~~~Yau da wuri na tashi daga office ban zame ko ina ba sai makarantar makafi, can na iskesu suna yin wasanni abun gwanin burgewa, an ɗaure zakara ansakeshi a tsakiyar fili sun bazu kowa yana yunƙurin kamawa, wuri na samu na zauna ina murmushi ni ɗaya duk da babu hashim acikinsu amma hakan ya sanyaya raina ganin suna rayuwa cikin farin ciki, suma kenan da halittarsu ta samu tawaya sun fawwalawa Allah komai suna rayuwa cikin godiyar ubangiji da farin ciki ina ga mu da Allah bai tauye mana komai na halitta ba ya zama dole mu kasance cikin hali na godiya da kuma takatsantsan akan duk wani abu da ya haramta,
Neman hashim na shiga yi ina yi ina tambayar ma'aikatan wurin da haka har aka kai ni wani wuri mai kama da office inda yake zaune kan kujera da wata na'ura gabansa yana yin typing sai dai tasu na'urar ba irin tamu bace masu idanu akwai bambance bambance masu tarin yawa, jin motsin shigowa ta yasa shi saurarawa daga abin da yake yi yayin da ni kuma nayi shiru ina takowa a hankali har na zo dab dashi ɗan karkato da kanshi yayi kafin naga yayi murmushi ya cigaba da aikin sa, zuwa can yace,
"munatu na ya aka yi kika san cewa ina nan? waye ya kawo ki?"
Murmushi nayi na nemi wuri na zauna kan wata kujerar roba koriya,
"kayi mamakin ganina ne a wannan lokaci?"
"a'a banyi mamaki ba, kawai dai na tambaya ne"
"Rakoni aka yi"
"to barka da zuwa, bari yanzu zan ƙarasa sai mu tafi"
"to shikenan"
Wayata na ciro daga cikin handbag ɗina ina yi masa hotona shi kuma yana cigaba da aikin sa har ya kammala. Gidansu muka wuce direct dan ina so inji ko iya ta samu zuwa gidan ɗan bahago, ita kaɗai muka tarar a gidan tana zaune ta kunna radio tana saurara maganin zaman kaɗaici, shigowarmu ya sanya ta kashe radion tana yi mana sannu da zuwa, nidai a tsattsaye muka gaisa na soma tambayarta ya maganar zuwanta wurin iyalan ɗan bahago?
"insha Allah dama gobe nake son zuwa, sammako ma zanyi da yardar Allah kan azahar na dawo"
"to shikenan iya ubangiji Allah ya kiyaye hanya sai kin dawo ɗin"
Sallama muka yi dasu na tashi na tafi kuma tun ina cikin napep naga manager na kirana amma ban ɗauka ba har sai da na sauka sannan na kira shi nan yake faɗa min komai ya zama daidai insha Allah zasu bani loan ɗin da na buƙata godiya nayi masa muka yi sallama na shiga gida.
Kamar yadda na tsara hakance ta kasance ba tare da wani kuskure ba domin na samu duk kuɗaɗen da nake buƙata, sannan cikin Ikon Allah lokacin da Iya taje gidan Malam Ɗan bahago ta iskeshi ya dawo daga doguwar tafiyar da yayi shekara da shekara a ƙasar Mali nan suka shirya maganar yadda zasu tafi Chadi domin shine zai yi musu jagora har zuwa gidan mutumin da yace shine zai baiwa Hashim maganin lalurarsa da izinin ubangiji,a ranar da na ɗauki adashena na haɗa da kuɗin wurina wanda na karɓi loan na kai musu domin cikin satin nan zasu yi tafiyar, ban tsaya iya nan ba har sai da na siyo musu wayar hannu mai sauƙin kuɗi wacce zasu iya sarrafawa domin jin halin da suke ciki domin tafiya ce zasu yi ta mota ba wai jirgi ba sannan hanyar cike take da ƙalubale kala kala kamar yadda Malam Ɗan bahago ya faɗa.
Tamkar zanyi kuka lokacin da naje yi musu sallama saboda da asuba zasu kama hanya gobe, duk nabi na shiga damuwa jikina yayi sanyi, tafiyar nan da Hashim zai yi ina ji ajikina kamar zan rasa wani ɓangare ajikina mai muhimmanci sai yanzu ne na gane irin ƙarfin girman shaƙuwar da muka yi dan na kasa ɓoye damuwata ji nake kamar inbisu mu tafi tare ayi komai akan idona in gani, shi da kansa sai da ya fahimci ina cikin matsananciyar damuwa daga ƙarshe yace to ko dai a fasa tafiyar tunda hakan na neman sakani cikin damuwa?,
Hawayen dake tsere akan kumatuna na goge sannan cikin raunin zuciya nace,
"A'a dan Allah karku fasa Hashim, lafiyarka itace gaba da komai awurina, kuje Allah ya kiyaye hanya ya dawo daku lafiya"
YOU ARE READING
GARIN DAƊI.....!
RomanceTabbas lamarin so yana da rikitarwa domin yakan jefa zuciya so da kaunar wanda bai dace ba, a wani sa'ilin so na mayar da mai yinsa kamar wani zautacce Hakan shine ya faru da widat....!