©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_*GARIN DAƊI......!*💍💍
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
*Wattpad:ummishatu*
End of book 1(end of free pages)PAID BOOK #500
{38}
*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma'abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*
~MAI DA TSOHUWA YARINYA
~FEMALE CARE
~REODEO
~VIGOR MAX
~ LONGZIT
~B CLEAR
*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA.....*
~~~Cike da kasala na soma ware kitson kaina amma ko biyar ban tsefe ba naji na gaji ba zan iya cigaba da tsifar ba babu shiri na haƙura sakamakon wani bacci da naji yana fisgata, tashi nayi na rufe ko ina na dawo na kwanta nan kan kujera ko minti goma banyi da kwanciya ba bacci yayi gaba dani, bacci nayi mai shegen daɗi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa wanda bani na farka ba sai misalin ƙarfe ɗaya da rabi na rana,
Wanka na shiga nayi a raina ina cewa har yanzu wannan bawan Allahn bai dawo ba daga zuwa siyan waina, shiryawa nayi cikin riga da skirt ƴan kanti masu santsi na shan iska, ni kaina mamakin kaina da kaina nake saboda irin yanda na ɗan yi kumari, ƙirjina ya cika dam ya ninka da, bra ɗin da samz ke yimin ɗan biki a kai yake cewa wai tayi min yawa to yanzu tama yi min kaɗan shiyasa ko sawa bana yi, salla nayi bayan na feshe jikina da turaruka masu sanyin ƙamshi, ƙarar wayata ne ya sani miƙewa na nufi falo inda take, ganin samz ne ya sani yin murmushi kafin na ɗaga na zauna kan kujera,
"Baby.... Are you still sleeping?"
"No, na tashi, salla nayi..."
"ok, buɗe min na dawo"
Ajiye wayar nayi na fita na buɗe masa, shigowa ciki yayi yana kallo na fuskar sa cike da so da kulawa,
"Sannu da zuwa..." nace dashi ina ɗan hugging ɗinsa,
"Thank you baby...."
Ciki muka shiga ya miƙo min ledar da yazo da ita karɓa nayi na buɗe, ai ina buɗewa naji yawuna ya tsinke tashi nayi na ɗauko jug da filet na juye wainar da kunun dan duk a cikin leda aka zubo, ƙuliƙulin na kunce na juye a kai na fara ci kamar na shekara hanci komai ba, tsayawa kawai yayi yana kallona amma ban san yana yiba har sai da naji cikina ya ɗauka sannan na ajiye guntuwar wainar na ɗauki kunun nasha, ba ƙaramin daɗi wainar tayi min ba ko kuma dan ina kwaɗayinta ne naji daɗinta oho,
"Kaifa? Ka ci abinci?"
"Naci...... Baby your chest is now full......" ya faɗa yana kai hannunsa wurin,lumshe idanuwana nayi na shige cikin jikinsa ina jin wani irin shauƙin son kasancewa da shi, ada mijina bai wani dameni ba asalima har faɗuwar gaba nake ji duk lokacin da na fuskanci zai raya sunnah dani amma yanzu ni da kaina na bashi gudummawar faruwar hakan ban san dalili ba yanzu sam bana ƙosawa dashi. Soyayya muka shayar da junanmu sannan muka tsarkake jikinmu muka yi sallar la'asar wacce har mun so ma mu makara, muna manne da juna har dare, ni ina narke jikinsa kamar wata kyanwa bayan munyi sallar ishah muka fita tare na rakashi restaurant yaci abinci ina waje ina jiransa domin ni bana son jin koda ƙamshin abincinne, ina tsaye a waje ina jiran fitowarsa wasu samari guda biyu suka zo wucewa har sun wuce sai suka dawo da baya, bakina cike fal da yawu saboda tashin zuciyar da nake ji haka kawai,
YOU ARE READING
GARIN DAƊI.....!
RomanceTabbas lamarin so yana da rikitarwa domin yakan jefa zuciya so da kaunar wanda bai dace ba, a wani sa'ilin so na mayar da mai yinsa kamar wani zautacce Hakan shine ya faru da widat....!