BABI NA SABA'IN CIF
_EH SABA'UNA😂🤣 ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI DA YADDA KUKA AMSHI LABARIN_Hankali Galadima ya janyo Gidado zuwa bakin gaba domin yadda ya sha ruwa kamar ya mutu, a hankali ya kwantar da shi, shima kwanciya yai yana tari, kafin ya Kalli Gidado.
A hankali ya mike, duk da jikin girma haka yayi ya matse cikin shi yana aman ruwa da jini.
"Ka tashi ka tashi domin gaskiya ta rayu koda zamu rasa rayukan mu ba zamu tab'a gudu ga abokan gaba ba, tashi Sarki Husain masarautar Gobir tana ci da wuta karka sake wutar ta cinye da Abinda kake so! Anum tana hannun makiyan ka, ita ce makami me linzamin da ta rage maka, ita take da ikon tafiyar da kome."Ya jima akan shi, kafin ya fara tari yana amai. Bude idanun yayi yana mika hannu.
Dariya Lamido yake mishi tare da mika mishi hannu, sai kuma ya mai da hannun shi a hankali yana kallon hannun.
"Ka tashi Ammyn da Baffa'm suna jiranka, itama tana jiranka. Zam tafi bana son na makara ne." Har ya juya zai tafi ya d'an juya kadan sannan ya ce.
"Nagode da bani damar haka da kuma hakuri da kayi dani, ina maka fatan Alkhairi " a hankali ya cigaba da tafiya a cikin wani haske har ya daina ganin Lamido, a firgice ya farka kallon galadima yake kwance.
A hankali ya kai hannu zai cire kibiyar yaji gurnanin zakin su, cire hannun shi yayi Tagwai ya cire kibiyar da bakin shi, kallon Biyuna yayi yana tsaye shima, tashi yayi ya nufi wurin su. Zubawa sukayi suna gurnani.
Dawowa yayi ya dauki galadima ya sab'a shi a kafadar shi, suka nufi Masarautan.
"Karka bar kowa da rai, kar kayi irin Kuskuren da muka saka lamido yayi na kin kashe kowa. Ka bayyana a matsayin shugaban su"
Haka yake ta nanata mishi kalma daya, har ya isa Masarautan, buga kofar yayi aka ki budewa, gyara rike galadima yayi cikin wani irin fushi da fusata ya saki da kofar da kafar shi, wani irin faduwa kofar tayi tare sa karyewa. A hankali ya shiga kofar birnin yana kallon yadda aka zuba masu tsaro.
Sauke galadima yayi sannan ya kalli yadda suka yo kan shi.
"Idan kuka sake nayi amfani da iyawata matan ku da Yaran ku ne zasu zama marayu da zawarawa, idan kuka yi mubaya'a zan baku yanci. Ni Husainin Muhammad Bello."
Kamar jira ake ya ida Fadar sunan shi Masarautan ta dauki sabon gud'a, tare da buge buge kamar yadda aka yiwa Lamido.
A hankali suka yi ta Zubawa akan gwiwar su, suna bada hadin kai.
*
"Gud'ar me nake ji?" Chiroma ya tambayi Waziri,
"Gud'ar kasancewar Barkindo ya zama sarki na gaba "
"Bana tunanin haka!" Bai kai ga rufe baki ba, dakaru biyu suka shigo fadar.
"Yarima Gidado ya dawo."
Zubur suka mike.
"Kenan gud'ar nan Washi suka yiwa Lale Maraba da sabon Sarki? Haka na nufin jinin Bello ne zasu rike masarautan nan" murmushi Zakaria yayi sannan ya kalle su
Ya ce."Kowa ya koma gidan shi, kafin rana ta fito"
Haka kuwa ya faru kafin Gidado ya iso masarautan kowa ya kama gaban shi.
A can kuwa Bingel da Barkindo sun juyawa Anum tunani da duniyar ta, domin baki daya sai da suka bata labarin cewa ai Gidado ya kashe lamido ne sabida yana son ta, sannan kuma yana son mulki, shi yasa ya nimo magani yayi baki.
Dakyar suka dakatar da ita a daren domin birkice musu tayi tana son ganin Lamido."Idan muka barki wallahi kashe ki zai yi akan mulki, domin idan yasan ba zaki yarda da shi ba toh abinda zai yi kenan, ke baki da Buri ne akan cikin jikin ki" kallon su take domin bata yarda lamido zai mutu ba.
