BABI NA SITTIN DA UKU
Make hannun shi, tayi cike da matsanancin kunya dan sai yanzu ta tuna da wani ido zata kalli surukanta. Kamar wata yar Yarinya karama ta kalle shi tare da zubewa a kirjin shi ta ce.
"Baffa'm!!!" Ta kira sunan shi matukar shagwab'e, hawaye ne ya shiga sauka daga idanun shi, ya rasa wani irin farin ciki zai yi a karon na biyu a rayuwar su.
"Baffa'm ina jin kunyar su Bintu da Anum!"
"Kai haba?" Ya tambaye ta muryan shi na nuna damuwarsa a fili ƙarara.
"Baffa'm!"
"Hmm Fulanina! Me kike so? Baki koshi da ni bane?" Ya tambaye ta cikin wani irin kulawa.
Ware idanu yayi tana dukar kirjin shi.
"Baffa'm dan taimaka min na gyara jikina"
Kamar jiran Umarnin ta yaƙe, ya dauke ta cak, yayi ban daki da ita (al'amarin soyayya ba lallai sai matasa ba, har yau turawa sun fimu cigaba wallahi basu tsofa a tattalin juna da nuna kaunar juna amma sai kaji bahaushe nacewa chaii gaskiya mu sauya hali idan ba haka ba zamu iya karewa muna ji muna gani bamu moru rayuwar mu ba, akwai mata dayawa da suke da matsalar a rayuwar auren su, wanda deeply inside din su suna fama da rashin kulawar aure da d'a namiji, matuƙar rayuwa zata cigaba da tafiya ba makawa mata dayawa zasu faɗa sharrin shaidan Allah ya kyauta)Sai da ya taimaka mata tafito daga wanka ta shirya suka fito tana zuba kamshi irin sabon auren nan, kallon gidado tayi da yake gaban abinci, sai wasa yake da abincin gaban shi.
"Ubana ya dai?" D'ago raunanin idanun shi yayi, a hankali ya ce mata da hannu.
"Babu kome"
Zama suka yi suna kallon shi, duk ya fige kamar ba shi ba, yana kokarin boye damuwar shi amma sai da suka d'ago shi.
"Kayi hakuri da abinda ya Fãrû, ni na yanke shawarar hada shi da yarinyar." D'ago kai yayi yana kallon Baffa'm idanun shi cikin na Baffa'm a hankali hawaye ya fara zuba daga idanun shi. Dunkule hannun shi yayi jikin shi yana rawa, hannun ta ta daura akan dunkulallen hannun, idanun ta a lumshe, tana buga hannun a hankali kallon su yayi a hankali ya sake hannun, ya fara sauke ajiyar zuciya.
"Ko kana son na mutu ne?" Girgiza mata kai yayi.
"Ban isa na roki arziki ba ne? Na roki arzikin a bar maganar nan iyakar mu ko ban roka ba? Idan har na isa toh ka ajiye Anum a matsayin surukar ka ko wasan kanin miji bana so! Bana son alakar da ta wuce na Musulunci idan ba haka ba."
A hankali ta Lumshe idanun ta, kafin ta bude ya koma wani iri.
"Zan bayyana kaina kar a tsalleke abinda nake bukata"
Rike kadadar ta Baffa'm yayi yana cewa.
"Zai fahimce ki ba sai kin fusata ba" baki daya suka kuma shiga rarrashin sa, da nuna mishi illar hassadar da take shirin kama zuciyar shi. A tare su uku suka karya,sannan suka shiga cikin gidan sarautar suka kai gaisuwa, matan mai Martaba sai tsokanar Ammyn suke tare da zolayar, har suka fito akan gobe za a dauki hanya zuwa Gobir.
Surikar su baki daya suka tawo suka gaida iyayen mazan su, kafin suka koma aka cigaba da gyara, da shirin komawa masarautan.
Washi gari kuwa suka D'aga daga borno. Zuwa Gobir,
**
Tunda Baffa'm suka bar Gobir ake samun cigaba na ban mamaki, talakawa da kan su sun yarda an yi sabon Sarki, domin shi sa galadima suka yi badd'a kama suka shiga cikin gari suna duba abubuwan cigaba da aka samu da wanda aka fadi, da yadda kome.
Da ya gama zaga Masarautan da al'ummar shi, a hankali ya haura katangar wurin hutawar Baffa'm, yana kallon ko ina. Gyaran murya ya ji a bakin kofar.
Kallon ta yayi sannan ya nad'e hannun shi a kirjin.
"Mara kunyar da ya iya dukar kwarkwaran Uban shi, kazo ka samu mulki ka haye kamar yadda nayi adawa da Mahaifiyar ka a wancan lokacin naji Bello ya je dawo da ita. Hmm kallon ku nake" murmushi yayi sannan ya taka gaban ta tare da kai fuskar shi kunnen ta ya fada mata wani magana da yasa ta yanki jiki ta faɗi. Jikin ta yana rawa. Durkusawa yayi, sannan ya ce mata.
