BABI NA SABA'IN DA BIYAR

437 104 10
                                    

BABI NA SABA'IN DA BIYAR
"Innalillahi wa'inna illahi raju'un!" Abinda fadar ya dauka kenan, Waziri yana kallon Gidado cike da al'ajabi, yadda yaro karami ya yaudara shi tare da mishi kwanton bauna.

Cike da mamaki yake kallon Gidado.
Sannan ya zubawa Tabawa idanun, yana jin yadda take kokarin tona mishi asiri a idanun duniya.
"Lokacin da Bingel ta shigo masarautar nan, shi ta fara gani ta ce mishi tana son ganin sarki don Allah yayi mata hanyar da zata gan shi,anan take ba shi labarin yadda akayi tasan shi, ita kaunar shi take. Shine ya dauke ta ya kawo ta sashin su har ake zargin marigayi Yakubu da shiga kan bayi ba shine Waziri ne. Shine yake shiga rigar Yakubu a zata tsohon sarki ne, lokacin da yasa ka aka mai da bingel gidan Chiroma daga baya yasa Chiroma ya bawa Sarki Bello ita a matsayin kwarkwarah,  kafin tazo wurin Sarki Bello yayi ta mu'amalar ta har ta samu ciki a lokacin sai aka danne cikin yadda lokacin da zaa bayyana shi kowa zai gamsu na Bello ne, koda aka kawo ta sarki Bello yaki mu'amalar ta sai da ta kai ga tayiwa Innayoh barazanar cutar da Aminatu ta hanyar d'aga mata hankali ta hanyar saka ciwon Aminatu ya tashi tayi ta barna bayan Baffa'm ya rufe mata yadda zai tashi,.da wannan innayo ta amince aka sakawa Sarki Bello maganin da zai saka shi bukatar ta, ita kuma tayi amfani da hakan tarar Sarki Bello har wani abu ta shiga tsakanin su, tun daga ranar bai kuma bin ta kanta ba, sai ranar da ta haihu, daga d'aga Yaron ya fahimci bana shi bane ni da kaina na ga haka a kwayar idanun shi, amma babu wanda ha fahimta, ganin idan na cigaba da zama da su kome zai warware shine ta saka aka tafi a kashe Ni, Yallabai Galadima wannan shine abinda na sani!"

Kallon Barkindo yayi da yake kuka wiwi, yana karawa kallon waziri yayi kafin ya ce.
"Laifin me na muku? Me yasa suka saka na biya bashin da ban ci ba? Me na muku a duniyar nan? Ku je a dauki Innar " ya fada a fusace.
A hankali ya warware igiyar alkyabbar jikin shi, yana kallon yadda kowa yake gyada,  takawa Gidado yayi gaban Waziri.
"Kayi mamakin yadda na shammace ka ne? Ko kayi mamakin yadda na tafiyar da kome kamar ban san me nake yi ba ko? Kamar yadda ka kashe kowa haka wancan sakaran zai idda nufin shi akan ka zan yi amfani da iyawa ta na ga ya saka an kashe ka, s cikin kwanaki biyu masu zuwa idan ka isa ka tserewa ƙaddarar mutuwar ka"

Sannan ya koma ya tsaya a gefen Barkindo.
"Kayi hakuri kukan da kake bai kai wanda aka saka ni ba, a cikin masu sakani kukan har da kai! Me yasa ks cewa Anum ni na kashe Lamido? Me yasa ka lalata min dangantakar da yake tsakanin mu? Kai adalin sarki ne amma kasa sani a yau a yanzun mulki ya haramta maka har abada kujeran da kake kai na cikin Jikin Anum ce, amma a matsayin ka na wanda yake iko na yau da na gobe zaka iya taimakawa wurin hukunta masu laifin da ake tare da su "

