SHAFI NA TALATIN DA ƊAYA

424 65 6
                                    

31

~~~Cikin barcina naji wasu lafiyayyun tagwayen kisses bisa kumatuna zuwa kan lips ɗina waɗanda suka yi sanadiyyar katsewar daddaɗan baccin da nake yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, a hankali na buɗe idanuwa na dake cike da tarin baccin gajiya nan idanuwan nawa suka sauka kan fuskarsa inda yake durƙushe gaban gadon yana kallo na,take ƙwaƙwalwata tayi hanzarin tuno min da a inda nake da kuma halin da nake, cikin azama na sake jan duvet na tuƙunƙune, kau da kansa yayi,

"ki tashi kiyi salla.... We are late" ya faɗa yana ƙoƙarin tashi daga gaban gadon, kai tsaye wurin da aka keɓance domin yin salla ya nufa sai lokacin na kula da yayi alwala tun tuni ashe, cikin rashin sakin jiki na lalubo rigar bacci na nasaka sannan na sauko daga kan gadon ina mamakin irin baccin da muka sha wanda ya haddasa mana wannan makarar dan har gari yayi haske tarr,

Bathroom na shiga na yi alwala da ruwan ɗumi sannan na fito lokacin har shi ya idar yana karatun alqur'ani mai tsarki, gefenshi naje nima na tada salla bayan na saka dogon hijabi har ƙasa wanda ke ajiye wurin dama duka kayana ƙawalli da Bishra sun shirya min komai sun saka shi inda ya dace a ajiye sh.

Har nayi sallama bai gama karatun da yake yi ba, zikirin da annabi ya koyar na safiya da marece nima na fara karantawa ina zaune kusa dashi, juyowa yayi ya kalleni nikuma na sunkuyar da kaina,

"Good morning...." na ce dashi kaina a ƙasa,

"morning my baby.... How was your night"

Shiru nayi ban amsa ba sai ma casbaha da na ɗauka zan soma ja, hannun shi naji yasa ya kwantoni gefen jikinshi,

"Baby....... Zan je Kaduna yanzu.... Insha Allah zuwa yamma i will be back to you"

Sai lokacin na ɗaga idona na kalle shi jin abin da ya faɗa,

"me ya faru a Kaduna?"

"mommy bata da lafiya, zan je in dubata"

Duk da ban san mahaifiyarsa ba sannan babu abin da ya taɓa haɗani da ita sai da naji gabana yayi masifar faɗuwa, cikin dauriya tare da ƙarfin hali nace,

"In shirya mu tafi tare?"

"no baby.... Kiyi zamanki zan je ni ɗaya, za muje tare wata rana mu gaisheta"

Ɓata fuska nayi bayan na shagwaɓe zan yi masa shagwaɓar da na saba,

"Sorry baby.... Come here... Yanzu ai inada hanyoyi da yawa na rarrashinki" ya faɗa yana ɗagoni gaba ɗaya zuwa kan jikinsa,

"Ni na haƙura" na faɗa ina ƙoƙarin zamewa,

"no..." yace dani yana kissing ɗin goshina, sakina yayi ya tashi ya shiga toilet, karatun alqur'ani na cigaba da yi ina nan zaune har ya fito daga shi sai short iya cinya shiyasa tunda na kalle shi sau ɗaya ban ƙara ba na mayar da kaina ƙasa duk da yanata yimin magana jifa jifa, fita yayi zuwa ɗayan bedroom ɗin mintuna kaɗan sai gashi ya dawo riƙe da kayanshi, light blue ɗin shadda da hula, sakawa yayi sannan na tashi da zummar zuwa kitchen dan in dafa masa ko ruwan zafi ne ya sha tea, hannuna ya riƙo yana fesa turaren dake kan mirror ɗina,

"ina zaki je?"

"Zan duba ko da akwai abin da zan baka a matsayin breakfast"

"no, ba zan ci komai ba, is too early ai"

"ko tea kasha to" na sake faɗa ina kallon fuskarsa,

"no, sai naje Kaduna insha Allah, ki kwanta kiyi bacci"

"Allah ya kai ka lafiya ya dawo dakai lafiya, ka gaida mommy ka dubata, Allah ya bata lafiya, agaida su daddy da kowa da kowa"

"Duk zasu ji"

GARIN DAƊI.....! Where stories live. Discover now