*<BABI NA SHA BIYAR*
Wani jan numfashi take cikin tsananin tsoro da tashin hankali, idanun ta sun firfito waje, ta kuma damke damtsen shi ta fashe da wani irin kuka jikinta babu inda baya rawa, tsoron da take ji a bayyana a kan fuskar ta, ware idanu tayi tare da fashewa da kuka tana ture shi.
"Baffa'm don Allah kayi hakuri, Wayyo Allah Innayoh, Wayyo Baffana. Hamma na kazo ka ceci ni"
Baki daya sarki Ballo ya rasa nutsuwar shi yar Kwailar shi ta gama rikita shi, ji yake duniyar kamar shi tafi kowa dace da wannan yanayin, shi yasa bai ji ta ba, bai kuma ji me take cewa ba, ya rintsa idanun shi tare da toshe kunnen shi yayi ta kwasar baiwar da Allah yayi mata tare da cin alwashin babu abinda zai isa raba su. Bai tab'a sanin cewa haka aure yake ba, sai da ya nika yar mutane, yayi mata bulaliyar shi, bai san lokacin da ya dauka yana zungure ta ba, amma tabbas yayi fatan hakan ya kasance har gaban abada.**
*Birnin Sahel*
Wani irin uban ihu bokanya Tursi tayi tare da kutufal da halwar tsafinta wanda a kala zai kai kimanin shekaru dari da casa'in domin gadar dashi tayi a wurin kakanin ta, halwar ta mirgina ta faɗi kafin ta kuma tashi zaune, kasancewar aiki da suke da manyan ifiritai.
"Uwar gijiyata ƙaddara ba ta karya, Ƙarki manta bai zama dole sarki arkan ya samu Magaji ba, kuma kema kin san da haka" d'ago kai tayi ta kurawa turwa Idanu, kwalla na zuba mata sili-sili.
"Na rantse da toshe zuri'ata ba zan dauki faduwa ba, maza mu wuce fadar sarki Arkhan!"
"Ya shugabata a wannan gabbar akwai son rai! Nasarar da ta zo har gidan ka itace nasarar ka, amma ƙaddarar da zata dauke ka har zuwa wuni wurin sunan shi son zuciya. Matukar aka farmaki mutanen da basu ji ba babu gani ba, tabbas an kawo karshen Sahel ne, kuma kin san da haka, kuma kin fahimci haka ba kaddaran Arkhan bane haihuwa.""Turwa ya zan yi da sarki Arkhan? Tunda na tabbatar mishi da cewa wiwar haihuwar shi a wurin yarinyar yake?" Ta tambaya tana me zama dabas akan shimfidar da yake dakin.
Sunkuyar da kai Turwa tayi tana kallon kasa.
"Daga lokacin da kika tabbatar zaki iya yaki toh ina ji a jikina zaki yi nasara, amma da zaran na fara jin kamshin faduwa jikina yake bani ki dakatar da zuwa ga Arkhan domin..""Babu nasara ko? Domin dakarun da muka tura su ma basu da kwarin gwiwa ko turwa?" Ta tambaye ta.
Gyada kai tayi, tana me had'e hannun ta wuri guda tana matse shi. Takawa tayi gaban ta tana kallon yadda take tsaye.
"Turwa baki daya na kasa gane wacce irin halitta kike da ita na sunshino kaddaran wasu?" D'ago kai tayi, kafin ta sunkuyar da kanta tana me jin wani irin kaduwa, na tsoro kafin ta zube a gaban Tursi tana cewa.
"Ya shugabata ki gafarce ni"
***
*Masarautar Gobir*
A hankali ya janye tare da rubda cikin shi yana goga kan shi a kadadar Fulani Aminatu, baki daya ya rasa kuzarin shi. Ji yake kamar bai da cikakken lafiya domin baki daya da zuciyar shi yake bin al'amarin ta, ya kai wani lokaci a wurin kwance, amma sama-sama yake jin shashekar kukan ta. A sanyayye ya juya yana kallon ta, yadda ta dunkule samun kan shi yayi da kasa tabuka kome, yadda take jan kukan ta cikin yarinta yana kara fisgar zuciyar shi da imanin shi. Wani irin kaunarta da begen ta, suna kara samun mafaka a ruhin shi, baya jin akwai wani abu da ya kaita tasirantuwa ruhin shi kamar yadda take shashekar kuka. Cikin tsananin gajiya ya matsa bayan ta, sannan ya sakala hannun shi a K'ugunta, ya juyo da ita suna fuskartar juna.
"Kiyi shiru Kinji" ya fada mata yana me daura yatsar hannun shi a saman bakinta, idanun ta a rufe ta shiga gyada mishi kai.
Bakin shi ya kai habb'arta, ya sumbaci wurin a hankali, kafin ya janyota kirjin shi yana shafa bayan ta, kamar dama jira take ya janyota, ta shiga mishi wasu kananun rikici wanda ya haifar mata da zazzafar zazzaɓi a daren, abin gwanin ban tausayi.
Dakyar ya samu ya mike ya tsaftace jikin shi, ko kafin ya fito ya samu har ta koma barcin ta. Hakura yayi da wurin kwanciyar ya koma kasa ya kwanta a Kilishi da matashin sa.**
*Wayewar gari*
An tashi da wani sabon al'amari ne na farin ciki, wanda tun asubar farko ake buga tamburan masarautar wanda dama dabi'a ce ko ace al'adun masarauta ce, ana bugawa duk lokacin da Sarkin Gida ya samu labarin wani cigaba ya faru a masarautan, ko za'a tarbi mai Martaba daga dawowa a yaki,.ko an samu karuwa a cikin masarautan, ko sarki ya kwana da Amaryan shi da yake girmama al'amarin ta, toh tun asuban fari ya sanar da Sarkin gida a kira Innayoh, tana shiga turakar Mai Martaba, aka ji ta rangad'a gud'a tare da fitowa da sauri tayi ta rangad'a gud'a, wanda ya farka da wasu bayin sashin Fulani Aminatu, kafin kace me an shiga had'a gagarumin biki, kamar yau ake bikin Sarki Bello da Fulani Aminatu, biki me sunan buki, wanda Innayoh ita ta wanke Fulani Aminatu da madarar saniya da aka amso daga can gidan gonar masarautar
YOU ARE READING
KALLABI..! A tsakanin Rawuna...
HistoryczneThe gap between Love and Hate is not the same as the gap between Death and Life ... But to be killed or to win is one thing ... you are nothing .. in terms of Drawing Fate .. To die or not to live must be shared on two things ... Love and Destiny...