SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDA

449 63 13
                                    

26

~~~Abu kamar wasa shirye shiryen biki sun kankama gadan gadan a gidan mu kuma sai lokacin na fara jin fargabar auren da za ayi min, ada bani da magana ko buri sai na in ganni a gidan Samz amma yanzu da zarar na tuna sai inji gabana ya faɗi sannan ga wata irin kewa da nake ji ta ƴan gidanmu gaba ɗaya tun kafin in bar gidan sai dai duk da fargabar da nake ciki hakan bai hanani yin kumari ba saboda yanzu bani da wata sauran damuwa ko matsala, kullum muna tare da shi awaya duk da tun zuwanshi bikin Yaya Abdul Hakim bai ƙara dawowa ba sai dai ta waya wannan kam yakan ɓata lokutansa da dukiyarsa wurin hira dani, lokacinsa yake bani sosai kamar bai da sauran wani abu mai muhimmanci a rayuwar sa sama dani, duk wani abu da ya shige masa duhu dangane da addini ni yake fara tambaya ni kuma in bashi amsa gwargwadon sanina da fahimtata wanda kuma ilmi na bai kai ba sai in tambayi Abba, sosai ya dage wurin neman ilmin addini dan duk bayan sallar magriba yake zuwa wurin wani alaramma ɗaukar karatu, ni dai a lokuta da dama ina zama in yi shiru in yi ta tunani dan har yau ban san kowa nashi ba duk da ya sanar dani yana da ƙanne Hadiza, Maryam da Abdallah saboda mahaifinsu dama can sunan musulmai yake saka musu duk da mommy bata so,

A yanda na fahimta samz yana tare da damuwa duk da bai fito fili ya sanar dani ba ya barwa ransa domin damuwar tana da nasaba da mahaifiiyarsa dan gaba ɗaya ta fita sabgarsa ko gaisuwarsa bata amsawa tun daga ranar da yaje mata da maganar yana son zai musulunta, tun daga lokacin idan yayi mata waya bata ɗauka idan ya kira ƙannenshi sun bata wayar bata karɓa fushi take yi dashi sosai kuma wannan abun shine yafi komai damunsa ahalin yanzu, duk da tana fushi dashi hakan bai hana shi sake shiryawa ba ya nufi Kaduna ranar Juma'a, saida yayi mata tsaraba da kayan fruits domin tana mutuwar son kankana da gwanda da abarba da kuma apple, duk ya siya mata harda ƙarin ayaba da lemo, bayan sallar la'asar ya shiga gidan sanye da farin yadi riƙe da kayan da ya siya, tana zaune tsakar gida tare da ƙanwarshi Mary tana yi mata kitso, Mary ce kaɗai tayi masa magana ta hanyar gaida shi amma ita mommy yi tayi kamar bata san dashi ba a wurin,

"Mommy.... Zuwa nayi in baki haƙuri akan abin da nayi miki, pls forgive me mommy..... Dan Allah ki daina fushi dani, fushinki zai iya cutar da rsyuwata"

"Ai Samuel baka ga komai ba, ba dai kace ni zaka watsawa ƙasa a ido ba? Ni da na haife ka na reneka na kula da rayuwar ka ni kayiwa haka ko? To hanya ɗaya ce kuma ita kaɗai zata sa in daina fushi da kai, kayi gaggawar barin wannan addinin ka dawo kiristanci "

" Mommy kiyi haƙuri "

" ka tashi kaje na gama magana "

Tashi yayi bayan ya ajiye mata kayan duk da baida tabbacin zata ci, bedroom ɗinsa ya shiga ya ajiye jakar laptop ɗin shi sannan ya kwanta kan gadonshi, gaba ɗaya ya rasa abin da yake yi masa daɗi, shi dai ya san ba zai iya barin musulunci ba ahalin yanzu haka kuma baya son fushin da mommy keyi dashi, wayar shi ya ciro daga aljihun gaban rigarsa ya lalubo no beloved ya kira,

Ina falon mama ina kallon wani Indian series a tashar zee world naga kiran sa, kallon na kashe na miƙe na koma cikin ɗakina na zauna bakin gado ina yi masa sallama,

"Baby yakike......."

"lafiya lau Honey... Ya juma'a"

"Lafiya lau"

"Lafiya kuwa? Naji kamar akwai abin da yake damunka" na faɗa ina kishingiɗa a jikin gado na, shiru yayi na ɗan wani lokaci yana sake jinjina kulawa ta a gareshi domin ina saurin gane yanayinsa na farin ciki ko baƙin ciki koda kuwa iya muryarsa naji,

"Babu abin da ke damuna kawai na kwanta ne kaina na ciwo kaɗan"

"ayya sorry ko dai fargabar aurence?" na faɗa cikin tsokana, dariya naji yayi kamar yadda na tsammata,

"Fargaba kamar wata ke.... Ni da nake alla alla lokacin yazo in samu abokiyar hirar dare... Kamar in janyo lokacin fa haka nake ji"

"Wacece abokiyar hirar daren taka? Ai na faɗa maka ni bacci zan yi in barka"

"Haba baby..... Ba zaki tausaya min ba"

"Ka san me ƙawalli tace kwanaki?"

