https://www.wattpad.com/1202777502?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=%2FTkRLP2mVOiOibQOmSAZomlKU5lZCJrKgGsadyz5zbb1oHJQIrUZmlujwcmwOYjvR2oNox9TifPEUZMrn51misnMzQo8zFd8GVZXdYgFwL3EV0XzHOhA8qWeZfnQs9hF
*<Babi Na Biyar>*
EWF
Wannan shafin gaisuwarki ce Mammyn Afreen ki more pagen da gasken gaske... Ina son COMMENTS ɗinki na musamman ne🔥😍 Nagode
_Mai yiwuwar tafiya ce mikakkiya! Domin duk zaren azabarin da zaka kulla sai ka samu yana sarkaffe da al'amurra mabanbantan ra'ayi! Mai yiwuwa kuma gajeruwar tafiya ce me kunshe da kaddararren al'amari! Ban sani ba amma matukar alkalami na Ya bani dama ba mamaki muyi fidda asalin kalmar kamar yadda muka saba cin karo da kowacce tafiya Nagode Mabiya ƘALLABI A TSAKANIN RAWUNA...🔥Son so daga Mai Daraja😍_
A hankali labarin Auren Fulani Aminatu ya zama mafi girman labarin da ta wanzu cikin masarautan da kewayar ta, ya kasance ko Innayo ce ta gfta gulmarta ake da ya feccenta. Kasancewar Innayoh ba karamar mace bace domin akalla tana shirin dosar shekaru Talatin. Amma a kasancewar ta baiwa mafi kusanci ga Fulani Aminatu dayawan mutane suke kiranta da Jakadiyar alkhairi. Musamman ma bayi yan uwan ta, domin ta kai kololuwar sanin Darajar kanta da kimarta.
Mace ce da ta fahimci abinda take, kuma su din can bayi ne na amana, wanda tarihi ya nuna tun da aka kafa masarautan zuri'arta take cikin masarautan kuma suke aikin Bauta, gashi ana hasashen Mai Martaba Sarkin Gombe zai barta da Fulani Aminatu. Kasancewar kamar Uwa ce a wurin Aminatu.
Tana zaune Jakadiya Bimbi tazo cikin tsananin son jin wani abu daga Innayoh ta ce mata.
"Jakadiyar alkhairi, wai da gaske uwar dakin ki. Sarkin Gobir zaa aura mata?"
Murmushi tayi sannan ta mike, bayan ta tattara zaren da take yin adon fure a jikin farin mayafin siliki, wata yadi ce da ake zuba da shi daga nahiyar gabas. Mai tsantsi da yauki, sannan yana wani irin daukar idanu kamar karanmiski, sai zaren audigar da take kadi da shi, wanda idan ta cire y'ay'an audigar take zama yayi kadin zaren. A hankali ta karkade mayafin sannan ta kalli Jakadiya ta ce Mata.
"Jakadiya kenan, ai idan ba aji mutuwar sarki a bakin bafade ba, ai ba za aji a bakin wawa." Tana gama fadar haka ta juya tana bin bayan Innayoh da harara, har ta kusan kulewa ta ce mata."Mai Martaba yana niman ki"
"Toh" daga haka bata kuma juyawa ga Jakadiya ba, domin matukar ta juya gare ta, zata iya magana maganar kuma da zata yi bata son ya zama kamar fidda amo ne daga danyen karfe.Tana shiga ta samu Fulani Aminatu, dauke da dan zomonta, a duniya Fulani tana masifar kaunar dan zomon ta da ta saka mishi dan dalago, wanda Hamma Buba ya bata shi kafin ya tafi sokoto karatu. Dan duk abinda ake Buba bai sani ba.
"Innayoh" ta kira sunanta a wani irin shagwababben murya. Kafin ta cigaba da cewa.
"Dan dalago yaki cin kome" yadda tai maganar gwanin ban sha'awa ce, domin irin Yaran nan ne da matukar suka samu gata da kulawa za ayi tabararrun yara ne masu cike da hutu.
