SHAFI NA ASHIRIN DA TAKWAS

393 60 9
                                    

28

~~~Ji nayi tamkar in shiga cikin wayar in gano me ke faruwa dashi a daidai wannan lokaci, cikin raina kuwa addu'a nake yi,

"ya Allah ka bawa bawan nan naka lafiya..... Ya Allah ka tsawaita rayuwar sa, ya Allah ka bashi nisan kwana kada ka ɗauki rayuwarsa yanzu ko dan halin da zan shiga.... Ya baki farin ciki a lokacin da na yanke ƙauna da sake samun sa cikin rayuwa ta..... Ya mallaka min komai dan ganin na dawwama cikin farin ciki..... Ya bani lokacinsa da duk wani abu da yake da iko dashi dan kawai in yi farin ciki, ya soni a lokacin da wani ya ƙini.... Yana burin zama dani tun a lokacin da wani ya guje ni.... Ya Allah ka tausaya min kada ka sake yanke min wannan farin ciki..... " na faɗa hawaye na sauka kan kumatu na,

" Baby.... " naji muryarsa ta daki dodon kunnuwa na duk da a hankali yayi maganar sannan kana ji ka san baida cikakkiyar lafiya,

" Dear... Sannu ya jikin naka? " na faɗa cikin hawayen farin ciki, ashe dai bai mutun ba yana nan a raye,

"Da sauƙi..... Amma ina fushi dake"

"kayi hakuri dear.... Menene laifi na?"

"Ba ki zo kin dubani ba"

"zan zo gobe goben nan insha Allah, dama kara nayi da alkunya amma tunda har yanzu kana kwance dole in zo..."

"A'a kiyi zamanki.... Na samu sauƙi"

"nidai duk da haka sai na zo.... Dama burina ka samu sauƙi kayi lafiya sosai"

"ba kya son ayi bikinmu ina kwance....."

"Akan me zan so ayi biki angona yana kwance"

"Kar na kasa baki kulawa ko?"

Share hawayen fuskata na shiga yi ina murmushi ohh wannan mutum ya iya jan magana, daga faɗin abin da ke raina shikenan shine har an juya min magana,

"Kuka kika yi ko?" ya sake tambaya ta,

"A'a...."

"Ga voice ɗinki nan ya sauya.... Waye ya saki kuka? Faɗa min"

"Babu kowa.... Kawai nayi missing ɗinka ne"

"I miss you more baby..... Zaki zo goben in turo miki kudin flight?"

"uhmm uhmm nidai karka turo" na faɗa cikin shagwaɓa,

"no zan turo miki"

Sallama muka yi nan na shiga haɗa kayana cikin traveling bag duk wani abu da zan buƙata na haɗa kayana saboda dama anty nata son in je a fara gyara ni tun kwanakin baya amma naƙi sai aiko min da kayan take amma babu wanda na taɓa amfani dashi dan ƙawalli ta gama tsoratar dani wai wallahi idan na yi wa waɗannan abubuwan shan hauka Samz kashe ni zai yi gara ma in yi sama sama,

A ranar na siyi ticket online nagama komai kuma daga wannan lokacin bamu ƙara magana da shi ba sai kuɗin flight da ya turo min kamar yadda ya alƙawarta daga nan ya kashe wayarsa, ko bacci rabi da rabi nayi asubar fari na yi wanka duk da bana wankan sassafe amma ranar na asuba nayi gashi dama ina fashin salla jikina na mulke da madarar turare sannan na shirya cikin doguwar riga kamar yadda na saba dan tashin wuri zamu yi.

Ƙarfe goma daidai na sauka garin Abuja, kamar koda yaushe Anty ce tazo ta ɗaukeni zuwa gidan ta, gidan babu kowa sai mai yi mata aiki da yarinyar dake tayata renon Fawas wacce ake kira da Labiba, tun bayan sauka ta a garin hankalina ya tafi ga Samz domin ban san a wanne hali yake ciki ba, so nake kawai in ganshi inga yanda ya koma, magana nayi wa Anty nace zan tafi duboshi nan ta fara yimin faɗa wai ni na cika gaggawa da rashin ta ido idan nayi haƙuri ma ai nan da ƴan kwanaki ne za a aura min shi in zauna tare dashi a inuwa ɗaya, shiru nayi ban ƙara maganar ba har sai da ta kirani da kanta tace in fito mu tafi bayan ta kammala shirya masa abinci, ina riƙe da Fawas muka tafi me renonshi kuma tana baya,

GARIN DAƊI.....! Where stories live. Discover now