"a'a... Me tace?"

"wai in fara koya maka baccin tun daga yanzu, dan haka har baccin rana zaka rinƙa yi"

"zan so haka nima.... May be dama rashinki ne yasa nake kasa baccin amma idan kina nan na san zanyi"

"ai dolenka ma ka koyi bacci...."

"Haba baby...." ya sake faɗa yana murmushi,

"Ehh, da bacci da abinci zan rinƙa baka da yawa"

"kina son na ƙara ƙiba kenan"

"ohh yeah"

"OK babu problem amma ni bana son nayi ƙiba baby..... Haka ya isa"

"amma shine ni kake so in yi" na faɗa cikin shagwaɓa,

"kema kaɗan nake so kiyi amma idan kin yi da yawa babu matsala ina sonki a duk yanda kike"

"thank you Dear, I love you"

"I love you too"

A taƙaice dai mun jima muna hira sannan muka yi sallama. Har Samz ya gama weekend ɗinshi ya koma mommy bata saurare shi ba sai Daddynshi ke kwantar masa da hankali cewar wata rana zata sauko shi dai kawai ya cigaba da yi mata biyayya, ya san zai yi wuya ta sauko musamman ma idan ta ji maganar aurenshi da ni wanda har yanzu ba a faɗa mata ba, sai da aka gama haɗa komai sannan Daddy ke sanar da ita wai next month bikin Muhammad Mu'allim, suma ne kawai bata yi ba nan ta shiga zage zage da yiwa daddy Allah ya isa wai ya raba ta da yaronta kuma ita ɗanta bazai auri  musulmi ba,

Kwana tayi tana bala'i ta hana Daddy bacci sai masifa take,

"yaro na... My beloved son shine yau zai auri Muslim ehhhhhh...... Over my dead body...... Samz zai auri Muslim ya fasa auren Felicia.... Impossible... This will not be possible... Allah ya isa tsakanina da ku..... An yiwa yaro na asiri"

Duk maganganun da take yi daddy yana jin ta amma ya rabu da ita da yake shi mutum ne mai haƙurin gaske sai dai ka cuce shi ba dai ya cuce ka ba, har asuba bata yi bacci ba gari yana wayewa ta shirya ta fita duk a tunaninsa church ta tafi, gidan aminiyarta mahaifiyar Felicia ta tafi wato madam comfort, tana zuwa ta fashe da kuka tana zayyana mata abunda ke faruwa,

"Maman Mary inada solution.... Dole na san ba a banza Samz ya zama haka ba, dan haka shawara ta shine muje inda za a raba shi da tsafin da aka yi masa a juya tunaninsa da ƙwaƙwalwarsa ya manta da kowacce mace sai Felicia, nan da next month ɗin sai ayi wedding ceremony ɗinsu " na'am maman Mary tayi da shawarar madam comfort nan suka bazama suka rankaya suka tafi wurin bokansu wanda saida suka yi doguwar tafiya dan sai da suka manta da barin cikin gari tun suna wuce ƴan ƙauyuka da gidaje tsilla tsilla har ya zamana sai sai jeji, tun wayewar gari suke tafiya akan babur amma basu isa ga wannan boka ba sai la'asar sakaliya,

Madam comfort ce ta fara shiga cikin ƴar bukkar bayan ta jima tana yi wa boka bayani ta fito ta kira Maman Mary, tambayar ta boka yayi,

"Duk naji matsalolinki da damuwarki dama dalilin zuwanki nan.... Yanzu me kike so ayi masa?"

"Yawwa boka so nake a juya tunanin sa ya bar wannan sabon addinin da ya shiga ya dawo namu.... Sannan akwai wata yarinya da yake so zai aura amma ni ban san ta ba itama ina so a nisanta ta dashi a mantar dashi ita gaba ɗaya yaji ta fita a ransa ya daina tunawa da ita ya dawo ya auri ƴar aminiyata Felicia....... "

Wata ƙara boka yayi da kuwwa mai tsoratarwa ya shafa ƙoƙon dake gaban sa cike da ruwan tsafi sai ga hoton samz nan ya bayyana raɗau,

" Wannan ne? "

" Ehh shine " inji Madam comfort,

" To angama" boka ya basu tabbaci,

"Boka kar a cutar dashi kawai iya abin da na faɗa maka za ayi masa", "babu matsala zuwa cikin dare zamu gama aikin mu lokacin aiki yafi tafiya daidai" kuɗi ta ajiye masa suka tashi suka sake kama hanyar gida.

Nidai yau tunda na tashi nake faɗuwar gaba barin ma lokacin sallar azahar amma koda na gayawa Anty wadda ta zo gida bayan ta haihu sai take cemin wai dama in dai biki ya kusa haka kowacce mace ke ji kawai dai in tsananta addu'a, addu'ar naketa yi acikin zuciya ta kome nake ina yin wannan addu'ar har magriba inda Samz ya kirani video call ganin sa nayi kamar marar lafiya shima yana zaune gefen titi.........

GARIN DAƊI.....! Where stories live. Discover now