SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI

422 62 5
                                    

17

~~~Hannu na sa ina murza idanuwa dan samun tabbacin shin dagaske ne ko kuma sune suke yimin gizo? Tabbas da gaske ne hakan ya sanya naji jikina ya fara rawa wadda ban san ko ta mecece ba,

"uhmm....... Kin yi shiru" ya sake turo min, cikin kasala na koma na kwanta sannan na bashi amsa da,

"Babu abin da ke damuna kawai dai na gaji ne...."

"Gajiya? Wacce irin gajiya?"

Murmushi nayi araina ina jinjina ƙwaƙwarsa da gani zai yi tambaya,

"Na gaji da zama ne wuri ɗaya kuma ina fama da ciwon kai" na bashi amsa ina murmushi ni kaɗai,

"ayya sorry....."

Murmushi kaɗai nayi kafin na buɗe saƙon da ya sake turo min,

"Zan iya zuwa in duba ki yanzu?" ɗan jimm nayi na kalli gefen da anty Salma ke zaune tana duba manual,

"Kar ka zo pls....."

"Why?" ya sake tambaya ta,

"Idan ka zo za ayi min faɗa"

"OK na gane, amma ina buƙatar wata alfarma daga gareki"

"Allah yasa zan iya"

"Ki turo min pics ɗin ki ina son ganin ki ban taɓa ganin fuskarki ba"

Ajiyar zuciya na sauke araina ina cewa idan wannan ne babu matsala abune mai sauƙi, pics ɗina na tura masa guda biyu nace shima ya turo min nashi, turo min yayi sama da guda biyar a ƙasan ya rubuta wai shi bai iya rowar pics ba, murmushi nayi na fara buɗesu ɗaya bayan ɗaya ina kalla, gaba ɗaya hotunan yayi bala'in kyau kamar ka sace shi ka gudu,

"Zan iya kiran ki yanzu?"

Shiru nayi kafin na bashi amsa da "ehh" yana buɗe saƙona sai ga kiran sa, nan naji gabana ya shiga faɗuwa, to ni yanzu me zan ce masa ni Maimunatu? Na shiga tambayar kaina ba tare da na ɗauki wayar ba har sai da na jiyo muryar anty Salma tana cewa ba kirana ake yiba? Cikin sanyin murya da tsoro wanda ban san ko na menene ba na ɗaga kiran,

"Hello...." na faɗa ina lumshe idanuwa na,

"Hello........ Ya jikin?" ya tambaya cikin harshen turanci,

"Da sauƙi....." na amsa ina sake gyara kwanciya ta,

"Kin sha magani?" kai na girgiza masa kamar yana kallo na,

"Meyasa baki sha magani ba?"

"Babu komai...."

"kin ci abinci?? “

" Ehh "

" Ban yarda ba..... Duk da baki son in zo dole zan zo zan kawo miki maganin headache ɗin"

"ka bar shi kawai.... Na gode" tun kafin in ƙarasa naji ya katseni da cewa,

"Zamu fara faɗa ba daga fara wayarmu yau, ki jirani nan da 5 minutes"

Katse wayar yayi nikuma na sake mirginawa ɗaya ɓangaren ina mamakin wannan al'amari, har 5 minutes ɗin tayi ta gota ban sani ba saboda ina can ina tunani, mamaki da al'ajabi sun taru sunyi min rubdugu har sai da naji ƙarar wayata alamar kira sannan na tuna,

"Zo ki karɓa....."

"kana ina?"

"Ina harabar hotel ɗin"

Tashi nayi zaune na kalli anty Salma nace mata ankawo min magani zan karɓo, ita duk tunanin ta Samir ne saboda taji muna hira da turanci nikuma bance mata ba shi bane na barta ahaka, a yadda nake haka na fita babu abin da na sauya ina sanye da dogon hijabi mai hannu har ƙasa. Irin faɗuwa da bugawar da gabana ke yi ba zata kwatantu ba, haka dai na daure na fita harabar hotel ɗin, caan na hango shi tsaye shi kaɗai dan haka cikin sassarfa na ƙarasa jikina yana ɗan rawa,ko da naje dab dashi sai na rasa me zanyi, shin zanyi masa sallama ne ko yaya?

GARIN DAƊI.....! Where stories live. Discover now