SHAFI NA TAKWAS

304 49 1
                                    

8

~~~Sai da na ɗan nisa kaɗan sannan na kalli iya zuciya ta cike fal da farin ciki nace,

"iya ban tari numfashinki ba kuɗin zasu kai har naira nawa...."

Jugum naga tayi kuma ta rafka tagumi alamar tunani, zuwa can ta ɗago ta kalleni,

"ƴarnan kuɗin nan fa da yawa dan tun a lokacin malam ɗan bahago aminin mahaifinsu cewa yayi muddin wannan malamin zai yi mana aiki to sai mun bada kuɗi sama da dubu dari biyar a lokacin, tun lokacin haka yace bare yanzu da komai ya sake tsananta abubuwa duk suka sake yin tashin gwauron zabi..... "

" hakane, amma iya a ina za asamu shi aminin baban domin a sake jin dahir ɗin inda za asamu shi mai maganin? "

" ehh to, a gaskiya yanzu ba nace ga takamaimai wurin da za a samu ɗan bahago ba domin mafatauci ne, yawo yake yi ƙasashen duniya, wuri daban daban yake zuwa yau yana nan gobe yana can, ko lokacin da mahaifin su hashimu ya rasu da iyalinsa tazo gaisuwa cewa tayi shi ɗin yana can ƙasar Mali, sanin takamaiman inda yake sai an dangano da iyalinsa.... "

" to iya a ina iyalin nasa suke? Ai sai aje a tambayo su inyaso sai su haɗamu dashi yayi mana bayani..... "

" to shikenan sai inje, suna can wajen Kano daidai wannan ɗan dajin dake tsakankanin kano da Katsina.... "

" yawwa iya sai ki daure kije"

"zan je in Allah ya yarda"

Tashi tayi taje taci gaba da ƴan aikace aikacenta domin Amira bata nan, shirun da muka yi gaba ɗayanmu nida shi na katse ta hanyar faɗin,

"wai lafiya kuwa naga kayi shiru ranka ya daɗe?"

Ɗan kawar da kansa yayi kafin ya bani amsa da,

"gaskiya maimunatu ɗawainiyar da kike yi dani tayi yawa...... Tunda muka haɗu ban taɓa yi miki wani abu na kyautatawa koda sau ɗaya ba amma ke kullum cikin yi min wahala kike, anya wannan tarayyar tamu babu ƙwara aciki?"

Tamke fuska nayi nasha kunu kamar yana kallona cikin ɓacin rai nace,

" ohhh kulawar da nake yi da kai ashe dama wahala ce ban sani ba? Ashe dama tsakaninmu akwai ƙwara ni ban sani ba? Hmm to ai gara da ka tunatar dani abin da na manta" daga haka na ɗauki handbag ɗina na zira takalmi na nayi gaba dama sai da na hanga na hango na tabbatar iya bata kusa,

A bakin ƙofa na tsaya daga waje domin nasan dole zai biyo baya na, ban kai ga gama tunanina ba kuwa sai gashi ya fito, baya na juya masa,

"Haba maimunatu menene kuma abin yin fushi daga magana? Kiyi haƙuri ban san cewa hakan zai ɓata miki rai ba"

Sai lokacin na juyo na kalleshi, ƙura masa ido nayi duk da nasan shi ba ganina yake yi ba, "baki haƙura bane? Ki sani duk punishment ɗin da kika ga yayi daidai da laifin da na aikata"

Dariya nayi na ɗan rausaya "ta yaya zan baka punishment? Ka rufa min asiri ban isa yin wannan ɗanyen aikin ba"

"waye ya faɗa miki cewa ɗanyen aiki ne? Karma ki ƙara faɗa"

"to shikenan bazan sake ba, nidai yanzu daga nan gida zan wuce, ka faɗawa iya na tafi"

"zan faɗa mata kin yi fushi shiyasa ko sallama baki yi mata ba"

"nayi fushi abaya amma yanzu na huce, kuma dama ai kaine ka saka nayi fushin"

"to ina neman afuwa"

"kin wuce wannan matsayin agareni, duk laifin da za kiyi min komai girmansa na yafe miki tun kafin kiyi"

"ka jika ko, so kake ka shagwaɓani kenan inyita cin kare na babu babbaka tunda an ce an yafe min"

"ki yi min duk abin da kike so in dai nine na yafe miki"

GARIN DAƊI.....! Where stories live. Discover now