"Toh ranki shi dade, ya zanyi da dan dalago tunda yaki cin kome, ba mamaki azumi yake?" Innayoh ta fada mata haka, d'ago kai tayi tana kallon Innayoh kafin ta sunkuyar da kanta ta ce.
"Innayoh!"
"Na'am ranki shi dade, kiyi hakuri mai martaba yana kirana, idan na dawo xan saka dan dalago ya ci abinci ko kuma yau na saka Sarkin gida ya yanka mana dan kai da kunnuwa""A'a Innayo kar ya yanka min abuna, zai tashi" ta fada kamar zata yi kuka, fita Innayoh tayi da sauri ta nufi babban shashi, da sallama ta shiga tana me zubewa akan gwiwar ta.
"Allah ya baka nasara, Allah ya baka lafiya! Allah ya tsare ka da tsarin shi Uban Aminatu Uban Sakina." Murmushi mai Martaba yayi, Sarkin Fada yana cewa.
"Mai Martaba ya amsa Jakadiyar Alkhairi, Mai martaba ya kuma amsawa Uwa ga Fulani Aminatu"Jibril ne ya gaya Zama wato Babayo, ya fara magana cikin dattako.
"Innayoh, Mutanen Aminatu sun iso,za a daura auren Ranar Juma'a, gobe kuma bamu sani ba ko zaku yi wani abin da ya shafi al'ada irin taku ta mata. Akwai sako daga masarautan elkaname wato masarautar borno na turare. Anan cikin gida kuma Balkisu ta gaya min wai ana wanka da madara da wasu al'adu, gobe insha Allah zata zo tare da Fulani Shatu zaku tsaya akan al'amarin Aminatu.""Insha Allah zan tsayar da hankali na da nutsuwa ta akan kome ba Fulani Aminatu" ta fada kanta a sunkuye.
Gyara zama yayi tare da cewa.
"Ban sani ba ko akwai yan dabarbarunku na mata, ki samu Fulani Shatu zata miki karin bayani""Inshallah zan same ta Yarimar gambawa" jinjina kai yayi,sannan suka sallame ta, bata koma shashin su ba, sai ta wuce cikin gida anan ta samu ana ta aiki kamar yau ne bikin. Saukewa da daurawa na manyan tukwane. Jakadiya ta tsaya akan kome kamar me, wuce su tai sabida yadda bayi suke kaunarta duk inda ta wuce mika mata gaisuwa ake. Har ta isa shashin Fulani Shatu, tun daga bakin kofar tayi karo da Kilishi. Cikin girmama ta zube tana gaishe ta.
"Rike gaisuwarki Innayoh, ai yanzu tsakanina da ku sai Alkhairin tunda Naji mai Martaba yar lelen shi a takaba zata kere"Murmushi Innayoh tayi bata ce kome ba, daga can dakin Fulani Shatu ta ce.
Hmm Kilishi kenan, dan tsakon da uwar shi ta kasa ai Allah ke ci da abin shi, ai Aminatu ta zama kainuwa. Idan ana faɗin mai rabon ganin badi toh ko da jinjibi Aminatu ta ketare iyakar kowa"Dariya Kilishi tayi sannan ta ce.
"Zuciyar mutum birnin sa, ai ba sabon abu bane carar zakara da tsakiyar rana, sai dai abid'a Sa'a da tagomashin alkhairi.""Sa kai yafi bauta ciwo, wani da barci wani da munshari. Toh bari mu ga waye me sa'a a tafiyar da babu guziri" inji Fulani Shatu.
"Ina niman tsari ga kukan Jaki, ai a nan nake da iko a can kuwa zaman takaba ya isa haka" tana fadar haka ta juya zata bar wurin. Fulani Aminatu ta ce.
"Da alamu dai tsayuwa bata karewa me shirin gyaran wata ba, bari mu jira muji ra bakin ki" a fusace ta juya tana kallon Fulani Shatu, kafin tayi kwafa. Kallon Innayoh Fulani Shatu tayi sannan ta ce mata.
