SHAFI NA TALATIN DA BIYAR

47 1 0
                                    

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
   _(Home of experts & perfect Writers)_


   *GARIN DAƊI........!*💍💍

       *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

*Wattpad:ummishatu*

PAID BOOK #500

{35}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun  Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE  CARE

~REODEO

~VIGOR  MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*

~~~Tun bayan lokacin da yaci maganin da mommy ta bashi yaji garin Kano gaba ɗaya ya fitar masa arai irin fitar da ko sunan garin baya ƙaunar yaji an ambata bare har ya taka ƙafafuwanshi yaje,

Tsakanina dashi kuwa babu wata matsala sai ko ta rashin zuwansa dan tun last week yace min zai zo weekend bai zo ba gashi wannan weekend ɗinma shiru abin da yake damuna kenan a halin yanzu saboda sati biyu kenan bai zo ba duk rashin zuwan nasa sai ya fake da aiki,

Kasancewar weekend ne kuma bai zo ba tare muke da Bishra, ita tana can falo tana yi min gugar kayana yayinda nikuma nake cikin ɗakina, shigowar kiranshi cikin wayata shine ya katse ni daga shafa man da nake yi,

"Hello my sugar baby....."

Sai da na turo masa baki kamar irin yana ganina ɗinnan sannan na narkar da murya nace,

"Bayan munyi faɗa da kai...."

"Am soo sorry baby.... Ki shirya anjima kina da baƙo na aiko shi zai kawo miki wani gift na auren mu da na siya miki"

"Ni wallahi bana son ganin kowa kai nake son gani" na faɗa ina diddira ƙafafu a ƙasa idanuwana har sun taru da ƙwalla,

"ok to karki yi kuka please..... Kiyi haƙuri insha Allah next week zan zo"

"koda yaushe haka kake cewa, last week ma haka kace"

"am very sorry, ba zan sake ba"

Rarrashi na yayita yi har sai da na haƙura na ware na bar wannan maganar sannan muka yi sallama na cigaba da shiryawa, bayan na kammala na koma falo wurin Bishra wadda har ta kammala gugar da take yi ta ɗora mana abincin rana,

Zuwa ƙarfe uku na yamma baƙon da samz ya aiko ya ƙaraso kuma ba kowa bane illa abokinshi Ahmad, hijabi nasa na fita na yi masa iso har cikin falonmu sannan na gabatar masa da abinci da sauran kayan motsa baki muna cikin gaisawa oga ya iyo waya, tashi nayi na wuce ɗayan bedroom ɗina domin Bishra tana ɗayan waya da samz kuwa sai an keɓe dan yanzun nan zaka ji yana let me see your chest, aikin kenan kullum,

"Ahmad ya ƙaraso?" ya buƙata,

"ehh bai jima da zuwa ba"

"ok kin dai saka hijab ko?"

"No" na faɗa cikin tsokana,

"haba baby..... Dan Allah ki rufa min asiri ki rufe jikinki mana"

"Uhmm uhmmm"

GARIN DAƊI.....! Where stories live. Discover now