BABI NA HAMSIN DA BIYU
___________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
___________Bude idanu shi yayi gaban shi yana tsannanta faduwa, a hankali ya mike yana kallon Gidado da yake ta barcin shi hankali kwance, zama yayi sosai ya tankwashe kafar shi yana kallon yadda dan uwan shi yake ta barci, baki daya ya shiga zulumi.
Tasowa yayi zuwa wurin kwanciyar Gidado ya kwanta a gefen shi, tare da karanta wasikar jiki.
**
Kallon Mahaifiyar ta tayi da take zuba mata man shanu a cikin tuwon dawa miyar kubewa, sai tashin kamshi yake.
"Inna don Allah kiyi hakuri!" Ta fada cikin matsanancin kuka.
"Haima na gaya miki ba yau ba, ki fita idona ki daina kai kanki wurin Bingel, amma baki ji ki fita hanyar Barkindo"
"Inna naji ba zan kuma ba"
Shigowa Waziri Zakaria yayi yana kallon su, bai ce musu ƙalla ba ya wuce abin shi, tashi Maman Haima tayi ta nufi dakin shi.
Zama yayi ya zabga tagumi yana nazarin yadda kome yake kara lalacewa.
"Sannun me gida"
"Yawwa! Me kuma Haima tayi?"
"Kawai bata jin magana ne bana son tana shigewa Barkindo ne tunda uwar shi bata son ganin ta."
"Toh Allah ya kyauta karki raba musu zumunci, ki bar su haka ko bata je ba shi zai zo ai"
"Hm ya batun Hamza daga masarautan Fika?"
Shiru yayi kafin ya ce mata.
"Bingel ta ce a dakatar da shi, yaje a nime shi."
Kikewa Maman Haima tayi zuciyar ta a tafashe.
Zata d'aga murya ya ce mata.
"Kin ga wuce can bana son ciwon kai" ya fada yana nuna mata hanya, fuu ta bar mishi dakin, aikuwa ya dafe kan shi domin wallahi ya rasa inda zai tsuma ran shi ya huta da fitinar bingel ya gaji wallahi kamar shima ya gudu dan ta addabi rayuwa shi.
-
A cikin gidan kuwa tun da Barkindo ya dawo bai kuma gigin fita ba, amma hankalin shi yana wurin Anum. Baki daya ya daina kula Bingel kamar xaya yi hauka, rarrashin duniyan nan babu wanda baya tayi ba, amma fir yaki kula.
**
Zaune yake a gaban bokan wanda yake watsa abu a cikin ruwan wutan gaban shi, bude ido yayi ya kalli Yakubu.
"Kana zaton cewa zaka yi dace na gamon abinda kake bukata?" Ya fada yana kara rintsa idanun shi. Kafin ya bude tarr yana kallon cikin ruwan wutan yana murmushi ya ce mishi.
"Ka cire ranka babu nasara, domin ita din sai namijin duniya.""Mulkina fa?"
"Cike yake da zubda jini! Ita ba zata kara maka kome ba sai zubda jini, dama ace zaka iya tankwara ne ba mamaki kayi nasara."
"Taya zan gane ta ina bukatar ta domin mulkina"
"Yakubu ba zaka yi nasara ba, sai dai da ace kana da d'a ne tabbas zai yi nasara""Ka dai duba boka zan yi nasara naji haka a jikina, da wacce alama zan gane ta?" Yayi tambayar cikin kafiya da mugun naci.
Zane yayi kafin ya kuma kallon shi.
"Ka jima da haduwa da ita, sai dai ka cigaba da niman ta, ka aure ta idan ka same ta kazo nan sai mu san yadda zamu yi a nima maka yadda za a hana yanayin ta tasiri.
Gyada kai yayi sannan ya ajiye mishi wata jakar fata me ɗauke da silalar zinari.
Har ya mike zai bar bokar ya ce masa.
"Akwai wani a cikin gidan ku, yana kokarin ganin ya taimaka an ture mulkin ka, ka dakatar da numfashin sa. Yana nan shi yake jan ragamar wasu abubuwan kawo kunnen ka!"
Sai da ya gaya mishi wanda zai kashe.
"Karka yarda ka bar wani wanda zai baka damar rasa ta, mutane dayawa suna niman shigowa a cikin su kuwa har da Tsohon sarki da ahalin shi, amma akwai mutanen da suke musu mubaya'a"
YOU ARE READING
KALLABI..! A tsakanin Rawuna...
Ficción históricaThe gap between Love and Hate is not the same as the gap between Death and Life ... But to be killed or to win is one thing ... you are nothing .. in terms of Drawing Fate .. To die or not to live must be shared on two things ... Love and Destiny...