SHAFI NA ASHIRIN DA TARA

487 72 19
                                    

29

~~~Cikin farin ciki da ɗoki nake shaƙar iskar garina kuma tushena wato Kanon dabo tarin Allah, sai murna nake yi wadda ban san ko ta mecece ba amma ni dai na san ba murnar aure bace,

Lokacin da naje gida tun daga ƙofar gida na san anyi gyara na musamman a gidan domin gashi nan ya sha sabon fenti ko ina an gyareshi tsaf, ƙawalli tana gidan dan haka rungume juna muka yi muna tsalle yaya Abdul Hakim da fitowarsa kenan daga sashen Annie ya bimu da harara wadda ba mu san ma yana yi ba, sakina tayi tana ƙare min kallo sakamakon canjawar da nayi nai ƙiba da haske saboda supplements din da Anty ke bani na gyaran jiki da sauran abubuwa ita kanta bata san yawan kuɗin da ta kashe ba wurin gyara ni tun daga kan su dilke, magungunan infection, na gyara fata da dai sauran su,

"Tabdijam...... Samz zai kwashi lagwada...." ta faɗa a hankali ta yadda wani ba zai jiyo ta ba, harararta nayi nace "ya ranki"

"Wataƙila daren ranar da aka kaiki ki samu ciki ƙawalli....."

"Ta Allah ba taki ba ƙawalli......insha Allah sai bayan shekara biyu zan haihu"

"a wannan samz ɗin naki zaki kai shekara biyu baki haihu ba?"

Kallon yanda ta riƙe haɓa kamar wata tsohuwa nayi dariya nayi nai gaba abina ta biyo baya na, gani nayi gaba ɗaya ƴan gidanmu sun zama busy dan ban samu mama agida ba wai sun fita kasuwa ita da Anty Salaha sai iya Annie kaɗai da sauran abokan arziƙi wadanda suka zo ganin kaya dan har yau ba agama zuwa kallo ba, ni dai ko ta kan kayan ban bi ba sai wadanda aka dinko min su na dudduba ciki harda wanda zanyi fitar biki dasu na kamu da dinner, ƙawalli ke tsara yanda shigar tawa zata kasance, ni dai duk jikina yayi la'asar da ganin dagaske gidan zan bari in tafi gidan samz ada babu abin da nake so irin maganar aure na dashi amma ahalin yanzu idan ƙawalli tayi min faɗa ma muke yi ita kuma tunda ta gane shikenan bata da aiki sai tsokana ta, gaba ɗaya ji nake auren ya fice min arai kamar a sake ƙara watanni amma na san hakan ba zata taɓa faruwa ba, ƙawalli na kalla dake ta haɗa min kaya na wuri ɗaya ina daure da towel da hijabi a jikina fitowata kenan daga wanka,

"yaushe angon zai shigo ne?"

"oho masa ni na sani ne" na bata amsa ina ƙokarin zama gefen gado, dariya naji ta fashe da ita,

"ohh Allah me iko wai ashe dama zanga widat haka? Ashe wannan ranar zata zo da zata rinƙa jin tsoron Samz"

"Wallahi ji nake inama a ɗaga....." na faɗa ƙwalla na taruwa acikin idanuwa na dan duk da ina sonsa yanzu ji nake bana son haɗuwarmu kwana kusa balle har mu zauna inuwa ɗaya,

"ai idan aka ɗaga ina jin sai an baki gado a asibiti.... Mutumin da kike ta jinya a kansa yanzu kuma kice wai so kike a ɗaga...."

Ban sake tanka mata ba kawai na fara kuka, lallashi na ta fara tana cemin to kuma menene abin kuka har itama ta fara a haka anty ta shigo ta same mu,

" kin jimin yara da shashanci kunzo kun zauna kun ƙule a ɗaki kuna kuka kamar waɗanda aka yiwa mutuwa.... Dan Allah ni karku ɓata min lokaci ungo ku zaɓa....."

Wayarta ta miƙo mana, decorations ne kala kala take son mu zaɓi kalar wanda za ayi, ƙawalli ce ta zaɓi wani kamar na gargajiya gargajiya amma yayi bala'in kyau, karɓa anty tayi tana cewa,

" Ranar kamun wanne kaya ma zata saka? Ungo ku zaɓi na dinner "

"Golden ne Anty" ƙawalli ta bata amsa, sake zaɓar na dinner ɗin tayi ta miƙa mata wayarta ta fice ta barmu kamar yadda tazo ta same mu, kafin kace mi har magriba tayi wanda hakan ke sake tada min da hankali,

Bayan tafiyar ƙawalli ɗakin mama naje muka zauna tana ta haɗa kan kayan da ta siyo na amfanin kitchen wanda za a tafi dasu jere gobe laraba ranar Alhamis za ayi kamu juma'a dinner asabar kuma za a ɗaura aure ayi yini akai amarya ɗakinta, duk ji nake kamar inyita kuka har sai an fasa bikin nan yanzu Ala basshi nan gaba sai ayi, shi kansa samz ɗin yanzu bana doguwar hira dashi dan gaba ɗaya haushinsa nake ji daga ya kirani zan tambayi menene sannan ina gama bashi amsa zan kashe wayata, ba wai laifi yayi min ko daina sonshi nayi ba a'a haka kawai nake jin bana son kusancinmu dashi, duk da hakan da nake yi masa shi baya zuciya ya kan kirani kamar yadda ya saba, dan ko yanzu da na zo kwanciya saida ya kirani amma nace bacci nake ji, cewa yayi to shikenan in kwanta in yi, kashe wayar nayi gaba ɗaya ina ta juye juye nama kasa baccin gaba ɗaya, daga ƙarshe hijabi na nasa na fita, sashen Annie na shiga na buɗe ɗakin bishra wacce ke kwance tana bacci sakamakon zirga zirgar da itama tasha yau, kusa da ita naje na kwanta naja bargo na lulluɓa sai hawaye, na jima ina zubar da hawaye kafin bacci ya ɗauke ni wanda bani na tashi ba sai bayan asuba irin ƙarfe 6 ɗin nan wannan ɗinma anty ce ta shigo da ban san ranar tashin mu ba daga ni har Bishran, ɗakina na koma nayi wanka a gurguje bayan nayi salla, sama sama nayi breakfast sannan na tafi gidan ƙunshi nida Anty wadda tayi dropping ɗina sannan ta wuce kasuwa ta can kuma zata wuce gidana, sai bayan da aka gama min ƙunshin sannan ƙawalli ta sameni a gidan,

GARIN DAƊI.....! Where stories live. Discover now