BABI NA SHIDA

544 122 21
                                    

*<Babi Na Shida>*

https://www.wattpad.com/1204063012?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published

Wannan pagen gaisuwar taki ce Momyn noor Nagode kwarai da gaske 😍

A dan rude suka kalli kofar dakin, babban mayafi ta rufawa Fulani Aminatu. Jakadiya Jebu ce da wasu manyan bayi mata suka shigo cikin dakin, dauke da manyan manyan tasa na damamiyar lalle da yaji  turare. Kallon su Innayoh tayi kafin ta sake murmushi ta ce musu.
"Daga ina haka?" Wani irin kallo Jakadiyar tayi mata sannan ta ce mata.
"Ana babbakun giwa wake na zomo, Malama bamu hanya mu wuce, Fulani Aminatu zo ki cire kayan ki za a miki wanka da.."

    Bata kai aya ba Innayoh ta ce mata.
"Haba ai ko min saurain unguwar zoma ta jira haihu ko? Ki mai da shi an rigada an gama bamu bukatar na kowa sai na Allah"   dariya takaici Jakadiya tayi kafin ta ce mata.
"Kina wasa da ni ko?"
"Jebu ke kudi tara ta ce da zan yi wasa da ke? Ko ke Kanwar kakata ta ce da zan dara dake? Ga hanya nan. Kika sake wani abu ya same ta toh wallahi da baikon Sarkin Gobir akan ta ki jinjina girman rundunar mayakan su mana" murmushi tai sannan ta koma gefe ta tsaya.

"Me furcin ki yake nufi?" Inji Jakadiya Jebu, murmushi  Innayoh tayi sannan ta nuna mata hanya.

"Kowa ya ci tuwo dani hmm miya  yasha.  Ni jakar kaza ce sai na shiga sauran kajin suke shi Innayoh inda rai da rabo zaki biya bashin da kika ci" inji Jakadiya,
Dariya Innayoh tayi sannan ta ce mata.
"Haba? Gaske toh ai kafin ayi ɗaran akayi kwanɗi, dan haka ki ajiye a hannun ki wata rana ba mamaki Masha ruwa magirbi" a fusace  suka fita da kayan. Murmushi Innayoh tayi sannan ta cigaba da shirya Fulani Aminatu..

   **
Masarautar Gobir.

Ana cikin fadanci sunkuyar da kai Shamaki yayi sannan ya ce.
"Allah ya baka nasara, ya kuma taimaka dirken gobir" jinjina kai Sarki Bello yayi yana sauraron Shamaki dan yasan akwai magana a bakin shi.

       "Sarki ya amsawa shamaki" inji Sarkin Fada, cikin wani irin shakka da abinda zai fito bakin shi Shamaki ya ce.
"Allah ya huci zuciyar Barden Gobir"  "Sarki ya Amsawa Shamaki ya fadi abinda yake bakin shi" Sarkin Fada ya kuma faɗa, ganin Shamaki na gumi yasa Sarki Bello kara jinjina abinda yake son fada  ba karamin abu ba ne. Caraf Sarkin Zagi ya fara magana.

   "Allah ya baka nasara da nisan kwana, Shamaki ya kasa magana ai abinda yake son fada ba kome bane yaji rad'e rad'en da yake yawo a cikin masarautar nan ne akan Sarkin Gombe zai baka auren Yar shi ne dan ya fidda fulanin da suke cikin masarautan nan" ya fada yana muxurai. Dama shi sarkin Zagi an tanade shi domin sake kowacce irin magana da tayiwa kowa nauyi toh shi ko a gaban waye zai fade ta sai dai idan Sarkin ba adali bane yasaka a zage sarkin Zagi.

     Shiru fadar yayi kowa yana jiran aji me Sarki Bello zai ce. Har ya mike ya zai bar fadar aka shiga cewa.
"Gyara kintsi mai martaba zai tashi" a hankali ya mike ya bar fadar, bin bayan shi da ido Shamaki yayi yana sauke ajiyar zuciya, domin abin da bai zata bane. Kallon Sarkin Zagi yayi tare da mai da hankalin shi kan kujerar da Sarki Bello ya mike.

"Barka da arziki" Chiroma ya fadawa Shamaki, girgiza kai yayi.
"Kana tsammani da Iro ne tuni ba a sauke min rawani na ba" murmushi yayi shima ya bar fadar yana dariyar Shamaki.

   Haka dayawan dattawan fadar suke mishi barka da arziki, domin kuwa ta tsallake rijiya da baya.

  --
A can turakar Sarki Bello, zama tayi yana cire kayan shi, Sarkin gida yana bakin kofar shiga.
A yau yana jin tsohuwar al'adar shi tana kuma yawo a ranshi. Gyaran murya yayi Sarkin gida ya shigo tare da zubewa kasa.
"Tashi bana son kana min haka." Tashi yayi ya zauna yana murmushi.
"Allah ya baka nasara." Kallon juna suka yi kuma suka sake murmushi lokaci guda.
"Ina son shiga dawa" ya fada yana kishingida, a saman gadon shi. Gyara zama sarkin gida yayi yana faɗin.
" Ba dai da rana nan ba? Wani ya bata maka rai ne?" Yayi mishi tambaya biyu lokaci guda, sai kuma ya gyara zama sannan ya cigaba da ce mishi.
"Tsohuwar al'adar ka ko? Amma me zai hana kayi rubutu, ko kuma kayi barci yadda suka zama al'adar ka"

KALLABI..! A tsakanin Rawuna...Where stories live. Discover now