BABI NA TALATIN DA BAKWAI

443 113 10
                                    

BABI NA TALATIN DA BAKWAI
Kallon juna suka yi da Innayoh, kowacce fuskar ta dauke da murmushi. Shi kan sa yanayin sakewar shi zai saka ka fahimci yana cikin yanayi na musamman, amma ba wai akwai murmushi bane kawai fuskar ce a sake ba kamar dazun ba, Wani sirrintacciyar murmushi ne, wanda sai ka nutsu zaka fahimci cewa yana yi, juya musu baya tayi tana kallon yanayin garin, tare da sauraron hiran da suke.
"Uban gidana, ai da ka fada tuntuni da mun san abin yi amma kayi ta boye mana" mika mata kofin yayi yana kallon kasa, a ranta ta ce.
*Lamido kenan maganar ma sai ka nuna mata mulki*
Shiru yayi kamar baya wurin yana kallon Mahaifiyar su, kafin ya mike bai ce musu cikin ku ba, abin sai da ya bawa Fulani Aminatu dariya.
"Innayoh wai yaushe zai dana jin nauyina?"
"Zai daina mana Insha Allah lokacin yana zuwa"
Kallon hanyar da ya bi ta juya wurin Innayoh ta ce mata.
"Na tausayawa matar da zata zauna da shi."
"Sabida bai nuna miki boyayyen halin shi ba, amma babu wani mugun abu a halin shi, asalima haka shine me kyau, duk inda zaka zauna ka nunawa mutane kai din na musamman ne, amma ba ka zauna duniya su goranta maka ba"
"Toh Innayoh" ta fada tana Murmushi dan ta san halin Innayoh,
Sauya kayan shi yayi ya fito daga cikin gidan, sannan ya fita wajen masarautan anan ya hango Gidado dasu Fulani Bintu suna ta yawo, bai bi ta kansu ba yayi ficewar shi daga masarautan.
A bakin kofa aka bashi kayan farautar shi ya nufi daji, idan yana jin nishada a rayuwar shi daji yake nufa yayi farautar, yana saka shi jin wani irin yanayi na musamman.
**
M. Gobir
A fusace ta kalle su, a daidai lokacin da Barkindo yake son shiga babban zauren.
"Taya haka zai faru? A ce ku kasa kamo mace daya a cikin rugar tsoron ta kuke ji? Matar nan na mata alamar da ba zata iya guduwa ba. Kuma da kun tafi akan lokaci taya zata gudu ku fita ku bani wuri"
Shiga yayi yana kallon ta, idanun shi jajjur.
"Me yasa kike tunanin zaki iya sakawa a cutar da ita," ya tambaye ta.
Wani mugun kallo ta mishi tare da tsuke fuska babu alamar wasa ta ce mishi.
"Ka b'ace min da gani" yadda ta daka mishi tsawa, yasa shi da baya tare da barin kofar da sauri duk rashin hankalin shi yasan halin ta idan ranta ya b'aci bata mishi na wasa, dan haka ya juya tare da komawa dakin shi. Yana barin wurin ta kalli Mandiya ta ce mata.
"Ki nimo min waziri maza"
"An gama Uwargijiya ta, baya goya marayu giwa me tafiyar kasaita" sannan ta fita, can ba da jimawa ba, sai gasu tare.
Da sallama suka shiga babban zauren tana zaune ranta a jagule.
"Wai kina da nima na?"
Kura mishi ido tayi na wani lokaci, kafin ta zuba mishi ido.
"Haka ne" daga haka ta mai da hankali kan abinda ta ke yi.
"Ina da abu me muhimmanci ina son tafiya"
Ya gaya mata.
"Tun da kana da abu me muhimmanci ka tafi, zamu yi magana amma karka manta da Haima" da sauri ya d'ago kai yana kallon ta.
Murmushi tayi tana wasa da warwaron hannunta.
"Ita da uwarta da take jin kanta ita wata ne ba, duk matan masarautan nan girmama ni suke amma matar ka ko hmm" ta fada tana kallon shi.
"Ranki shi dade me kike bukata!" Ya fada yana matse hannun shi.
"Yawwa dan gari ina so a saka idanu a duk motsin Barkindo, kafin ya zama sarki haka ba zai samu ba, sai da taimakon ka. Idan wani abu ta faru Bana tunanin zan iya yafewa"