Shigo da Bingel aka yi, sannan Gidado ya juya ga Sarkin gida.
"Ina jin ka sarkin gida"
" A lokacin da muka fahimci Sarki Bello yana tare da Aminatu ba zai iya rabuwa da ita ba, sai kawai muka yi amfani da yadda yake gaya mana abinda take mishi na gujewa shimfidar shi, naso Aminatu tun daga ranar da na fara ganin ta, dan haka burina na raba ta da Sarki Bello duk da Abokina ne tun yarinta,sau gashi ba mutu akan matar shi, lokacin da na fahimci kudirin Waziri shima ta tafi akan soyayyar Aminatu da kishin ta sai na boye nawa halin na tsaya a bayan shi muka yi ta cutar da Sarki Bello ina kuma karawa Waziri kaimi, lokacin da yake adawa da Bello,duk da Galadima yaso ya fahimce mu sai muka yi kokarin dakatar da shi ta hanyar lalata duk wani shirin sa.
Amma daga baya sai da ya gano akwai hannuna a jikin Bello dan haka ya min gargadi akan na cire ko kuma ya kashe ni, nayi bakin cikin haka, shi yasa koda muka dawo wajen gari na sanar da waziri sai yayi kokarin dauke kai kamar bai san muna nan ba, har zuwa Gidado da shiga masarautar da yayi yana zaga gari, tun lokacin muka so kashe shi, toh sai muka fahimci ba zai iya mulki ba, sai ta gaya mana dan uwan shi yana nan mayaki ne, koda aka fara binciken sai ga Matar Lamidon ta bayyana, ba wai iya Lamido ne zai iya da ita ba,hatta Gidado zai iya sarrafa baiwarta sama da Lamido, sai aka yi dace babu wani alaka akan shi da ita, sai dai da zai tafi ya bayyana min na gayawa Baffa'm yana son Yarinayr, ni kuma domin na haifar da gaba da kiyayya a cikin gidan Bello sai na gayawa Baffa'm amma idan ta auri Gidado mutuwa zai yi ya haɗa ta da Lamido, koda yazo sai aka yi dace ya amince, amma shi bai da ra'ayin Anum,har na raka su zuwa Borno anan na gayawa Gidado cewa.
Mahaifin ku baya kaunar ka domin kai na kasashe ne, ba zaka iya mulki da kome ba, shi yasa na dauki matar da kake so ya bawa Dan uwanka dan baka da amfani, na cusa mishi tsanar dan uwan shi kafin su zo Gobir, so nake Yaran Bello su kashe junan su bakin ciki ya kashe Amunatu ni kuma na kashe Bello na dauke Anum, sai aka yi dace daga Uwar har Uban sun tankwara Gidado, har aka yi bikin bayan tafiyar Gidado, shine na gayawa Lamido domin idan gidado yazo lamido ya sa a kashe shi. Nace mishi naji labarin matar ka Dan uwanka yake so, har ba bashi wasikar gidadon da na ajiye, wanda na samu a ranar da na shiga dakin shi a Maiduguri. Sai dai na lura soyayyar Yaran Amunatu halittace daga Rabbil Alamin ba zasu tab'a cutar da juna akan mace ba.  Kwarai naso dawowarsa Lamido ya kashe shi,sai akayi rashin dace shi kuma a bangaren mulki Lamido ya hana Waziri sakat, ni kuma a cikin gidan su, sun hana ni sakat shine muka hada karfi da karfe muka kashe shi sannan muka tura Barkindo ya fadawa Anum ce wa Gidado ne ya kashe mata mijinta yadda koda an wayi gari za'a bashi mulkin zata hana ga hanyar zuciya ta kashe shi a gaban jama'a. Sai akayi dace ta zauce a kan mijin ta har yau bata dawo daidai ba, sai dai a yadda Lamido ya soke ni, na zata zan samu kulawa daga Waziri amma ina mutumin nan yasaka aka kai ni kogin wajen gari aka wurga ni a cikin ruwa wannan itace cin amanar da aka yi bayan wanda muka yi,  A yanzun na ƙara yarda da Bello yayi Kuskuren bawa mayaki mulki da manazarci ya bawa mulkin TOH wallahi babu wanda ya isa ya kawo har yau, domin a cikin shekaru talatin da wata shida da kwanaki ake shirin nan kai kuma a cikin wata daya da kwana takwas ka gama shirin ka wannan shine ake kira Jarumta ba iya takobi ya. Ahhhhhh!" Yayi shiru sakamakon soke Sarkin gida da Waziri yayi a makoshi.
Faduwa sarkin gida yayi yana shure-shure, har rai yayi halin shi.
Da gudu yayo kan Gidado,kafin ya iso barkindo ya yi wani tsalle ya dira tare da suke junan su. Inda ya kare Gidado.
"Yazidu!!!" Ya kira sunan shi da ƙarfi, a hankali Barkindo ya kuma soke shi sai da ya fito waje, shi kuma ya koma da baya ya rike gefen cikin shi.
"Shiiiiiiiii" Gidado ya durkusa kadan a gaban shi.
"Ayya karshen tuka-tiki tak, ka kashe Ubanka yau Danka ya kashe ka, kun bata rawan ku da tsalle babban burina a wanke kanku daga zunubi, maza ku fitar da shi, daga masarautar nan sannan a bawa Yazidu kulawa a lullube karagar da farin mayafi, nayi alƙawarin kafin Lamido ya cika arba'in zaku biya bashin da kuka ci, dan haka Bingel ku fitar da ita daga masarautar kar na..."
"Mahaifiya ta ce "
Juyawa yayi ya fuskaci Barkindo.
"Idan na ce dan yi amfani da zuciya har kai sai na datse wuyar ka, balle ita laifin ka na hada ni da matar dan uwana, dan haka ta fita a cikin masarautan kai ne dan uwana da bani da wani bayan shi ka sake ka kulla wani abu a ranka wallahi mutuwar wulakanci sai tafi kome wanzuwa a rayuwar ka, dan haka ka bi bayan su a jinyace ka, Muna da Ammyn da Baffa'm zasu bamu soyayyar da ya dace mulki kuwa babu kai babu shi har duniya ta tashi idan aka kwana biyu zan san yadda zan yi da kai lowa ya b'acce min a fadar "
Akan lokaci kowa ya kama ganin shi, shi kuma ya zauna a kasar fadar baya. Kowa ya watse, Baffa'm da ya zauna shima a gefen shi, sai lokacin ya daura kan shi a kafadar Gidadon, yana kuka hankali.
"Ina son ku babu wanda na ware saboda daukakar shi, tunda na dauki littafin ka na soyayyar bayan mutuwa. Na fahimci kai taka baiwar daban yake, da na kuma duba wata rubutun ka me mulki a Shari'ar Muslunci, sai na fahimci kai zaka iya mulki amma rashin baki ba zai baka damar haka ba, domin mulkin ce ta zabi Lamido ba ni na zabe shi ba, ban san dalilin da yasa suka min haka ba, ka yafewa dan uwanka da ni kaina "

