~~~Lokacin da ƙawalli ta fito nayi zurfi cikin tunani har sai da ta taɓa ni sannan na dawo cikin hayyacina na kalle ta da idanuwa na waɗanda suka yi jajur kamar gauta,
"ƙawalli lafiya kuwa? Me ke damunki?" ta tambayeni tana ƙokarin zama kusa da ni tare da dafa kafaɗa ta,
"ƙawalli ban san ta yaya zan kwatanta miki irin halin da zuciya ta take ciki ba..... Ina cikin matsananciyar damuwar da ni kaina ban san adadinta ba....... Gaba ɗaya jina nake a wata duniya ta daban ba wannan tamu wadda na sani kuma na saba da ita ba...... " Gaba ɗaya abin da ya faru tsakanina da Hashim na kwashe na sanar da ita tun daga farkon haɗuwar mu har kawo yau da abin da ya faru babu abin da na ɓoye mata,
Tunda ta gama sauraren labarin da na bata wanda yafi kama da tatsuniya tayi shiru tana kallo na kamar ruwa ya ci ta, ni kuma sai lokacin na samu damar zubar da hawaye na waɗanda suka jima suna suna ƙona zuciya ta,
"Haƙiƙa widat kin yi kuskure babba ba ƙarami ba..... A wannan zamanin da muke ciki yanzu ai ba kowane zaka yi masa alkhairi bai butulce maka ba daga ƙarshe shiyasa alkhairinma ake tsoron yinsa, kuskure na farko da kika yi shine ƙin sanar da kowa ko kuma rashin neman shawarar kowa cikin wannan al'amari, da ace kin nemi shawara da duk hakan bata faru ba saboda me shawara aikinsa baya ɓaci..... Amma babu komai tunda dai aikin gama ya gama, yanzu kawai karki sa damuwa acikin ranki ki manta komai kuma ki ɗauka kamar ba ayiba, shi ma Hashim ki sa aranki kamar baki taɓa haɗuwa dashi ba a cikin tarihin rayuwar ki "
Hawayen dake zuba a idanuwa na ta share tana ci gaba da rarrashina, ni kam sai da na ci kukana na more sannan nayi shiru amma nasa araina sannan na yiwa kaina alƙawarin mantawa da Hashim da dukkan rayuwarsa gaba ɗaya koda kuwa shi ne autan maza duk na san ba abu ne mai sauƙi ba manta butulci musamman ga mutumin da ada ba komai ba ta sanadiyyarka ya zama komai sannan daga baya yazo ya ɗauke ka babban maƙiyinka.
Tare da ƙawalli muka tafi gidanmu tana sake kwantar min da hankali, mun jima muna hira kafin ta tafi, ni kam ko abincin dare yau ban ci ba haka bacci shima na kasa sai juyi kawai nake yi raina cike da damuwa, tunda na zo duniya ba a taɓa cimin mutunci irin wannan ba, babu wanda ya taɓa wulaƙantani kamar yanda Hashim ya wulaƙantani yau, kwata kwata kasa runtsawa nayi sai bayan asuba sannan bacci ɓarawo ya samu nasarar yin awon gaba dani.
Tsawon kwana da kwanaki na ɗauka cikin hali na damuwa da rashin walwala dan hatta abinci wannan daƙyar nake daurewa ina ci amma ba wai dan ina jin daɗinsa ba, kuka kuwa kusan kowanne dare sai na yishi dan har ya zame min sabo saboda da rana zan ɗan yi al'amura na zan fita aiki zan haɗu da abokan aiki na zamu tattauna za ayi hira ayita dariya ina jin su kuma ina zaune ina kallon kowa amma da zarar na dawo gida sai inji ƙuncin duniya da damuwa sun taru sun lulluɓeni wani lokacin ma inji duniyar gaba ɗaya ta isheni gashi in nemi bacci a idona inji na rasa, gaba ɗaya dai rayuwar ina yin ta ne cikin ƙunci da damuwa sam bani da wata walwala gaba ɗaya na rasa farin ciki abinci wannan wani sa'ilin kasa ci nake yi shiyasa duk na rame na lalace sai uban ƙashin wuya da nake ta fama dashi,
Kowa ya ganni yasan ina cikin damuwa kuma akwai abin da ke damuna amma duk wanda ya tambayeni cikin yayuna ko su Annie sai ince babu komai, daga ƙarshe da Annie taga abun ya isheta anty khadija ta kira babbar yayarmu tace ita ta kasa gane kaina kullum ina cikin damuwa kuma ganina cikin wannan hali itama nata hankalin tashi yake dan Allah ta kirani in je wajen ta in yi kwana biyu ko zan ɗan warware dan tayi min juyin duniyar nan tana tambaya ta amma naƙi na sanar da ita damuwa ta,
Sam ban san sunyi haka ba, bayan na dawo daga aiki ina ɗaki kamar yanda na saba zama ni ɗaya cikin ƙunci tare da tunani marar amfani ba wai tunanin Hashim ba a'a asalima tun daga ranar da yayi min wannan wulakancin ban ƙara tuna shi ba cikin raina kawai dai ta dalilin abin da yayi min ne na rasa farin ciki da walwala kuma na shiga ƙunci da damuwa, shiyasa kullum cikin tunanin makomar rayuwa ta nake, ƙarar waya ta ne ya cika ɗakin amma har tayi ta tsinke ban ji ba saboda hankali na baya wurin, sai akaro na biyu sannan naji shi ɗinma yana dab da tsinkewa, ganin anty ce ya sani hanzarin ɗauka,
"hello anty...."
