SHAFI NA GOMA SHA UKU

312 45 1
                                    



  *13*

~~~Duk irin yadda na so in ɓoye damuwata kasawa nayi dan gaba ɗaya nayi wani irin muzu muzu dani duk na fiffige kana ganina ka san akwai abin da yake damuna, ada na tsammani zan iya yin pretending in danne ba tare da wani ya gane ba amma kash labarin zuciya a tambayi fuska,

Zaune nake tsakiyar gadon da aka kwantar dani hannu na riƙe da wayata ba komai nake kallo ba illa pictures ɗinmu nida Hashim waɗanda muka yi a lokacin da bai samu lafiya ba a lokacin yana makahonsa sai dai duk da baya gani a lokacin rayuwa tafi yimin daɗi dashi saboda ko babu komai yana da lokacina sosai kuma muna baiwa junanmu kulawa cikin so da ƙauna tare da ririta juna saɓanin yanzu da abubuwa suka rincaɓe suka tsananta komai babu daɗi,

Shigowar ƴan gidanmu ce ta sani ajiye wayar ina kallon su ɗaya bayan ɗaya mama ce kan gaba sai anty Khadija, Bishra da yaya Abdul Hakim shine ƙarshen shigowa,

"ya na ganki ke kadai ina ƙawar taki?" anty Khadija ta buƙata tana ƙoƙarin zama kusa dani,

"Tana zuwa anty abu ta fita siyowa"

Anty bata ƙara magana ba muka fara gaisawa dasu mama suna yi min ya jiki gefe ɗaya ga abincin da suka zo da shi da su fruits da dai sauran su ahaka har ƙawalli ta dawo daga siyan pad ɗin da ta tafi shagunan waje domin taje na cikin asibitin wai ya ƙare.

Har na ƙaraci zamana a asibiti nagama tsawon sati biyu Hashim bai yimin ko sannu ba bare har in sa ran zai zo ya duba ni haƙiƙa wannan abu yayi min ciwo mutuƙa, ranar da aka sallame ni muka tattara muka koma gida nida ƴan uwa na domin na warke sumul sai dai ɗan abin da ba a rasa ba dan har yanzu wani ciwon bai gama warkewa ba caan gida na cigaba da kula dashi.

Sai da na warke tass sannan na koma aiki washe garin ranar da na koma na shiga kasuwa nayiwa su Iya siyayyar kayan abinci kamar yadda na saba, duk da Hashim ya nuna bai damu da rayuwata ba yanzu to ni ba saboda shi zanyi ba dan Allah zanyi,

Napep na samu ya zuba min kayan muka tafi, muna shiga unguwar shima Hashim yana shigowa nan mai Napep ya sauke min kayan ina ƙoƙarin sallamarsa Hashim ya ƙaraso, ƙananan kaya ne a jikinsa fuskarsa ɗauke da baƙin tabarau,wani irin kallo na wulaƙanci da ƙasƙanci yake bin kayan dasu kafin naga ya tare ƙofar gidan alamun baza a wuce a shiga ciki ba,

"lafiya? Wannan kayan fa?"

Zuciya ta na danna sannan na danne fushi na nace,

"Hashim baka gane ni bane??"

"To idan ma ban gane ki ba menene? Ki kwashi tarkacenki kiyi gaba ba a buƙata anan"

Da mamaki nake kallonsa kafin nima in murtuke fuska kamar yadda yayi,

"Idan kana tsammanin saboda kai na kawo kayan nan to kayi kuskure, ni har na manta da wata aba wai rayuwar ka ma dan ni mutanen kirki ne a gaba na bana banza ba, kuma taimakawa mai buƙatar taimako ba kanka na fara ba,bare ingama a kanka...."