"Ki dauka naji dadi da mai Martaba ya amshi bukata na, na barin ki a wurin Aminatu. Domin ba zata yi maraicin Uwa ba, ke din kamar wata Alkaryar ce a gare ta. Ki nuna mata yadda ake magana da yadda ake mu'amala da kowa. Ƙarki sake ta zama matattarar sharan kowa ki nuna mata babu Maraya sai rago, ki tsawatar mata, ki nuna mata kuskuren abu. Yarinya ce karki ce zaki barta tayi wasa kamar yadda take so, nan da shekara daya ba mamaki ta fara neman zama mace, domin idan ta samu kulawa kashin girma ne da ita. Ƙarki manta mareniya ce, Gwargwadon abinda kika bata gwargwadon yadda zata kula da kanta da ahalinta. Masarautan da zata shiga babban masarauta ce me ɗauke da manyan alamura ban sani ba ko zata iya dauka bazata iya dauka ba, amma na had'aki da Allah ki nusar da ita abinda ya da da domin da shi zamu yi alfaharin mu basu Y'a. Ƙarki sake abin kunya ya dawo Masarautan nan domin zai fi kyau a ci mu da yaki sama da a wayi gari masarautar mu tana fuskarta barazana da tsangwama sabida kuskuren wasu mun."Mika mata kayan tayi tana gaya mata yadda zata yi amfani da shi, da ku taimakawa Aminatu. Sannan ta ce mata.
"Akwai baki a cikin gidan nan ba mamaki zasu iya zuwa domin neman ganin Aminatu wannan hurumin ki ne a ganta yadda ya dace hurimin ku ne ki barta yadda zasu tafi da kowa, amma ki sani muna da kyakkyawan yakinin cewa ke mutum ce guda ba bari ba, Aminatu tana hannun Allah tana hannun ki duk abinda ya dawo ke ce me mafi girman laifi."Gyada kai Innayoh tayi, a yau wani nauyin ne ua kuma hawa kanta sama da koda yaushe, kuma a tsarin sarakuna babu abinda suke gudu kamar abin kunya basu kaunar su ji an shi a cikin masarautan su. Ga kuma Aminatu da kowa yasan yadda ta taso a cikin matsue da tsangwama ya isa ya karya zuciyar Innayoh.
Haka tayi ta godiya sannan ta fita daga shashin ta nufi nasu, koda ta isa shigar da Aminatu kewaye tayi ta ajiye ta tana faɗin.
"Kiyi shiru bari na Miki wanka" ta fada a hankali, fita tayi ta haɗa ruwan zafi sannan ta kawo madaran turare da Kwababben sabulu da lalle ta shiga wanke Aminatu da shi, tana gurje mata jiki.Fulani Aminatu fara ce kyakyawar gaske bata dauko kalar fatar mahaifiyar ta ba, sai ta dauko na Baban ta, sannan yanayin kyanta da jikinta na Mahaifiyar ce. Haka yayi saka mutanen gidan tsanarta domin itama Uwarta sabida kyanta ya kara rura wutar kishinta, a wurin Kilishi da sauran matan, sai da ta mata wanka sosai sannan ta fito da ita zuwa dakin su, ta shirya ya tsaf kafin ta shafe mata jiki da turare. Bata gama kimtsa ta ba, aka musu sallama daga bakin kofar shashin su....
__________________________________
*Ayi hakuri ban gama ba idan na gama zaku ji ni insha Allah a kai kai... Nagode sosai da jirana da kuke*
#Mai_Dambu
YOU ARE READING
KALLABI..! A tsakanin Rawuna...
Historical FictionThe gap between Love and Hate is not the same as the gap between Death and Life ... But to be killed or to win is one thing ... you are nothing .. in terms of Drawing Fate .. To die or not to live must be shared on two things ... Love and Destiny...