Play store ka duba shi da kyau duk wata addu'a da kake buƙata insha Allah zaka samu aciki...."
"Baby ai ban iyaba.... Ki koya min"
"Babu matsala bari mu fara tun daga addu'ar farko..."
Hannu nasa na buɗe bed drawer ɗina na ciro littafin Hisnul Muslim ɗina na buɗe muka fara tun daga addu'ar farko, ina faɗa yana faɗa sannan kowacce addu'a sai nayi masa cikakken bayani akanta, har 12 muka kai sannan nace yayi bacci haka ya ɗan huta, sallama muka yi yace zai yi baccin wai amma idan 3 tayi na tashe shi tunda nace ni ba bacci zanyi ba karatu zanyi, saida na fara yin salloli na nayi raka'a takwas sannan na fara karatun littafi mai tsarki, har 3 na kai idona biyu bayan na idar ina shirin kwanciya sai ga kiran Samz,
"Yanzu nake shirin kiran ka fa"
"Na tashi..... Nayi wani mafarki ne"
"Kayi addu'a?"
"Nayi"
"Allah yasa ya zama alkhairi"
Baccina na kwanta na shaƙa cikin kwanciyar hankali shi kuma samz ya kwana yana salla har asuba, washe gari da matsanancin zazzabi ya tashi da ciwon kai, tun yana iya amsa waya har yazo baya iyawa, ai hankali na idan yayi dubu sai da ya tashi, ji nayi kamar in yi tsuntsuwa in tafi Abuja in je in kula dashi, sai yau naji da ace zan iya janyo ranar bikin mu da na janyota ko dan in bashi cikakkiyar kulawa domin tun ina iya samun wayar tashi har ta kai ta kawo idan na kira sai injita akashe, sai zuwa dare sannan naji ta shiga kuma nan ɗinma ba shine ya ɗaga wayar ba wani friend ɗin shi ne Ahmad wanda suke yin aiki tare, shine yake yimin bayanin wai dama Samz ɗin yana da typhoid soo yanzun ma typhoid ɗin nasa ne ya tashi, nidai ban samu jin muryarsa ba sai da gari ya waye har lokacin yana asibiti ba a sallameshi ba, babu abin da ya sauya ko ya canja daga kulawar da muke baiwa junanmu sai dai zuwa Kanon da bai yi ba kenan kamar yadda yaci buri rashin lafiya yayi ta yi har tsawon wasu kwanaki, a ɓangare ɗaya kuma ya ware maƙudan kuɗi ya bawa matar uncle ɗinsa wadda ita ce ke haɗa lefe na ba lefe kaɗai ba kusan duk wani shirye shirye ma wanda ya shafi bikinmu a gidan uncle ɗinsa ake yi dan hatta gidan da zamu zauna ma uncle ɗinsa ya bawa wakilci akan ya samo mana gida mai daraja a Kano acikin manyan unguwanni wai tunda nace a Kano zan zauna, cikin lokaci ƙanƙani aka samu wani lafiyayyen gida a unguwar hotoro, gidane flat mai mutuƙar kyau da aji sabo fil ban san adadin miliyoyin da ya salwantar ba wurin mallakar gidan amma bai sanar dani ba har yanzu saboda yana cikin hali na rashin lafiya, ganin rashin lafiyar tasa ta tsananta ya sanya mahaifinsu da ƙannenshi tafiya wurinsa amma banda mommy wadda tace ko mutuwa zai yi yaje yaita mutuwar ita babu ruwanta, nima na so in je in duba shi amma ƴan gidanmu basu barni ba sai iya su kaɗai ne suka je, anty kuwa kullum daga gidan ta ake kai musu abinci asibitin da suke, ga biki nata ƙaratowa ga ango na kwance yana fama da kansa, ni kaina ni ɗinma bani da maraba da marar lafiyar domin kullum cikin damuwa da tunani nake gashi kullum addu'a ta kar Allah yasa in yi mafarki da ya warke saboda ance idan kayi mafarki marar lafiya ya warke to mutuwa yayi, duk abin da baka so sau da yawa shine yake faruwa, ina cikin bacci wanda ya ɗauke ni mintuna kaɗan da suka wuce nayi mafarki wai Samz ya rasu ai a wani hargitse na tashi hankalina a dugunzume, fuskata sharkaf hawaye sakamakon kukan da nasha cikin mafarkin, wayata na ɗauka jikina na rawa na soma kiran wayarsa........
YOU ARE READING
GARIN DAƊI.....!
RomanceTabbas lamarin so yana da rikitarwa domin yakan jefa zuciya so da kaunar wanda bai dace ba, a wani sa'ilin so na mayar da mai yinsa kamar wani zautacce Hakan shine ya faru da widat....!