"Kin zata babu wanda ya sani ne? Kowa zuba muku ido yayi taga tsalle birin ku,, idan kika gama kafin duniya ta gaya mishi gaskiya ji fara gaya mishi kafin ba dawo kan ku, an haife ni ne domin daukar fansa, na rantse da Allah kamar yadda kuka saka ta kuka sai na saka ku kuka, na jima da ajiye kome akan ku dan haka ki gama kewaye-kewayen ki namiji ne a gaban ku!"Yana gama fadar haka ya tsallake ta yayi tafiyar shi, mutanan nan sun cuci iyayen shi, sun zalinci iyayen ba zai tab'a barin su su huta ba har sai ya ga bayan su kaf din su, shi yasa ya hana ayiwa su Chiroma kome ya bar su a inda babu wanda ya sani daga shi sai Galadima ko Baffa'm bai gayawa mishi ya sauya musu gida ba, gudun kar a samu matsala daga baya.
Dan haka ya shiga binciken shi, bayan tafiyar su Baffa'm da kwana biyar aka kawo Fulani Dija,daga Kano kallo daya yayiwa sashin ta, bai kuma bin ta kanta ba, dan baya kaunar ganin fuskar ta, kuma yayi alƙawarin yadda aka kawo ta haka zai bar musu ita. Domin duk wanda ya tab'a martabar Mahaifiyar shi har duniya ta tashi tsakanin su takobi, ita kuma tayi abin har abada ba zai yafe mata ba. Dan idan ya ce ya dauke ta a matar shi toh tabbas ya tabbatar wanda bai san darajar kan shi ba kenan.
Tun daga ranar da aka kawo ta aka fara shirin biki daga gidan Galadima ake shirya duk wani bikin da ake, haka abincin shi a tare da galadima suke ci, domin yarda da yasa galadima sakawa ana saka musu abincin, wani abin da yake kara musu son zama tare shine yadda Lamido vaya aikata kome sai abinda galadima ya gaya mishi, kuma abin yake yi kai yi ba yayi kai tsaye sai da shawarar galadima, sannan Galadima ya bashi wasu irin abubuwa da wasu sirrin masarautan, da kome da ya dace. Sannan ya bashi Shawaran ya nemi maganin tsarin jiki saboda mulki sai da niman kariya, murmushi kawai yake yace toh zai nima.
Satin su Baffa'm biyu suka dawo, inda aka daura biki na garari, da ya samu halartar manyan sarakunan kasar Hausa har zuwa wasu sassan, anyi bikin da ko a tarihi ba a tab'a yin irin shi ba, musamman wasan dawakai da aka yi, Anum tana kallon yadda lamido yake wasan doki, cikin wani irin farin ciki, take kallon shi kamar ta dauke shi, lokacin da Dijah ta zo wurin ganin yadda Anum take kallon lamido kamar an ce ya d'ago kai ya zuba akan Anum, tana kallon shi.
Kallon gefen ta yayi yaga Dijah, tawowa yayi gabanta, ya sauka tare da cire alkyabbar shi ya rufawa, sannan ya sunkuyar da kan shi daidai kunnen ta, ya kama a hankali ya ciza, wani jan numfashi tayi tare da rike rigar shi, tare da d'ago kai tana kallon shi hura mata isar bakin shi yayi. Sannan ya juya yana me hawa dokin shi.Kallon shi Gidado yayi cikin takaici dama tunda suka iso yaki yarda su hadu, sai ma wani kauce mishi yake, yanzun da yaga abinda yayiwa Anum gani yake kamar da gayya yayi mishi, shi kuwa yayi haka ne domin ya kular da Dijah, ai kuwa, zubawa Anum ido tayi cikin tsannanin kiyayyar ta da mugun kishin Anum, take kallon ta har aka gama wannan taron, tana zaune ita da Bintu suna cin abincin, sai kus-kus suke suna dariya a can gidan su Haimah itama Anan ake nata shagalin, Dijah na gidan Galadima, sai wani kunci take ba ta dauka zata ga Anum haka ba domin taji labarin an daura auren shi da wata, amma ganin Anum yasa mata masifar kaunar Lamido, bata kuma gigita da al'amarin shi sai da yazo yayi mata wannan abin.
...
"Kin yi sa'a fa Anum Lamido yana son ki ya nunawa duniya yana tare da ke" kunya ce ya kamata, tana murmushi.
"Addah don..." Hàdiye yawu tayi sakamakon shigowar, kasa karasa maganar tayi tana zare idanu.
Mikewa Bintu tayi tare da gaishe shi. Jinjina kai yayi tare da zubawa Anum idanun yana karantar rikicewar ta...
💪👑
Ayi maneji
#Mai_Dambu
YOU ARE READING
KALLABI..! A tsakanin Rawuna...
Historical FictionThe gap between Love and Hate is not the same as the gap between Death and Life ... But to be killed or to win is one thing ... you are nothing .. in terms of Drawing Fate .. To die or not to live must be shared on two things ... Love and Destiny...