SHAFI NA HUDU

427 48 1
                                    

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
  _(Home of expert & perfect writers)_


   *GARIN DAƊI.......!*💍💍

  Free Book

  *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

*Wattpad:ummishatu*

*4*

~~~Nidai har naje gida ban daina tunanin wannan bawan Allahn ba domin dagaske al'amarinsa naji ya tsaya min acikin raina amma ban iya faɗawa kowa ba duk da cewa ƙawalli tazo munsha hira domin har bayan mgriba muna tare amma ban sanar da ita ba sai hirar bikina da take ta faman yi tana cewa gaba ɗaya ma ta rasa irin shigar da zata yi ranar, kasancewar tunanin wannan guy ɗin da naji ankira da suna hashim yana ƙoƙon raina shiyasa ban sake nayita yi mata kauɗi kamar koda yaushe ba daga ƙarshe har taso ta fahimta,

"ƙawalli wai ko dai wani abu yana damunki ne?" naji ta faɗa bayan ta zuba min ido, murmushi na ɗan yi cikin ƙarfin hali sannan nima na dubeta ina wasa da igiyar dake gaban doguwar rigar dake jikina mai gajeren hannu,

"me kika gani ƙawalli?"

"to ai na ganki ne gaba ɗaya kamar kinyi sanyi"

"wallahi lafiya lau nake kawai tsabar gajiya ce, yau tunda naje office ban samu kaina ba har lokacin tashi"

"to ya kamata ki kwanta da wuri ki huta, nima bari na tashi na wuce gida, idan yaya faisal yakira a miƙa min gaisuwa"

Harararta nayi na ɗauke kaina ina cewa,

"idan dagaske gaisheshin kike son yi ga no ɗinsa nan ki ɗauka sai ki kirashi"

"kya dai ji dashi"

"ko kuma ke kiji dashi ba"

Hijabinta ta saka tana dariya tare da ficewa daga ɗakin. Ni dai yau gaba ɗaya na kasa mantawa da tunanin wannan makahon saurayin dan hatta yaya faisal ma sai da ya fahimci yau bana jin hira shiyasa ba mu wani jima ba muka yi sallama nikam sai bacci ɓarawo, washe gari da wuri na tashi na shirya domin tafiya aiki, kamar koda yaushe doguwar riga na saka ta atamfa dark purple na yafa purple ɗin mayafi sai zuba ƙamshin turaren blue nake yi wanda ya haɗu da ƙamshin Arabian oud, ina ƙoƙarin fita daga gida bayan na yiwa su Annie sallama naji ƙarar wayata, ganin yaya faisal ne ya sani yin murmushi kafin na ɗaga wayar,

"ko har kin fita?"

"a'a sai dai niyya ka ganni nan zan fita yanzu"

"to shikenan Allah ya kiyaye hanya, idan kika je office za muyi waya"

"babu matsala" na faɗa ina zare wayar daga kunnena tare da mitar kiran da yaya faisal yayi min dan gashi nan sanadiyyar hakan ban samu damar gabatar da addu'ar fita daga cikin gida ba.

Lokaci zuwa lokaci nake duba agogon dake ɗaure a hannuna domin bana son yin latti so nake na fita kamar jiya ko Allah zai sa insake gamo da hashim wanda tausayinsa da son sanin halin da yake ciki ya gama addabar ruhi na da zuciyata gaba ɗaya, misalin ƙarfe 5 dai dai na yamma na fito daga office na ɗauki drop ɗin napep muka nufi hanyar da nabi jiya, sai tsittsilla ido nake yi ai kuwa cikin ikon Allah na hangosu tsaye da wannan dattijon na jiya wanda yace shine yake tare masa abun hawa kullum, agabansu muka yi parking ina kallonsu cikin fara'a na fito ina gaida wannan dattijon,

"yarinya sai dai kuma ban ganeki ba daga ina?"

"Baba Jinjiri itace fa budurwar jiya baka gane ta ba? Wadda muka tafi tare...." jin abin da ya fito daga bakin saurayin ya sakani sakin baki ina kallon ikon Allah,

GARIN DAƊI.....! Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora