BABI NA ARBA'IN DA BIYU
A hankali ya juya yana kallon su, Kafin ya juya ya kalli Barkindo, cikin mugun tausayi da bai tab'a jin na wani a cikin masarautan nan ba, tun bayan sarki Bello bai tab'a jin wani a cikin masarautan ba, sai Barkindo wani irin Tausayin shi Yaron ya cika zuciyar shi, bai da laifi ko daya bai san kome ba, Asalima masu laifin daban hukuncin laifin ya sauka a bisa ƙaddaran shi.
"Yarinyar zata iya sauya ƙaddaran shi, idan ta amince da shi, amma idan har taki amincewa babu dole, kuma duk wanda ya tunkare ta, tabbas abinda bai faru akan Fulani Aminatu shine zai faru, domin akwai kariya a tare da ita."Rufe bakin ta tayi cikin tashin hankali, ta ce mishi.
"Ba dai itace Kallabi a tsakanin rawuna ba" har ya isa bakin kofar fita daga cikin dakin, ya juya a matukar sanyayye ya ce mata.
"Bani da tabbas" ya fadi haka domin kare darajar Anum domin kuwa idan ya sake ya fadi wani abu toh ba makawa rayuwar yarinyar yana cikin hatsari, fita yayi cikin nutsuwa, amma a zuciyar shi babu nutsewa tun jiya yaji haka a ran shi, itace sanadin dawowar jiya da aka rasa Yau, dan haka ya nufi inda gidan shi yake ya shiga ya fara rubutu cikin zafin nama, sannan ya kira wasu Amintattun bayin shi. Daya ya tura shi yankin sokkoto da sakon galadima, biyu kuma ya basu sako su tabbatar saka a kofar Masarautan.
Inda me zuwa Sokoto ya gajarce mishi tafiya, yadda zai isa Sokoton da sauri.A can cikin masarautan kuwa, shiru kowa yayi da bakin shi domin kuwa abinda ake nima ne, gashi ya zo cikin kankanin lokaci, a sace aka fara yunkurin niman Anum. Domin cika burin su na zama sakarunan masarautan.
**
Kwana biyu ya dauka, kafin ya warwarewa, dan haka babu bata lokaci suka fara yunkurin tafiya makaranta, har sun gama shirin su, ranar da zasu tafi har iyakar Borno da Chadi aka raka su, sai dai koda suka tafi Gidado yaki mai da hankali ga karatun sa, Makarantar yana karkashin koyarwa Imam shafi'i, ana koyarwa sosai.
Sun tafi sun bar Fulani Aminatu da mugun kewar su.
**
Sokoto.
Lokacin da sako ya iso wurin Galadima, duba sakon yayi tare da nufar wurin Baffa'm ya zauna ya ce mishi.
"Lokacin komawa gida yayi, cikin wannan makon zamu koma kaje Insha Allah Aminatu tana nan tafe" kallon shi yayi kafin ya ce mishi.
"Ban gane me kake nufi ba?"
"Sakon da aka kawo min yana da nasaba da ita, bari na karanta maka kaji yadda sakon yake"
_AMINCIN ALLAH YA TABBATAR A GARE KU, KAMAR YADDA NA GAYA MAKA KUYI NISA KUYI DOGON TAFIYA YADDA XA A MANTA DA KU, INSHA ALLAH ALLAH XAI KAWO MAFITA. ALHAMDULILLAHI MAFITA YA ISO LALLAI INA SON NAN DA MAKO GUDA KU ZO GIDAN DA YAKE KUSA DA RUGA.... YARINYAR TA BAYYANA SAI DAI A WANNAN KARON AN SAMU AKASI DOMIN RAYUWAR TA YANA CIKIN BARAZANA KOWA YANA BUKATAR TA, IDAN DA HALI KUZO AKAN LOKACI, DOMIN KU BATA KARIYA AMMA NASAN TANA TARE DA KARIYAR UBANGIJI DOMIN ZAKUNAN DA SUKE ZAGAYE DA AMINATU SUN KASANCE TARE DA ITA KUZO DOMIN ZAME MATA GARKUWA_
"Kenan Zuri'ar Aminatu suna raye?" Baffa'm ya fadi haka, fuskar shi tana kara bayyana tashin hankali, shi yanzun da tsufar shi ina zai kai budurwa? Ai abin kunya ce ace yau yana auren yar cikin shi ga shi bai san me AMINATU ta haifa ba.
Galadima kamar ya karanci abinda yake kwance akan fuskar baffa'm ya ce mishi.
"Malam Jarumin soyayya bafa yarinyar ce zaka aura ba, ina jin wani al'amari akan cikin da Aminatu ta tafi da shi, ina ga shi zai kasance da ita."Murmushi baffa'm yayi yana shafa kan shi da ya kara bayyana girman shi, wato furfura.
*
A cikin satin suka yi sallama da Inna Marwa, mai maganin shi ya je da kan shi ya amshe su, ya kawo su masaukin da yayi musu kusa fa ruga, sannan ya shiga har cikin rugar suka nime mace dattijuwa da zata na shiga cikin gidan tana musu aiki, kiri kiri suka ki yarda dole suka tura Anum, kuma dama abinda yake bukata kenan shi yasa yayiwa masu niman Anum iyaka. Kuma alhamdulillahi, lokacin da Baffa'm yayi ido biyu da Anum, haka kawai jikin shi ya bashi girma da nasabarta da Fulanin shi, dan haka yayi ta tambyar ta, tana bashi amsa har ya zuba mata ido.
"Yanzu idan kina gama mana aiki kiwo?" Ya tambaye ta,
"Eh Baffa'm!" Da wani irin sauri ya zuba mata ido.
Ƙasa magana yayi yana kallon ta, baki daya ta rikide ta koma mishi Minani.
Haka ta wuce ta cigaba da aikin ta,.har ta gama ta ajiye sannan ta musu sallama.
Zuwan su baffa'm yasa ta samu nutsuwa kuma bata cika zuwa tallar nono ba,
YOU ARE READING
KALLABI..! A tsakanin Rawuna...
Historical FictionThe gap between Love and Hate is not the same as the gap between Death and Life ... But to be killed or to win is one thing ... you are nothing .. in terms of Drawing Fate .. To die or not to live must be shared on two things ... Love and Destiny...