*12*
~~~Kamar kullum cikin shiga ta alfarma na shirya nasha turare nayi breakfast sama sama sannan na fita, wayar Hashim nake ta kira amma no answer baya ɗauka hakan yayi mutuƙar bani mamaki domin a iya sanina baya ƙin ɗaukar waya inda yana kusa, canja shawara nayi nace da mai napep ya sauya akalar napep ɗin a maimakon hanyar office mu kama hanyar gidan su Hashim,
Da fara'a tare da sakin fuska Iya ta tarbeni muka gaisa banji motsin kowa ba sai nata ita kaɗai da alama gidan babu kowa,
"Iya su Amiran basa nanne?" na buƙata kaina na ƙasa,
"Amira ta tafi makaranta Maimunatu...... Shi kuma Hashimu yana ɗaki ina jin bai tashi ba bare in duba shi in yi masa magana kin zo"
Wani ɗan ƙaramin ɗaki mai ɗauke da wani tsohon koɗaɗɗen labule ta shiga, yana kwance yana lallatsa sabuwar wayar iPhone ɗin sa yana hira da hajja Sharifa wacce ke sanar dashi wai da kwaɗayin wainar gero ta tashi irin wadda ake saka garin ƙuli ƙuli aciki a ina zai samo mata?
"Au Hashim dama idonka biyu? Ai na ɗauka bacci kake yi?"
"wallahi idona biyu Iya...."
"ehh ai gashi na gani, baka ji shigowar Maimunatu ba?"
"naji mana"
"Haka fa, to amma kaji zuwan nata shine ba zaka fito ku gaisa ba?"
"Iya ai ke ta zo gaisarwa, ba fa danni ta zo ba"
"Eh lallai, to wai tsaya wannan dalleliyar wayar ita kuma daga ina? A ina ka samota?"
"Iya wani abokin kasuwanci nane ya bani, yanzu ma muna sake tattaunawa ne game da yanda kasuwancin zai gudana, dan Allah kice kawai ta tafi idan na samu lokaci zan nemeta yanzu inada abun yi"
"Yayi maka kyau Hashim, yau kuma Maimunatun za a cewa ta tafi? Ashe baka da kirki ban sani ba? Yarinyar ta tsallake gida fiye da dubu tazo namu amma kake furta irin waɗannan maganganun? To idan ka gadama ka fito, idan kuma baka gadama ba karka fito kayi zamanka "
Daga haka ta fito daga cikin ɗakin cike da ɓacin rai, duk abubuwan dake faruwa a kunnena ne kuma naji komai domin ɗakin bai da wani tazara da inda nake zaune,
Iya ƙokarin ɓoye ɓacin ranta tayi ta ce min wai yana zuwa amma abun takaici saida ya shafe mintuna 15 bai fito ba, miƙewa nayi ina sake duba agogon hannu na saboda lokaci yaja,
"Iya zan ƙarasa wurin aiki na makara sosai kar makarar tayi yawa" cike da damuwa da ɓacin rai naji tace,
"to shikenan Allah ya bada sa'a ta tsare sai kin dawo"
"amin Iya" na faɗa ina ɓoye damuwa ta dan har ga Allah naji haushi sosai ba kaɗan ba.
Sai bayan da na fita sannan Hashim ya fito daga cikin ɗaki daga shi sai singileti da gajeren wando,
"Da kyau butulu, ai na zaci ko zaka yi butulci bai kamata ka yi wa wannan Yarinyar ba haka bai kamata ka yi wa Allah butulci ba.... Tunda ka samu ido ka daina zuwa makaranta, ka daina zuwa majilissin ɗaukar karatu, ka daina zuwa masallaci, ka daina tashin asubah, anya Hashimu ka ɗauko hanya mai ɓullewa? Yanzu abin da ka yi wa Yarinyar nan kayi daidai kenan? "
" Iya nifa banyi komai ba, ba gashi na fito ba, tana ina? "
"Zama zatai tayi tana jiranka sai kace dan kai aka halicce ta? Wallahi tun wuri ka maida hankalinka, baka da aiki sai yawo, wuni zaka yi kana yawo na ba gaira bare ɗan dalili, ba zaka dawo gidan nan ba sai dare kuma daren ma ba na kusa ba, to wallahi ka san inda yake yi maka ciwo.... "
YOU ARE READING
GARIN DAƊI.....!
RomanceTabbas lamarin so yana da rikitarwa domin yakan jefa zuciya so da kaunar wanda bai dace ba, a wani sa'ilin so na mayar da mai yinsa kamar wani zautacce Hakan shine ya faru da widat....!