"Kun zata zai mutu ne haka, ina ji a jikina bai.mutu ba yana raye"Duk yadda suka so mata bayanin mutuwar Lamido taki yarda akan ya mutu, sai da aka yi sallah asuba.
Lokacin labari ya karade ko ina, sannan Alkali da Liman da Baffa'm da Allah ya hana shi magana suka shiga kan gawar Hassan, a lokacin Gidado ya shigo. Ajiyar zuciya Baffa'm ya sauke tare da kallon Gidado.
"Suturar mutane biyu za ayi ga Gawar Galadima shima"
"Ta mutane uku ne Gidado Hadizah ma ta mutu" jijiyar jikin shi ne ya mike murda'murd'an a gaban goshin sa da ilahirin jikin shi.
"Innayoh da wasu bayi zasu kula da ita."
Shigowar Waziri da su Chiroma suna kuka yasa baffa'm kallon su sai lokacin hawaye ya zubo mishi, yana kallon lokacin da suka yi ta saran Lamido, haka yasa shi ja da baya. Fita Gidado yayi ya koma cikin gidan tare da nufar sashin Ammy ya samu da mutane har da bingel. Sannan ya nufi sashin sa, zam-zam da turare tare da likafanin, shi ya sayawa kan shi ne lokacin da malamin su ta tafi Umrah ya da sako a kawo mishi ashe wa Hassan ya sayawa, sai da ya fito ko d'igon kwalla babu a ran shi, zuciyar shi zafi take, a lokacin da ya kai har an rasa yadda za ayi da Lamido saboda raunin jikin shi, shi ya kwabe tare da zama ya wanke dan uwa shi tass, sannan aka d'ago shi ta shirya shi.
"Ban tab'a kawowa da kaina zan shirya ka ba Hassan na san kai zaka shirya Jana'izata ba ashe ni zan shirya naka. Kafin yau na zata Ni zan mutu amma yau da na ga ni nake shirya gawan ka na yarda da cewa cuta ba mutuwa bace! Allah yasa Aljanna ta zama makomar ka."
Sannan ya mike ya kalle su, kafin ya ce.
"Bari na gyara jikina"
Fita yayi daidai lokacin da Barkindo ya rako Anum, dauke kai yayi kamar bai ganta ba.
"Laaa kaga Hamma Lamido" ta nunawa Barkindo Gidado, d'ago kan shi yayi ya zuba a bayan Gidado gaban shi ne ya fadi.
Kafin yayi magana Anum ta biyo Gidado da gudu tana rike hannun shi.
"Dama nasan baka mutu ba, da aka ce min Gidado ya kashe ka Sabida mulki da kuma ni, nace musu karya ne kai Jarumi ne ba zaka mutu a hannun Gidado ba, domin kana son shi ba zaka bari ya kashe ka ba"
Juyawa yayi tare da sunkuyar da kan shi.
"Kiyi hakuri Ammyn tana ciki"
Ja da baya tayi tare da rufe bakin ta.
"Ina Lamido?"
Bai bata amsa ba, ya shiga abin shi. Da sauri ta juya wurin Barkindo da yake ji kamar ya sake fitsari a wando dan tsoron irin kallon da Gidado yayi mishi, kamar Lamido ne yayi mishi wannan kallon, a raxane ya rakata har kofar Ammyn ta shiga. Daidai Innayoh ta fito daga dakin da ake suturar Hadiza.
"Innayoh Ina Lamido?"
Cikin karfin Zuciya Innayoh ta ce mata.
"Ki shiga wurin Ammyn" a hankali take ratsa mutane, tana shiga ta kalli Ammyn da Bintu.
"Ammyn Ina Lamido?"
"Sun kashe shi" inji Bintu.
Dariya ta kama yi tana cewa.
"Ba fa zai mutu ba"
Shigowar Baffa'm da wasu maza aka fita da gawar Hadizah, sannan aka kai babban zauren gidan.
---
"Kayi hakuri!" Ta fada tana daure mishi ciwon shi, sannan ya dauki kayan shi ya saka.
