SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS

360 59 9
                                    

18

~~Drop na ɗauka har masaukin da samz ya sauka kuma ban wani sha wahalar gane wurin ba saboda sanannen wuri ne, har ɗakin da yake na shiga bayan nayi knocking naji shiru, yana kwance cikin blanket, a hankali na ƙarasa shiga na zauna gefen gadon, zaune ya tashi fuskarsa ɗauke da murmushi duk da fuskar ta ɗan faɗa kaɗan haka bakinsa lips ɗinsa duk sun bushe sunyi fari alamun bai ci abinci ba,

"Sannu..... Ya jiki?" na tambayeshi ina kallon cikin ɗakin,

"Da sauƙi...... Me yasa kika wahalar da kanki kika zo?"

"Na zo inga yanda kake ne kuma in duba ka"

"Na gode, ya training?"

"Babu daɗi" na faɗa cikin shagwaɓa ina ɗan turo baki,

"Me yasa?" ya tambaye ni yana kallon cikin idanuwa na amma ban bari mun haɗa ido ba,

"Saboda baka nan...."

"Ayya sorry.... Gobe zan zo in dai naji sauƙi"

"Allah ya baka lafiya...... Amma me ke damunka?"

"Amin.... Nagode"

"Me ke damunka?" na sake tambayarshi ina kallon gefen da yake zaune sanye cikin fararen jersey,

"Karki damu naji sauƙi...." jin abin da ya faɗa ya sani ɗan ɓata fuska kaɗan ina gyara handbag ɗina,

"Shikenan tunda ba zaka faɗa min ba"

"Am sorry..... Kaina ne ke ciwo" ya faɗa yana murmushi, na san ba hakan bane kawai dai ya faɗa ne dan a wuce wurin,

"shikenan Allah ya baka lafiya..... Bari na wuce"

Langaɓar da kai naga yayi yana kallona,

"amma dai ba fushi kika yi ba ko?"

"uhmm ni ba fushi nayi ba" na faɗa ina miƙewa tsaye,

"OK bari na zo na rakaki masaukinku" cikin sauri na juya ina kallonsa yana ƙoƙarin saukowa daga kan gadon,

"a'a ni bana buƙata dan Allah ba sai ka fita ba kayi zaman ka"

"kina ganin babu matsala zaki iya zuwa ke daya?"

"insha Allah zan je lafiya kawai kayi zaman ka Allah ya kara sauƙi amma idan baka warke ba Allah nima zan kwanta" daga haka na fita daga cikin ɗakin ina murmushi ni kaɗai, murmushin shima yayi bayan fita ta yana mai shaƙar ƙamshin turare na da na bar masa shi kansa bai san wanne irin al'amari ne wannan ba amma yana jina acikin ransa fiye da komai da ya mallaka ahalin yanzu sannan bai taɓa ganin yarinyar da ta burgeshi yaji jininsa ya haɗu da nata tun akaron farko ba kamata, sai dai jikinsa da tunaninsa na bashi cewa akwai tarin ƙalubale a tarayyarmu wanda nima sau da dama ina tuna hakan.

Kamar ɗazu yanzu ma drop na ɗauka ina kallon yanda cikin garin yake wanda ya amsa sunansa birni, wayata na ciro cikin handbag dan ganin wanda ke kirana, Anty na gani nan na ɗaga bakina ɗauke da sallama,

"Salma tace min kin fita, ina kika je?"

"Anty bafa nisa nayi ba, kinma ganni a hanya na kusa komawa hotel ɗin da muka sauka"

"Har yanzu fa baki amsa min tambaya ta ba nace ina kika je?"

"Dubiya naje...."

"waye bashida lafiya?"

"Tare muke training"

"to daga yau karki sake fita dab da magriba, kin ji abin da nace?"

"To anty, agaida su Sultan"

GARIN DAƊI.....! Where stories live. Discover now