24
~~~Ƙarshen tashin hankali na shige shi irin wanda ban taɓa shiga ba dan ko lokacin da Hashim ya yaudare ni ya kuma juya min baya ban samu kaina cikin ƙunci damuwa da tashin hankali kwatankwacin wannan ba, abubuwa ne goma da ishirin suka taru suka yimin yawa cikin lokaci ƙanƙani na lalace na fita kamannina rabona da Samz kuwa tun ranar da su Abba suka yimin iyaka dashi dan wayata ma na kasheta na ajiye bana amfani da ita gaba ɗaya nabi na takura kaina, aikin da muke yi kuwa daƙyar na iya ƙarasa shi muna gamawa kuma na kwanta asibiti sai da nayi sati biyu ana yimin ƙarin ruwa da allurai sannan muka koma gida kuma har lokacin ba wai na manta da Samz bane ko na daina sonsa a'a har lokacin yana nan maƙale acikin raina, ni kaina ban san wanne irin so nake yi wa wannan bawan Allah ba ga yawan mafarki dashi da nake yi wanda har ya zame min jiki dan kusan kullum sai na ganshi cikin mafarki na. Tun bayan da aka sallamo ni daga asibiti ban sake yin lafiya ba kullum ni kenan kwantarwa a asibiti kamar wata me sikila kullum cikin rashin lafiya nake bini bini zaka ganni da cannula a hannu cikin haka aka saka ranar bikin ƙawalli da yaya Abdul Hakim nidai kawai lallaɓawa nake yi amma ba wai wata lafiya gare ni ba, ƙawalli kuwa cemin take dan Allah in taimaka kar in ƙara kwanciya gabannin bikin nan, duk lokacin da ta faɗi haka murmushi kawai nake yi ko in yi dariya danni ji nake kamar tawa ta kusa ƙarewa saboda wannan jinyace jinyacen da nake tayi bana cikakken wata guda sai an bani gado a hospital an ƙaƙƙara min ruwa Annie duk fushin da ta ɗauka dani yanzu ta sauko kullum cikin rarrashi na take tana cewa in kwantar da hankali na in dai akan Samz ne zasu aura min shi muddin idan ya musulunta dama ba wai basa sonshi bane addini ne bai bada damar inyi wata mu'amala dashi ba bare har maganar aure ta shigo in dai bai musulunta ba, kullum nasiha take yimin akan in rage damuwa in cigaba da addu'a tare da neman zaɓin Allah amma bata jin daɗin wannan rama da rashin lafiyar da kullum nake cikinta daga ƙarshe tace ko zan je gidan Anty inyi kwana biyu a'a nace mata saboda bana son zuwa ko ina a yanzu nafi son in zauna a gida,
Shima Abba kwanaki uku da suka wuce da kansa ya kirani yayi min nasiha akan in saki raina indaina damuwa wai idan ma akan maganar auren da yace zai yi minne da duk wanda yasamu ya fasa ba zai aura min wanda bana so ba zai jira har lokacin da zan samu wanda raina ya kwanta dashi kuma na gabatar musu dashi a matsayin wanda nake so saboda shi duk a tunaninshi wannan maganar ita na saka a raina take damuna nan kuwa ba haka bane tsabar tsananin ƙulafucin son Samz ne keta wahalar dani yana ɗawainiya da rayuwata wanda ni kaina ban da yanda zanyi, tunda jimawa dama muka ƙulla ƙawance da zaman ɗaki bani da aiki zai zama a ɗaki dan sai ka zo gidan ka wuni harma ka kwana baka san ina gidan ba sai idan Abba ne ya aika a kirani ko su mama,
Kamar koda yaushe yauma ina kwance a ɗakina bayan na gama gyara shi na wanke toilet na yanke farata na, ƙawalli ce ta shigo bakinta ɗauke sa sallama ganina kwance da cannula a hannuna ya sata ɓata fuska tana faɗin,
"ubangiji Allah dai yasa lafiyarki ƙalau...."
