16
~~~Misalin ƙarfe 3 da wasu ƴan mintuna muka isa cikin garin Iko cunkus ɗakin tsumma, awani katafaren haɗaɗɗen hotel muka sauka mai suna MORNING STAR HOTEL wanda acikine za a gabatar da training ɗin kuma nan suka namu masauki, bedroom guda ɗaya muka kama nida Anty Salma domin na faɗa mata nidai tsoro nake ji bazan iya zama ni ɗaya a ɗaki ba,
Abinci Anty Salma tayi mana order bayan mun ci munyi wanka na ɗan kwanta domin huce gajiya, ina kwance ina tunanin rayuwa ta da irin yanda komai na rayuwa ya juya min baya kuma yayi min atishawar tsaki, komai ya tsaya min cak bana jin daɗinsa kullum cikin tunani da damuwa nake na kasa dainawa, ƙarar wayata ce ta katse min tunanin da nake yi nan na ɗauka ina murmushi saboda ganin Anty ce,
"Matafiya an sauka lafiya?"
"Lafiya Lau anty yasu Aslam"
"Alhamdulilah, to Allah ya huta gajiya"
"amin Anty sai munyi waya"
Katse wayar nayi ina sake shiga cikin sabon tunani domin shine aikina ahalin yanzu, daren ranar tun 8:30 nayi bacci saboda tsabar uwar gajiyar da nake tattare da ita, zuwa asuba ni nafara tashi sannan na tada Anty Salma, zama nayi nai karatun alqur'ani har zuwa lokacin da rana ta soma ɓullowa lokacin tuni anty Salma ta shirya, nima wanka nayi na shirya tsaf cikin doguwar gown dark purple banyi wata doguwar kwalliya ba in banda powder da lipstick da na shafa ko kwalli ban saka ba nayi rolling da squeeze veil baƙi na saka takalmi toms baƙi, face mask na saka a fuska ta kamar yadda dokar training ɗin take dole asaka mask sannan a bayar da tazara, side hand bag ɗina na rataya light purple bayan na fesa turaren black oud,
Anty Salma dai tsayawa tayi tana kallona tare da sakin murmushi nima kallonta nayi kuma naji shigar ta ta burge ni domin doguwar riga ta atamfa ta saka tayi rolling da babban mayafi da ganin ta Kaga matar aure kamila,
"Widat ƴar gayu, karfa muje ki haɗa mana go slow awurin training ɗin"
Dariya nayi na wuce gaba tana biye dani a baya,
"Lallai anty Salma abinma harda tsokana"
"tsokana ko gaskiya? Kinga yanda kika sha kyau?"
Murmushi nayi bance komai ba muka jera har cikin babban hall ɗin da zamu gudanar da training ɗin wanda tuni har mutane sun fara zuwa a nata registration, kujera muka samu muka zauna kusa da wasu mata suma su biyu, ido na shiga tsittsillawa ina kallon cikin hall ɗin da mutanen dake cikin sa, bayan kamar mintuna biyar da zaman mu wani farin guy yazo saitinmu ya sha ƙananan kaya,
"kunyi signing?" ya tambaye mu cikin turanci, bashi amsa muka yi da cewa "a'a" mu ɗinma cikin harshen turanci,
Wani ya ɗagawa hannu wanda nidai banga ko wanene ba domin kaina yana ƙasa ina duba wayata ina kallon status ɗin yaya Abdurrashid babban yayanmu wanda ke bin Anty shima lawyer ne amma na gwamnati ba irin sauranba yana can Federal University dake Enugu yana lecturing inda yake koyar da Administrative law, jin anty Salma ta taɓani ya sani karɓar pen ɗin hannunta na rubuta sunana da phone no da state sannan nayi signature nasa date, duk yana tsaye yana kallo na ko ince suna kallo na domin bashi kaɗai ke kallo na ba har da wannan farin guy ɗin na farko wato wanda ya fara zuwa wurin mu. Saida aka gama registration sannan aka buɗe da addu'a aka ɗan yi jawabai jawabai na maraba tare da maƙasudin wannan training wato aiki ne da zamu bi mu lissafe tare da ƙidaya dukkanin kamfanoni da masana'antu haɗida shaguna dake kowacce jaha, daga nan akace za ayi breakfast sai a fara training dama already an shirya wurin cin abinci,
Ko a gida ni ba kasafai nake cin abubuwa ba barkatai musamman masu maiƙo domin sukan sanyani rashin lafiya irin ciwon ciki, ulcer da sauran su, ganin pepper chicken da donuts sai kayan tea ya sani yatsina fuska, iya naman kaɗai na samu na ci sai ruwan tea, na tattara kayan fulawar na mayar musu abin su, bayan an gama breakfast aka fara training wanda saida aka fara raba mana manual ɗin da zamu yi amfani dasu, tunda muka zauna ba mu tashi ba sai da lokacin salla yayi awurin salla ne muka rinka haɗuwa da mutane sosai waɗanda suka zo daga Kano amma kuma ba mu san su ba suma basu sanmu ba, bayan an dawo daga salla aka yi lunch wanda wannan ɗinma dai ɗan tabawa nayi kawai saboda yanzu bana iya cin abinci komai daɗinsa, Anty Salma dake kusa dani tashi tayi dan zuwa bathroom, kamar jira yake sai gashi yazo kusa dani,
YOU ARE READING
GARIN DAƊI.....!
RomanceTabbas lamarin so yana da rikitarwa domin yakan jefa zuciya so da kaunar wanda bai dace ba, a wani sa'ilin so na mayar da mai yinsa kamar wani zautacce Hakan shine ya faru da widat....!