"uhmm..... Widat bacci kike yi ne?"
"a'a anty, idona biyu"
"to ya aiki, an dawo an gaji ko"
"wallahi anty kamar kin sani"
"ato ba nace ki zama lawyer Irina ba mu baki aiki a chamber ɗinmu ba kin ƙi...."
"kai ai anty wannan aikin naku sai ku, haba taya zan iya zuwa tsakiyar mutane in tashi ina bayani kowa na kallo na"
Dariya anty tayi kafin naji tace,
"ni kuwa kinga ko yau sai da na shiga court can ma naga yayanki, shi ya je kare wanda ake ƙara nikuma ina kare masu ƙara...."
Cike da mamaki na gyara zama na dan jin wannan abun al'ajabi,
"Anty.... Kuma ya aka yi? Dama ana yin haka? Wanne daga ciki ma tukunna? Yaya Abdul Hakim ko yaya Abdul Majid?"
"Abdurrahman dai....."
"kuma anty yaya kuka yi? Baku nuna kun san juna ba?"
Dariya ta sake yi sannan naji tace,
"ina ruwana dashi, kowa aikinsa yayi, yayi nasa nayi nawa ko gaisawa ma ba muyi ba, to ke in banda abin ki sau nawa ina zuwa kotun Abba amma ai ba sani ba sabo, ita shari'a haka take, kuma da kike cewa ba zaki iya tsayawa gaban mutane ba naga kema inda kike aikin gaban students kike tsayawa "
" Anty ai wannan ba irin naku bane..... "
" menene bambanci munatu? Yanzu dai nan da friday ina so ki shirya ki taho nan Abuja wurina, akwai wani aiki da zan saki ankusa fara training...... "
" Anty zan iya kuwa.... " tun kafin in ƙarasa ta katse ni,
"Na san zaki iya ɗin ne ai yasa nace kizo, ki rubuta leave a wurin aikin naku"
"to shikenan Anty, yaushe zan taho?"
"ki taho Friday, bari zan turo miki kuɗin abin hawa"
"Anty na jirgi fa zaki turo"
"bakida matsala tawan"
Sallama muka yi na kashe wayar ina murmushi jin muryar anty har yasa na ɗan ji sanyi araina, ita dama tana da kula kuma ta iya tafi da damu dan mun fi shiri da ita fiye da anty salaha, ita anty salaha bata da yawan magana sannan ba kasafai ake zama da ita ayi hira ta ji matsalar ka ko damuwarka ba saɓanin Anty wanda ita da kanta zata kiraka tana tambayar ka babu wata damuwa ai ko? Ko dan kasancewarta lawyer ne ban sani ba amma gaskiya ta iya kulawa da rayuwar mutum.
*
Saɓe yake da jakarshi ya tare napep ya shiga kai tsaye hotel ɗin da take ya nufa, a bakin ɗakin da take ya tsaya yayi knocking tsawon mintuna 5 ta zo ta buɗe,"Hashim Kaine? Come in" ta faɗa tana bashi hanya tare da yi masa alama da hannun ta cewa ya shiga ciki,wuri ya samu ya zauna yana gaida ta cike da ladabi,
"any problem?" ta faɗa tana kallon yanayinsa wanda damuwa ta bayyana ƙarara,
"Ranki ya daɗe bani da wurin zama yanzu, an kore ni daga inda nake zaune...."
Shiru tayi na ƴan wasu mintuna kafin ta kalle shi, shi ma itan yake kallo yana kallon shigar da tayi cikin doguwar jar riga mai adon duwatsu kanta ta dan yafa ƙaramin mayafi,
"tashi muje...."
Babu musu ya miƙe suka fita daga ɗakin bayan ta rufe, hotel ɗin suka bari cikin rantsattsiyar motar ta baƙa wadda ke ɗauke da gilasai masu duhun gaske,
Wata sabuwar unguwa suka shiga mai ɗauke da manya manyan gine gine masu aji da matsayi, wani katafaren gida yaga sun dosa wanda ya sha ginin zamani da dashe dashe na manyan shokoki haɗeda flowers waɗanda suka taru suka yiwa gidan ƙawanya, horn tayi wani ɗan dattijon mutum ya leƙo ganin motar ta ya sashi hanzarin buɗe gate ɗin nan ta danna motar ta ciki, shi dai Hashim bin ko ina yake da kallo ba tare da yayi magana ba har zuwa lokacin da ta umarce shi da ya fito bayan tayi parking, cikin ɗaya daga cikin parts ɗin gidan suka shiga nan ya ganshi tamkar aljannar duniya domin komai yaji, falo ne ƙaton gaske ya sha kayan alatu sai bedrooms guda biyu kowanne da royal bed aciki,
"zaka iya zama anan... Daga nan har zuwa lokacin da ka so tashi"
Lumshe idanuwansa yayi gaba ɗaya ma ya rasa irin godiyar da zai yiwa hajja sharifa domin ta sauya rayuwar sa daga haɗuwarsu ta mayar dashi babban yaro abin kwatance agari...........
KAMU SEDANG MEMBACA
GARIN DAƊI.....!
RomansaTabbas lamarin so yana da rikitarwa domin yakan jefa zuciya so da kaunar wanda bai dace ba, a wani sa'ilin so na mayar da mai yinsa kamar wani zautacce Hakan shine ya faru da widat....!