10
~~~Na jima goshina a ƙasa ina tasbihi ga ubangiji na, ina ji Hashim na faman yi min karin bayani kan yadda al'amarin ya kasance amma ban iya amsa masa ba har sai da na ɗago daga doguwar sujjadar da nayi,
"Ya naji kin yi shiru ne Abar sona?"
Wasu hawayen farin ciki ne suka sake zubo min fuska ta kuma ɗauke da murmushi,
"Farin cikin halin da na tsinci kaina shi ne ya hana ni furta koda kalma ɗaya...."
"haƙiƙa ke wani sashe ne mai mutuƙar muhimmanci a rayuwa ta, Sam bani da bakin gode miki....."
"Ka daina yi min wannan godiyar Hashim.... Allah shi ya ƙaddara hakan zata kasance ni kawai dai ɗan taimako nayi dan haka give thanks to Allah"
"Maimuna kenan..... Ba zaki gane ƙarfin sonki acikin zuciya ta ba har sai ranar da na aure ki da yardar Allah, zan kula dake kamar yadda uwa take kula da jaririnta, zan lallaɓaki tamkar yadda ake lallaɓa ƙwai akan tire....."
Dariya nayi na koma na jingina da jikin gado na cikin farin ciki,
" Allah ya baka ikon kula dani fiye da hakan, ka san me yasa nake farin ciki da buɗewar idonka? "
" a'a sai kin faɗa "
" Ranar da muka fara haɗuwa ka sanar dani koda kana cikin damuwa mutane basa ganewa saboda ba idanuwanka suke gani ba, yanzu kuwa Kaga zaka ga idon kowa sannan kowa zai ga idonka.... "
" hakane amma ni dalilina ya sha baban da naki...."
" kai menene naka dalilin? "
" ni saboda zan rinƙa kallon kyakkyawar fuskarki.... Sannan a duk lokacin da kika yi min kwalliya zan gani kuma zan bada tukwici"
Wani ƙarin farin cikinne naji yana sake lulluɓeni. Mun jima muna hira dashi kafin daga bisani muka yi sallama domin lokacin sallar ishah yayi tuni aka jima da kira, sai da na jima ina addu'a tare da yi wa Allah godiya sannan na tashi daga kan abin salla ta, tsabar farin ciki yau kasa bacci nayi sai juye juye har garin Allah ya waye, duk wanda ya ganni ya san ina cikin farin ciki saboda annurin dake kwance kan fuska ta,
Lokacin da na fita domin zuwa aiki kuwa saida na tsaya nayi sadaka sannan na wuce office, wuni muka yi muna waya da Hashim wanda ke sanar dani wai zuwa gobe insha Allah zasu kamo hanyar gida, nidai kam bakina gaba ɗaya ya kasa rufuwa kawai jiran dawowarsu nake yi inyi ido huɗu da abin sona.
***Kamar yadda masu iya magana ke faɗi wai rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya tabbas kuwa hakanne domin tun daren jiya su Hashim suka sauka amma ban samu zuwa ba kasancewar basu dawo da wuri ba, yau dai insha Allah nake son zuwa,
Ƙawalli na kira domin ta taya ni yi masa abubuwan da zan tarɓeshi dasu, ada dai inata nuƙu nuƙu da ɓoye ɓoye kamar ban son kowa yasan tarayya ta dashi but now nafi to fili dan bana shayin nuna shi gaban kowa a Matsayin wanda nake so kuma nake da burin aure,
Farfesun kaji muka yi masa wanda ya sha kayan ƙamshi sai ƙamshin daddawa yake, sai jallop ɗin macaroni, bayan mun kammala na shiga wanka na fito, caɓa ado nayi cikin wata doguwar riga pink mai adon stones nasa milk colour ɗin takalmi da jaka na ɗebi kayan na tafi domin itama Ƙawalli tuni ta jima da tafiya dan tun bayan da muka gama,
Napep na shiga muka nufi unguwarsu Hashim sai ƙamshin black oud nake zubawa sam dama ban sanar dashi cewa na taho ba, misalin ƙarfe 11 harda wasu ƴan mintuna na isa gidan ina riƙe da babban basket ɗin da na zuba masa abubuwan da na girka masa na shiga bakina ɗauke da sallama, da gudun tsiya Amira ta zo ta rungume ni wanda na san ba komai ke ɗawainiya da ita ba face tsantsar farin ciki wanda nima acikinsa nake. Kayan hannuna ta karɓa muka ƙarasa ciki inda Iya keta faman lale marhabun dani, gabana ne naji ya yanke ya faɗi lokacin da muka yi ido huɗu da Hashim daidai lokacin da yake ƙokarin fitowa daga cikin ɗaki nikuma zan zauna kan tabarma,
"Tabarakallah, masha Allah" na faɗa a hankali sakamakon wani irin mashahurin kyau da naga ya bayyana a gareshi, duk da dama nasan kyakkyawa ne amma wannan kyawun na yau ya zarce na kullum lallai idanu ba ƙaramin kyau da kwarjini suke sake ƙarawa mutum ba, sunkuyar da kaina ƙasa nayi ina gaida Iya yayin da shi kuma yazo kusa dani ya zauna wanda hakan ya sani jin kunya mutuƙa,
"Sarauniya...... Me yasa zaki wahalar min da kanki ki fito, ai ni ya dace in zo har gida in gaida ki sannan in yi godiya, Maimunatu nagode, nagode da alkhairin da kika yi min, haƙiƙa bani da kalmomin da zan gode miki"
Ɗan ɓata face nayi ina gyara veil ɗin dake kaina, "Zaka fara maganar godiyar ko? Wai kai godiyar nan bata ƙarewa ne? Kullum sai kayi min godiya hakan bai isa ba? Bari na tashi na tafi...."
Cikin sauri yace "A'a dan Allah karki tafi, kiyi haƙuri bazan sake ba" ya faɗa yana riƙe gefen rigata, su Iya nayi saurin kalla amma sai naga babu kowa a wurin da alama sun tashi sun bar mana wurin tun lokacin da ban san ko yaushe bane,
"To gaskiya idan baka so raina ya ɓaci ka daina yi min godiyar nan haka..... Da wannan godiyar gara kayi min addu'a zai fi faranta min rai"
"Ina yi miki a koda yaushe, amma wacce iri kike so in yi miki nikuma nayi miki alƙwari kullum bazan manta ba zanyi miki"
"Kawai kace Allah ya cikawa Maimunatu burinta...."
Tun kafin in ƙarasa ya katse ni, "Menene burin nata?"
Ɗan kallon sa nayi amma ban iya tsayawa na kalleshin ba nayi gaggawar kawar da kaina gefe,
"Kasancewa da farin cikin ta har ƙarshen rayuwarta"
Murmushi yayi ya kalleni,
"Nikuma kin san addu'ar da nake buƙata a gare ki?"
"A'a" na faɗa ina maida hankali na gaba ɗaya kansa,
"Allah ya makantar da idanuwa na kar inga kowacce mace sai Maimunatu ita kaɗai har tsawon rayuwa ta...."
"Hmmm bana fatan haka, a har kullum abin da bana ku ƙauna shine inga idanuwanka basa gani.... Wannan shine babban tashin hankali agareni"
"Nagode Widat.... Haƙiƙa...."
Kallon sa da nayi shine sanadiyyar da yasa shi yin shiru yana murmushi, bakinsa ya kama da hannunsa alamar ba zai ƙara ba, abincin da na kawo masa na tura masa gabansa nan ya langaɓar da kai yana kallona,
"Inyi magana kuma ace za ayi fushi dani...." ya faɗa cikin muryar tsokana,
"Hmm baka taɓa ganin fuskata ba sai yau, ada murya ta kake ji yau kuma gashi ka ganni, Jina yafi ganina ko?" na faɗa nima cikin tsokana,kafe ni yayi da ido nikuma nayi saurin saukar da idanuwa ƙasa,
"Ai ko hasidin iza hasada ya ganki ya san jinki bai fi ganin ki ba... Tsarin halittar da ubangiji Allah yayi miki ya kyautata ta, madalla da ubangijin tsara halitta..."
Wani sanyi naji yana shigata ta ko ina saboda daɗaɗan kalaman da Hashim ke faɗa min, farin ciki biyu ne ya taru ya haɗar min ayau, farin cikin kalaman dake fitowa daga gareshi da kuma farin cikin yau gashi zaune gabana yana kallon kowanne irin motsi nawa................
YOU ARE READING
GARIN DAƊI.....!
RomanceTabbas lamarin so yana da rikitarwa domin yakan jefa zuciya so da kaunar wanda bai dace ba, a wani sa'ilin so na mayar da mai yinsa kamar wani zautacce Hakan shine ya faru da widat....!