Murmushi yayi sannan ya ce.
"Maguzanci da rashin wayewar musulunci yasa aka yi kome da kuma amfani da duba haramun ne a musulunci, ban san dalilin da yasa kuka yarda da cewa Lamido idan suka hadu da Anum zasu bada sa'a me yawa, a'a haramun ne soyayyar da ƙaddara ce ta haɗa su. Nasan kome zai faru yana kan turban addinin gargajiya da aka fara ne tare da yarda da Camfi, matsalar Anum ba wata matsala bace idan za a magance shi haka ma Ammyn za a iya magance nata idan har za'ayi amfani da magungunan Musulunci, ba wani tashin hankali bane. Sannan ranar da Lamido ya cika kwanaki arba'in ka koma bakin mulkin ka, domin kai ne ka dace da zama sarki a lokacin nan domin abinda Anum zata haifa mulkin na Uban shi ne."
Cike da mamaki yake kallon shi kafin bakin shi na rawa ya ce mishi.
"Baka sha'awan mulkin ne?"
Hawaye ne ya zubo mishi sannan ya sake murmushin yake ya ce mishi.
"Har abada na yafe mulki da duk abinda yake cikin shi, ina nan domin kare kujeran daga masu kawo hari "

"Don Allah kar ka ce min haka?"
"Wallahi na fada Baffa'm na haramtawa kaina kamar yadda dan uwana ya haramtawa kan shi farin cikin shi domin ni na hakura ka cigaba da rike mulkin kafin muga abinda zata haifa "
Duk yadda Baffa'm yaso yayi mulkin haka yaki, koda suka shiga cikin gidan Ammyn ma tasaka baki amma fir yaki sai ma cewa da yayi zai bar masarautan baki daya yasa suka hakura, tare da mamakin yadda yaki amincewa.
*
Bayan kwana biyu ne aka yi addu'ar arba'in Lamido Baffa'm ya koma kan mukaddashin Sarkin Gobir kafin asan abinda Anum zata haifa. Washi gari shi da Barkindo da ya samu lafiya, suka shirya suka raka iyayen Anum Somalia, a ranar da zasu tafi ne Kakar Anum take kallon Ammyn kafin ta ce mata.
"Tun da na ganki Aminatu nake ganin kamar ki da Yar Uwata Amratu, wacce aka ce Sarkin Gombe ya mai da ita kwarkwaran shi"
"Ikon Allah kece Rusailah?" Innayoh ta tambaye ta, ai kuwa take aka fasa tafiyar aka bude sabon filin hira, da koke koke da kaunar juna, ita kan  Yar macukule sai zare idanu da zaran an bata haushi sai ta saka hannu a baki ta fashe da kuka (🤣🚶🏾‍♀️😒😏😂 Anum yar macukule
#Mai_Dambu

KALLABI..! A tsakanin Rawuna...Where stories live. Discover now