Tana gama fadar haka ta juya tare da barin wurin, shi kan sa kamar an fara shi a wurin, jin jikin shi yana rawa, ba zata iya yafewa ba akan waye? Akan Yar shi mana, idanun shi sun cika da kwalla, baki daya ya rasa yadda zai yi da Bingel kai ko kashe ta yayi bai huce daga bakin cikin ta ba, mata sai ka ce jikanyar shaidan.
""
A can dakin shi sintiri yake,
Yake yana nazarin yadda zai fita wato ya nufi rugar nan da suka dawo daga can, yasan anyi rasuwa amma baki daya bai san me ya faru ba, dan taki yarda ya fita waje ta ce bai saba ganin mutuwa ba, kar ya gani ya razana. Haka yayi ta nazarin abinda zai yi.
*
Sokkoto.
Ba laifi tafiyar bata wani tsawo, amma kuma tafi zaman da yake, amma kuma yana samun kulawa daga wurin Inna Marwa da Yaranta, haka kuma Galadima da Sarkin Gida suna bashi kulawa, sai dai zuciyar shi ta kasa kwanciyar hankali domin kullum da Minani yake kwana yake tashi har yanayin yake hasasowa a idanun shi, na yadda ta kara girma ta zama babbar mace.
Sai dai idan ya tuna da haka zai ta shi zana hotonta, dan dama ya fara haka tun daga masarautan su, dan haka ba sabon abu bane a wurin shi.
Bude yar karamar akwatin shi nan yayi ha ciro wata yar karamar jaka, wacce duk fadin ta bata wuce tafin hannun shi ba,ya ciro jigidar ta, yana kallon su yana murmushi. Irin wannan yanayin, idan ya tuna yana kara saka shi kamar ya fita ya bazama duniya niman ta, kamar yayi ta yawo kasa zuwa kasa nahiya zuwa nahiya lardi zuwa lardi kusufa kusufa.
Tabbas zai nimo ta, matukar tana raye sai ya binciko a duk inda take a fadin duniya.
*
Kasancewar mako guda aka bashi domin shiryawa, fitowa yayi cikin shigar yaki, kamar sauran mayaka. Gwanin ban sha'awa idan ka gan shi, amma kamilalliyar fuskar shi da bata da yawan fara'a ta nuna tsagwaron jarumtar shi da kamalar shi, da fari ganin shi yasaka baki daya dakarun fashewa da dariya, kasancewar shine yaro matashi a cikin su, isowar shi da shigar shi hadi da kwarjinin shi wanda ya fidda sirrintacciyar ikon shi da nasabar shi yasa duk suka sunkuyar da kan su, zuwa yayi ya tsaya a jerin gwano, Gidado ba gefe can yana rubutu, tare da kallon shi yana dariya.
Farko a rayuwar shi da yaga wanda ya dace dabi'ar kanshi, kamar Hassan din shi. Suna tawowa yake tambayar mishi.
"Kana ta shirin yaki baka shirin komawa gobir ne?" Tunda ta kalle shi sau daya bai kuma kallon shi ba, dafa kafadar shi yayi yana mishi alama da hannun.
"Malam ka saurare ni, dole mu koma domin niman hakkin Ammyn, sannan idan bata koma ba haka yana nufin ta gudu bata koma ba, nazarci abinda nake gaya maka idan har zaka shiga yaki domin kare wasu al'ummar me yasa ba zamu kare martabar mu ba, daga ni har kai sunan Shegu shine tambarin mu, ita kuma Ammyn fa? Ka duba makomar ta" daga haka ya juya gindin bishi ya zauna, yana kallon shi shi kan sa Lamido ya jima a tsaye kafin ya nufi wurin taron, wani ikon Allah sarkin yaki ya zuwa ya mika mishi tutar borno, a duk tafiyar yaƙin da za ayi matukar aks baka tuta yana nufin kai ne mataimakin shugaban rundunar yakin kenan. Abinda ya faru dayawan dattawan da suka jima sun ji haushinsa kuwa, abin bai dame shi ba, haka da sarkin yaki yayi yana nufin koda ta Allah zata faru da shi toh na gaba shine Lamido. Shine mataimakin shi, kuma haka ba karamin al'amari bane asha'anin yaki, duk wanda aka bashi mataimakin toh ana nufin ko Meye shi zai jagoranci rundunar, su kuma basu san da haka ba, taya zaa zabi wanda ba kabilar su ba, a bashi shugabancin rundunar yakin su.
Haka ya haifar da gulma da tsegumi, yayinda shi kuma Sarkin yaki ta bada haka ne dan ta nanne zasu cimma burin su na maida su masarautan su, idan har ya iya tsayawa a matsayin mataimakin shugaban rundunar toh tabbas zai iya da mayakan gobir. Sauran dabara kuma tana hannun duk wani me ƙoƙarin ganin ya kwato hakkin Bello wannan shine makasudin bashi tutar. Kuma hallo dai idan suka yi nasara dole shi zai kafa tutar a sasansanin abokan yaƙin. Yin haka kuwa itace ribar tura shi matsayin da yake.
Haka suka bar masarautan, zuciyar shi ta tafi ga yaki.

A wannan lokacin wasu daga cikin rundunar su, suka kullawa kan su sharrin idan aka samu nasara toh a warware idan kuma aka fadi....
*Kuyi hakuri na gaya muku gaskiya ina da abubuwa dayawa a gabana yau din ma kawai kar na barku haka ne yasa na muku kaɗan sai tambaya ake ana jira labarin Kallabi ban yi rabi ba, idan nace zan yi gudu dayawa kuma labarin can make sense*
_zan yi Amfani da wannan damar domin na tallata muku sabon littafina me suna ZAYN MALIK 300₦ne zai zo Insha Allah 1/7/..._
#Mai_Dambu

KALLABI..! A tsakanin Rawuna...Where stories live. Discover now