"Kin jima da sanin mahaifin ki yana cutar ai? Me yasa baki gayawa Lamido ba? Sannan a ranar kin san abin zai faru kika zo kina gaya min nayi hakuri, Haimah nasan mahaifin ya jima yana abinda ya gadama, idan ke ce wani hukunci zaki yanke!" Yana fadar haka saka alkyabar shi ya fita. Kuka ta zauna tayi tayi, koda ya fito hango Innayoh yayi tana rike da Anum, Bintu ta Fito da Ammyn."Innalillahi wa inna alaihil raji'un allahumma ajirni fii musibati wa'akhlifni khairan minha, Wayyo Allah na Mijina wayyo Allah ku dawo min da Mijina na hada ku da Allah, don Allah Wayyo Allah Innayoh ki ce su dawo da shi wallahi bai mutu ba, wallahi bai mutu ba!" Rintsa idanun shi yayi yana jin kamar ana caccaka mishi kibiya a kirjin shi, cikin kuzari irinta sadaukan maza ya nufi inda gawar dan uwan shi take ya dauka tare da taimakon wasu daga cikin manyan fadawa aka fitar da gawan daga cikin gidan.
Kwace rikon da Jakadiya tayi mata, ta nufesu da gudu, cikin ihu da karamin Hauka ta ce.
"Ina sonka! Ina son ka!! ina son ka mijina!!! Wallahi nima mutuwa zan yi idan baka tashi ba!" Ganin ana ƙoƙarin rike ta, da gudu ta kuma shan gaban su, tare da kifa mishi mari.
" Ina ka tafi aka kashe min shi? Meye nayi maka da muka cancanci kyautar mutuwa? A daidai lokacin da nake shirin gaya mishi na shirya zama da samun soyayyar gaskiya?" Ta fada da ƙarfi, bai d'ago ya kalle ta, dan yasan dole tai haka, yasan dole tayi kewar shi, kamar yadda shima yake kewar shi."Ka kashe shi ne domin ka samu lafiya ko? Ka kashe shi ne domin ja mallake kowa da kome? Ka kashe shi ne domin kar daya daga cikin mu ta haifa mishi wanda zai zai rike mulki a?? Ka kashe shi ne kawai dan ka mallaki Masarautar Gobir Gaya min"
Tayi maganar da mugun ƙarfi, yadda ya haifar da wata irin amsakuwa, sarawan da kanta yayi yasa ta ja da baya zata fadi, Shehu yayi maza ya amshi inda yake rike da mankara, bayi mata ne suka nime riketa ta daka musu tsawa.
"Karku tab'a ni! Babu wanda ya isa ya fitar min da gawar mijina" d'ago kai yayi tare da kallon Waziri da liman, gyada mishi kai, da sauri ya nufeta aikuwa ta kuma haukacewa tana cewa.
"Wallahi ka tab'a sai na kashe ka" da sauri Innayoh ta isa wurin shi tare da cewa.
"Allah ya taimaki
Yarima, Fulani tana dauke da juna biyu, bayan haka da alamu yana niman fita domin ga alama nan a inda take tsaye" ta fadi haka cikin laskantar da kai, da wani irin sauri ya d'ago kai yana kallon ta. Jini ke zuba a tsakanin kafarta
Lashe bakin shi yayi tare gyada kai ya nufeta.
"Wallahi ka tab'a ni sai na kashe ka" kafin ta yi wani yunkurin, ya samu nasarar cafketa, wani irin ihu take tana fisge fisge, ya juya tare da cewa.
"A fita da gawar"Sannan ya dauke ta, tana ihu da fisge fisge, haka ya wuce da ita dakin mahaifiyar su, sannan ya dube ta cikin kulawa ya ce mata.
"Innayoh Ammyn a kula da abin jikinta, kar na rasa shi kamar yadda na rasa dan uwana"
"Karya kake kashe min shi kayi, kuma wallahi sai Allah ya saka min ya saka mishi, kuma tun wuri ka ajiye tunanin mulkin nan da kai gwara Barkindo dan shi yana son Mijina." Ta fada tana wani irin jan numfashi sama sama.Fita yayi bai kuma bin ta kanta ba, yana fita waje, ya samu shi ake jira. Dan haka aka sallaci gawarwakin aka kai sui makwancin sui da yake cikin masarautan.
*Sorry ban yi editing ba!*
YOU ARE READING
KALLABI..! A tsakanin Rawuna...
Historical FictionThe gap between Love and Hate is not the same as the gap between Death and Life ... But to be killed or to win is one thing ... you are nothing .. in terms of Drawing Fate .. To die or not to live must be shared on two things ... Love and Destiny...