"To ki kwashe kayan ki ki ƙara gaba dan ba zaki shiga gidan nan ba, kin zama tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba alkhairi ba, tunda nake da tsohuwa ta bata taɓa yin fushi dani ba sai ta dalilin ki yanzu ko gaishe ta nayi bata amsawa duk saboda ke.... Wallahi Maimunatu na tsane ki kuma nayi dana sanin sanin ki, tir da kasancewarki a cikin rayuwa..... "

" Tabbas Bahaushe yayi gaskiya da yace Tsintacciyar mage bata mage...... Dole kace kayi dana sani tunda ada acikin duhu kake rayuwa yanzu kuma Allah ya kawo maka WANI HASKE wanda ya yaye maka wannan duhun har kake iya ganin gabanka sannan kake iya bambance tsakanin ƙasa da gari, to ka sani dan kayi dana sanin sanina a rayuwa ba laifi bane dan dama wannan ɗabi'a ce ta dabbobi mayar da masoyi ya koma maƙiyi sannan dan ka tsaneni ai ba kai ka halicce ni ba bare hakan ya dameni..... Daga ƙarshe karka yi tir da kasancewata acikin rayuwar ka domin already na fita, kaje kayi rayuwa da duk wanda kake so kuma ka zaɓa..... Sannan gida da kake maganar bazan shiga ba sam banga laifin ka ba amma kaje ka bincika gidan Alƙali Mukhtar Garzali na tabbata zaka samu gidan ubana ya ɗara wannan sau dubu dan ko B/Q ɗin gidanmu tafi wannan akurkin daraja sau dubu.......Mtswwww " tun kafin in ƙarasa naji saukar mari tauuu, cikin zafin rai na ɗaga ido na kalleshi, kafin na ankara shima gani nayi an ɗauke shi da mari wanda ba kowa bane face mahaifiyarsa,

" Hashimu rashin mutuncin da butulcin har ya kai haka? "

" Hajiya zo mu tafi, ba girman ki bane sannan kuma ba mutunci ki bane ki zauna akan layi ana irin wannan dake ba, tunda yace ba zaki shiga gidan nan ba ki rabu dashi muje kawai...." Juyawa nayi ina kallon mai Napep ɗin da ya saukeni ashe bai tafi ba duk wannan dramar akan idonsa ta faru, sai lokacin naga mutanen da Hashim ya tara min wanda sam da ban san dasu ba, sai kace ana ɗaukar film saboda irin yanda mutane suka taru suna kallonmu, ban jira komai ba na wuce na shiga Napep na bar Hashim da mahaifiyarsa tana yi masa faɗa kamar zata dafashi ta cinye, idanuwa na jajur ina shafa marin da Hashim yayi min kamar acikin mafarki nake kallon lamarin wai yau nice Hashim ya mara,

"Ai hajiya kin burgeni da kika mayar masa da maganar da ya faɗa miki, na san maganganun da kika jefe shi dasu su zasu hana shi bacci a daren yau.... Irin waɗannan samarin basu da mutunci ko iyayen su ma basu ɗauke su a bakin komai ba to kinga kuwa wa zasu gani da mutunci? Ke kuwa ƴar gidan masu mutunci ce daga gidan mutunci kika fito, mahaifinki ubane a wurin kowa a cikin garin nan babu wanda bai san shi ba...... Ni kaina nan wallahi kallon uba nake yi masa domin uban ne "

Jin abin da mai Napep ɗin nan ke faɗa ya tuna min da karamci da kuma ƙoƙari na mahaifinmu bawai iya musulmi kaɗai ba har waɗanda ba musulmai ba dan da kunnena naji wata Christian tana cewa" wannan mutumin uba ne " bata ma san ina da alaƙa dashi ba, har muka isa unguwar mu mai Napep yana yabon mahaifina da irin taimakon da yake yi wanda hakan ne ya rage min kaso mai yawa na ɓacin ran da nake ciki, a ƙofar gidansu ƙawalli na sauka har zan shiga naji mai napep yana tambaya ta,

"Hajiya kayan naki fa......"

"kaje dashi na bar maka"

"Allah yayi miki albarka ya yi miki sakayya da gidan aljanna...."

"Amin" na faɗa ina ƙoƙarin shiga gidansu ƙawalli zuciya ta na faman tafarfasa kamar zata tarwatse,

Tana cikin bathroom tana wanka zama nayi kan gadonta ina jiran fitowarta dan ji nake kamar idan ban amayar da abin da ke damuna yana yimin yawo a cikin zuciya ba yau ɗin nan komai na iya faruwa.

Can gidansu Hashim kuwa bayan tahowata Iya cigaba da balbala masa faɗa tayi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,

"Marar mutunci butulu, yarinyar da ta ɗaukoka daga rana ta saka a inuwa yau ita kake ƙoƙarin turawa rana.... Ita kake tozartawa a gaban mutane saboda baka gaji mutunci ba...."

"To wai Iya nan gidan ubanta ne da dole sai ta shiga?"

"Kaima ai ba gidan ubanka bane.... Koda ubanka ya mutu bai bar min gida ba nan gidan ɗan uwanane dan haka kaima ka tattara ka bar min gidana tunda kai ba ɗan goyo da zani bane"

"akan waccan yarinyar kike cewa inbar gidan nan"

"ehh akanta, maza ka tattara naka ya naka kaje duk inda zaka je"

Ɗakinsa ya shiga bayan kamar mintuna biyu ya fito riƙe da jaka ƴar goyawa,

"Wallahi idona idon Maimunatu sai na wulaƙanta rayuwar ta tunda ta zama silar rabuwa ta da mahaifiya ta"

"kaje kayi mata duk abin da zaka yi karka fasa amma kar ka manta itama da gatanta dan gatanta ma yafi naka, ubanta Alƙali ne kuma yayunta ma haka dan haka kamaka zasu yi su ɗaure har sai igiya tayi rara karka ce ban baka labari ba......"

Bai tsaya ba bare ya tanka kawai saka kai yayi ya fice daga gidan har lokacin iya na faman faɗa kamar zata ari baki, Amira ce ta shigo tana sanye da kayan makarantar islamiyya,

" Iya... Iya yanzu naga yaya Hashim da jaka, korarsa kika yi? "

" korarsa nayi Amira yaje can ya samu wata uwar...."


GARIN DAƊI.....! Where stories live. Discover now