"lafiya ta Lau, me kika gani?"
Zama tayi gefen gado na tana shaƙar ƙamshin turaren tsinken da na kunna wanda ke tashi daga jan jikin ƙofar toilet ɗina,
"na ganki ne a kwance, wai ƙawalli me yasa zaki rinƙa zama shiru? Ki ɗauko wayarki haka mana ko kya rinƙa rage kaɗaici"
"uhmm uhmm bana buƙata,ko ranar Abba ma sai da yace zai bani kuɗi in sai waya nace ina da ita, kawai bana so ne yanzu"
"Amma widat wannan damuwar da kike ciki fa tayi yawa dan Allah ki rage, ai idan so cuta ne to haƙuri magani ne fa"
"hakane.... Allah ya bani iko"
"amin, ki tashi muje ki rakani kasuwar kwari dan Allah"
Ban binciki me zata siyo ba na miƙe na shirya muka tafi, sai a hanya take sanar dani wai material zamu siyo wanda zata saka ranar dinner jiya da daddare yaya Abdul Hakim ya tura mata kuɗin, nice na zaɓi duk abubuwan da zata saka tun daga kan material ɗin zuwa takalmi, da duk wani abu da zata saka ranar bikin sai dab da magriba sannan muka baro kasuwa wanda tun zuwanmu wani yaro ya maƙale min shagon na mahaifinsu ne daga ƙarshe ma shi ne ya mayar damu gida ƙawalli sai wani biye masa take yi ni kuwa a raina nace wallahi yamin yaro nan take samz ya faɗo min namiji har namiji ashe ba rabona bane.
***Jikinta har rawa yake saboda bala'i da masifa baka jin komai sai ƙarar sautin masifar ta wanda ta cika falon dashi,
"Ni Deborah ni za ayiwa wannan munafurcin da rainin hankalin? Ni yau kake faɗawa zaka bar addinin da ka taso aciki zaka koma wani? Wannan ba zai taɓa faruwa ba, ni ban haifi ɗan da zai zama musulmi ba Samuel.... Idan har mahaifinka shine ya zuga ka ko kuma yayi maka huɗuba to ina son in tunatar dakai abin da ka manta, kana dai ganin irin ƙyama da tsanar da dangin mahaifinku ke nuna mana, ko abinci nayi na basu basa ci idan abu ya fito daga hannuna basa ci, duk duniya bani da maƙiya sama dasu amma yanzu shine zaka zo kace min zaka musulunta...."
Sunkuyar da kansa yayi ƙasa sannan cikin sanyin murya yace,
" Am sorry mommy..... Ni yanzu na girma na san abin da ya dace da wanda bai dace da rayuwa ta ba and Daddy ba shine ya nemi da in musulunta ba in fact ko maganar ma bai sani ba, sannan mommy ai kowa yana da ikon zaɓar addinin da yayi niyya....." tun kafin ya rufe bakin sa yaji ta ɗauke shi da mari wanda rabon da tayi masa wani abu mai kama da wannan tun kafin ya mallaki hankalin kansa dan bama zai iya tuna rabon da ta ɗora hannunta a kansa ba da sunan mari ko duka dan duk cikin ƴaƴanta babu wanda take so kamar sa gashi yana tsananin jin tausayinta dan ko abu yaci ya rage sai ya kawo mata amma yau shine ke ƙoƙarin watsa mata ƙasa a ido wai zai koma addinin babansa,
"Samuel ni mahaifiyarka ni kake faɗawa kana da ikon yin duk addinin da ka zaɓa? Wallahi in dai nice na haife ka to babu kai babu musulunci idan kuwa ka bijirewa magana ta to sai na yi maka addu'ar la'anta...."
"Kiyi haƙuri mommy amma nikam daga yau na bar addinin kiristanci...." daga haka ya tashi ya fita yana fita mahaifinsa shi kuma na shigowa,
"Maman Maryam me yake faruwa nake jiyo hayaniya tun daga gate?"
