SHAFI NA ASHIRIN

447 63 11
                                    

20

~~~Ni kaina inada yaƙinin cewa zanyi missing Samz duba da irin yadda zuciyata ta shaƙu dashi ƙwarai dagaske, duk da baida yawan hayaniya amma ni idan yana tare dani mai surutu yake zama tare da barkwanci dan haka zai yi ta tsokana ta yana zolaya ta, da tunaninsa a ƙoƙon raina muka sauka garin Abuja, Anty da kanta itace ta ɗauko ni zuwa gidanta,

"Widat da alama Lagos ɗin nan ta karɓeki....." Anty ta faɗa cikin wasa akan hanyar mu ta zuwa gidanta fuskarta ƙunshe da fara'a, juyawa nayi na kalle ta,

"Anty me kika gani?" na buƙata ina kallonta,

"Na ganine ai kin narka uwar ƙiba..." ta bani amsa idanuwanta na kan titi,

"wai dagaske Anty?"

"Allah dagaske kin yi ƙiba Widat, babu wanda ya faɗa miki? Salma bata faɗa miki ba?"

"Ƙawalli ta faɗa min kuma....." shiru nayi ban ƙarasa ba dan naso in yi suɓutar baki ince Samz ma yace nayi ƙiba akan tsoffin pics ɗin da na tura masa wanda na ɗauka lokacin da na zo Abuja before mu tafi Lagos,

" To kinga ashe ba ma ni kaɗai na gani ba...... "

Murmushi kawai nayi a raina ina sake tuna shi, na san ta dalilinshi ne na samu tarin farin ciki da kwanciyar hankalin da har nake iya cin abinci in ƙoshi wanda har ya sani ƙiba, haka kuma ta dslilinsa ne farin cikin da na rasa ya dawo, ban taɓa sanin na kamu da sonshi har haka ba sai yanzu da na ɗan yi nesa dashi dan bana cikakken mintuna uku sai na tuna shi a cikin raina. Lokacin da muka ƙarasa gidan Anty salla nayi na zauna muna ta hira da ita inata bata labarin Lagos da abubuwan da suka faffaru wurin training,

"Baki bani labarinsa ba shi kuma"

"Waye kuma Anty?"

Dariya tayi kafin tace "Shi ƙanin nawa mana"

"Anty waye ya faɗa miki?"

"Sai an faɗa min? Ai da ganin yanda hankalinki ya kwanta na gane kin samu wani wanda ya iya kula da ke kuma....."

Tashi nayi na gudu bedroom ina ce mata zan bata labarinsa amma ba yanzu ba, sai da nayi wanka na gama shirin bacci sannan na kunna wayata, ina buɗeta massages ɗin Samz suka fara tururuwar shigowa, tun kafin na gama karantawa kuma kiran shi ya shigo,

" Hello Darling...." na faɗa murya ta can ƙasa,

"Yes Sweetie..... Sai yanzu ake samun ki?"

"Yi haƙuri wallahi kana raina..."

"Ya kike? Kin je gida lafiya?"

"Lafiya Lau...."

"I miss you baby...... Kinci abinci?"

"I miss you more..... Na ci ɗan kaɗan"

"why? Bana son kina cin abinci kaɗan baby"

"Kafi son in ci da yawa in yi ƙiba sosai.... Kana ji Anty ta fara cewa nayi ƙiba sosai"

"Nima ai na faɗa miki..... Amma idan kin ƙara kaɗan ki barta haka..... Idan kika yi nauyi da yawa ba zan rinka ɗaukar ki ba...." tun kafin ya ƙarasa na shagwaɓe fuska cikin shagwaɓa kamar zanyi kuka nace,

"Ba zaka rinƙa ɗauka na ba?" na faɗa kamar zanyi kuka,

"Ehh mana, idan kina so in rinƙa ɗaukar ki kar kiyi nauyi da yawa"

"uhmm uhmmm.... Ni dai a'a" ni kaina bana sanin na iya shagwaɓa sai idan ina tare da Samz ban san dalili ba sai in yi ta masa shagwaɓa shi kuma yana biye min yana rarrashi na kamar wata baby koda yake da babyn ma yake kirana,

GARIN DAƊI.....! Where stories live. Discover now