*<Babi Na Uku>*
~Masu azancin harshe sukan ce dakan d'aka shikar d'aka....masana harshe kuwa suka karasa azancin da da tankad'en bakin gado.... Inji Masana harshen Hausa~
Wannan haka yake domin sarakunan baya suna daukar ɗiyoyin su mata masu daraja su hawa wata masarautan, ba dan kome ba sai dan kulla alaka me kyau, sake raya zumuncin su.
Ko nace masarautan buba Yero! Masarautar ce da Fulani suka kafata,karkashin jagorancin Mujaddadi Shehu Usmanu danfodiyo, inda ya turo wakilin shi Muhammad Kwairanga. Ita kanta Gombe an samo ta ne daga wasu kabilun.
Tarihi ya nuna a karni na 13 aka fara sanin garin Gombe, sai dai kafin wannan lokaci an yi wadansu mutane masu karama da sarauta da ake kira ‘Soninke Mandigos’, wadannan mutane su ne suka samar da tsatson garin Gombe, kuma littafin ‘Tarekh-el- Sudan’ (Tarihin Kasar Bakake) na musu lakabi da ‘Fararen Shugabanni’.Wadannan mutane ana kuma kiransu da ‘Kaya- Manga’. Sun mulki yammacin Sudan na wasu karnoni da dama. A cikin Kaya-Manga an samu wani mutum da ake kira Bin-Kaya Mob, wanda sarki ne a wata masarauta da ake kira Mande, a yammacin Sudan din, wanda kuma wannan sarki ya ci zamaninsa a cikin karni na 10.
Sarki Bin-Kaya Mob yana matukar ji da jikansa Bin-Abubakar, wanda har ta kai ko kuda ba ya so ya taba shi. Ya mayar da shi dan lelensa kuma shafaffe da mansa. Hakan ce ta sanya Kaya Mob ya bai wa jikansa wani bangare na masarautar tasa da ake kira Ukuba. Bin-Abubakar kaka ne ga Aliyu Ukuba, wanda shi kuma yake mahaifi ga Usman. Aliyu Ukuba shahararren malami ne, ya haddace Alkur’ani, wanda daga baya aka hada shi aure da ’yar gidan wani attajiri a garin Tibati, inda kuma suka haifi Usman. Zuri'ar Usman ta rayu na wasu tsawon karnoni har zuwa lokacin da suka tashi daga yankin gombe.
A cikin shekarar 1913 Hedikwatar Gombe ta tashi daga garin
Gombe zuwa Nafada, wanda a cewar Nasarawa Nafada ta fi
saukin zuwa daga manyan garuruwan Arewa irin su Kano da
Bauci da Maiduguri da sauransu. Har ila yau a wannan shekarar
aka girke sojoji masu lura da shige-da- fice a kan iyaka. Sarkin
Gombe Umaru ya halarci wani hawan daba da aka yi a Kano,
lokacin da sarki Edward na III ya kawo ziyara Kano. Bayan sarki
Umaru ya dawo daga Kano ne, ya sake zabar wani
gari da ake kira Doma karkashin Akko. Inda a shekarar 1919 aka
sake rada wa garin suna Gombe-Doma.
A kuma wannan shekarar ce aka mayar da Gombe- Doma zuwa
masarautar Bauci, sannan aka rage mata dagatai zuwa 3, wanda
a da take da 13. Daga nan kuma sai aka dawo garin Gombe.... Takaitaccen tarihin masarautar Gombe.
__________________________________
Masarautan GombeKallon Kanin shi jibril wanda suke kira Babayo, yayi cikin nutsuwa sanna ya ce mishi.
"Jibril ina ganin kamar ba zasu amshi tayin ba?" Shiru yayi kafin ya sunkuyar da kan shi cikin ladabi da biyayya.
"Hamma Shehu, babu inda ba zasu so tayin ka ba, sabida Fulani Aminatu tana da nagarta, kuma kai ma nagartaccen mutum me, sannan idan yadda ka hango ne, Sarki Bello ya dace da Fulani Aminatu, kuma idan kayi nazari a da tarihin shi yana daga cikin sarakunar gobir da suke kin tashin hankali ba laifi bane idan aka bashi tunda har aka yi nad'in sarautar babu wanda yayi yunkurin bashi mace. Haka yana nufin cewa sun gaji da bawa mazan masarautar mata ne sabida.."Shiru yayi yana kallon kasa, gyara zama Mai martaba Sarkin Gombe ya ce.
"Babayo kana hidima da Aminatu domin Buba ne ko kawai dan ni ne?" Haɗe hannun shi yayi cikin tsannanin tsoron da tashin hankali kan shi sunkuye ya ce.
"Ina yi ne dan Fulani Amrah" d'ago kai Mai Martaba Sarkin Gombe yayi ya kura mishi ido. Sannan Babayo ya cigaba da cewa.
"Nayi mata alkawarin tsayawa Aminatu, bakwai dan Abubakar yana son ta ba, sai dai muna duba Gombe mu ne kafin mu zartar da hukunci. Sannan idan na duba ita kanta kafin ta san Meye soyayyar ya dace a fitar da ita daga cikin masarautan yanzun take da shekaru goma sha biyu. Daidai ta tashi a hannun mijinta. Sannan haka zai saka ta taso da soyayyar mijin ta da kuma sanin sha'anin mulki."
YOU ARE READING
KALLABI..! A tsakanin Rawuna...
HistoryczneThe gap between Love and Hate is not the same as the gap between Death and Life ... But to be killed or to win is one thing ... you are nothing .. in terms of Drawing Fate .. To die or not to live must be shared on two things ... Love and Destiny...