Wata uwar harara ta watsa masa idunwanta har juyawa suke dan ɓacin rai,
"Allah ya isa tsakanina daku kai da ɗan uwanka da kuka haɗa baki zaku rabani da ɗana kuma wallahi sai kunga abin da zai biyo baya dan ba yafewa zanyi ba..."
Cikin baƙin ciki da ɓacin rai ta faɗa ɗaki ta ɗauko Bible ɗin ta ta fita tana kuka bako ina zata je ba sai church ɗinsu wurin pastor dan ayi ma ɗan ta addu'a asirin da aka yi masa ya karye kamar yadda take tunani, dama tun farko wannan dalilinne yasa ta tsani uncle ɗinsu Samuel saboda shida iyalansa gaba ɗaya musulmai ne kuma tana zargin da sa hannun sa wurin musuluntar da Samuel ke ikirarin zai yi,duk da bata bari yaranta su raɓi gidan uncle Sadiq kamar yanda suke kiransa amma yau shine za a haɗa baki a cutar mata da ɗa, ita fa ko hutu bata bari yaranta suje masa duk da suna kusa, lokacin da taje church rufuwa akayi akanta ana yi mata addu'a sakamakon kururuwar da ta shiga da ita. Shi kuwa Samz ɓacin rai da damuwa ne suka sa ya ɗauki jakar sa ya bar gidan kuma aranar ya koma inda ya fito wato Abuja.
***
Shirye shiryen biki muke yi sosai daga gidanmu har gidan su ƙawalli, nice akan komai wanda ya shafi amarya da ƙawayenta danma bama shiri da angon sosai duk abin da na buƙata sai munyi faɗa kafin ya bani wani lokacin ma sai nayi fushi sai ƙawalli tasa baki sannan zai bada, daga ni har ƙawalli mun zama busy domin biki saura sati ɗaya amarya har anfara yi mata gyaran jiki tun sati biyu da ya wuce, nidai cikin Ikon Allah tunda bikin ya ƙarato ban kwanta jinya ba,Yau tunda na tashi ban zauna ba nice gidan ƙunshi da kasuwa nice wurin teloli dan can gidan ƙunshi ma nabar ƙawalli, na karɓo ɗinkunan nawa na dawo kenan ina shiga gida na haɗu da Bishra sai na ji tana cewa,
"yawwa gama ta nan ta dawo... Ga yaya widat ɗin nan"
"menene?" na buƙata ina riƙe da kayana da na ƙawalli wanda na karɓo,
"baƙo kika yi.... Yana falon Abba"
Gabana ne naji ya yanke ya faɗi dan duk baƙon da zai tsallake side ɗinsu yaya Abdul Hakim yawuce Guest room ya tafi har falon Abba kasan ba ƙaramin baƙo bane, ni dai haushi ne ya kama ni dan nasan ta yuyu wani ne ya zo neman aure na kuma sai yabi ta sama, raina a ɓace na shiga falon Abba, tabbas na hango mutum kan kujera amma ban ko kalle shi ba na nemi wuri na zauna, sanye nake da English wears riga da skirt sai nasa dogon hijabi wanda yaje min har ƙasa, wasa nake da hannuna wanda ya sha jan lalle da baƙi, fuskata fayau sakamakon ramar da nayi ta sanadiyyar jinyar da na shassha,
"Baby...." Kamar daga sama na jiyo amon muryar da kullum nake bege wadda ko daga bacci na tashi idan na jita sai na shaidata, cikin sauri tare da bugun zuciya wadda zuciya ta ke yi na waiwaya inda najiyo sautin dan ganin shi ɗin ne da gaske ko yaya?.............
YOU ARE READING
GARIN DAƊI.....!
RomanceTabbas lamarin so yana da rikitarwa domin yakan jefa zuciya so da kaunar wanda bai dace ba, a wani sa'ilin so na mayar da mai yinsa kamar wani zautacce Hakan shine ya faru da widat....!