SHAFI NA BAKWAI

335 48 2
                                    



~~~Hawaye ne kawai ke faman sintirin kaiwa da komowa akan kumatu na yayin da bakina ya kasa furta koda kalma guda,

"Abba hakan da kayi shine daidai, haka kawai yarinya tana neman ta mayar da mutane ƙananan mutane....."  yaya Abdul hakim ya faɗa bayan ya miƙe yana ƙoƙarin fita daga cikin falon, ni ɗinma mama kamani tayi muka fita har lokacin ban bar zubar da hawaye ba,

Kai tsaye sashen mama muka shiga wadda dama tun can ni a sashenta ɗakina yake, zaunar dani tayi kan kujera sannan itama ta zauna kusa dani ta soma rarrashi na,

"haba widat.... Ya ina yi miki kallon mai hankali kuma kina ƙoƙarin ɓata rawar ki da tsalle? Ringiɗi ringiɗi aka yi maganar nan sai yanzu zaki dawo ki cewa yaron nan kin fasa auren sa bayan duka burikansa sun ta'alaƙƙa ne akan ki..... Ai Kinga kamar ba a kyauta ba idan aka yi masa haka ko? "

Cikin shassheƙar kuka na ɗago kaina na kalli mama,

" mama wallahi bana sonshi, ban taɓa son yaya Faisal ba koda na aure shi kawai zan zauna dashi ne amma ba dan wai ina son shi ba "

Jijjiga kai mama tayi tace" na fahimceki amma kin san abin da nake so dake? "

" a'a.... " na faɗa cikin kuka,

" ki kwantar da hankalinki ki cigaba da addu'a, kin san sau dayawa muna son abu amma kuma ba alkhairi bane atare damu, wanda kuma muke ƙi sai kiga daga ƙarshe ya zame mana alkhairin, dan haka abin da nake so dake shine ki daina wannan kukan ki share hawayenki kiyi addu'a akan Allah ya tabbatar miki da koma menene in dai shine alkhairi agareki duniyar ki da lahirarki.... "

" to mama"

Sai da ta ɗan sake yi min nasiha sannan na tashi na wuce ɗakina naje na cigaba da kuka na, ina yi ina tuna hashim yanzu kowacece zata iya sonshi har ta aure shi ta bashi irin kulawar da nake mafarkin bashi a koda yaushe? Da zarar na tuno wannan lamari sai inji na kasa jurewa.

Yinin ranar haka na yishi cikin damuwa da koke koke domin wuni nayi cur ina cikin ɗaki in banda kuka babu abin da nake yi a haka har ƙawalli ta zo ta iskeni, ganinta sanye da hijabin makaranta hakan ya tabbatar min da daga islamiyya ta dawo ko gida bata je ba ta shigo wurina,

Ganin yanayin da nake ciki yasa ta faɗin "subhanallahi, ƙawalli lafiya kuwa? Ko dai baki da lafiya ne?" ta ƙarasa maganar tana zama kusa dani, murya ta a dashe na tashi zaune kuma har lokacin kayan bacci ne ajikina dan yau ko wanka ban yiba,

"ƙawalli gara rashin lafiya da wannan halin da nake ciki.... Su Abba sun yanke shawarar aura min yaya faisal duk da na faɗa musu gaskiya cewar bana sonshi...... Saboda jiya da daddare na faɗa masa abin da ke raina cewa inada wanda nake so shine ya zagaye yaje ya fadawa yaya hakim, shi kuma ya faɗawa su abba..... "

" gaskiya ƙawalli lamarinki yanzu yana bani mutuƙar mamaki..... To menene abin damuwa dan su abba sun yanke hukunci akan ki.... Ki sani fa duk zaɓin da zasu yi miki ba zai taɓa zama sharri agareki ba sai dai ya zama alkhairi.... Dan Allah ki daina irin abubuwan nan na marassa ilmi, ni wallahi har kin sa naji raina zai ɓaci..... "

Jajayen idanuwana na buɗe na kalleta, lallai duk yadda aka yi ƙawalli bata san zafi da raɗaɗin rabuwa da masoyi ba shiyasa take furta irin waɗannan kalaman, ni dai har ta ƙaraci faɗanta ta tafi bana fuskantar abin da take cewa, bayan tafiyarta ina zaune kan sallaya bayan na idar da sallar magariba mama ta shigo cikin ɗakin,

"ƴar mama taso mana.... Zo muje maza"

Tashi nayi nabi bayanta har zuwa falonta, abinci ta nuna min babu musu na zuba na fara ci ba wai dan yana yi min daɗi a bakina ba, bayan na gama mama ta sake yi min nasiha sannan tace in je inbaiwa Annie haƙuri dan da alama fushi take dani kuma fushin iyaye akan ƴaƴansu babu kyau, kamar yadda tace haka na tashi naje na samu Annie tana zaune kan carpet ɗin salla da carbi a hannunta tana ja, durƙusawa nayi agabanta na fara bata hakuri amma har nayi na gama bata kulani ba, tashi nayi na fita na koma ɗakina na cigaba da zaman ƙunci.

GARIN DAƊI.....! Where stories live. Discover now