*<Babi Na sha hudu>*
*Rundunar dakarun kasar Sahil*
Yada zango suka yi aka shiga kafa tanti masu fita farauta sun tafi har aka gama can sai gasu dauke da gadda da barewa, suka zuba a hankali tare da kallon shugaban su, a take aka hada itacce tare da ciyayi, aka feɗe dabbobin aka bankare su sannan aka saka gwaf, aka shiga gasu su."Shugaba akwai tafiya wata goma sha biyar a har yanzu fa" inji wani badakare da yake tsaye, a gefen shi.
Shiru yayi yana zane a kasa kafin ya d'ago kai yana kallon shi.
"Lati bana tsammanin zamu samu nasarar dauko Yarinyar"
Zaro idanu Lati yayi yana kallon Shugaban shi. Kafin yayi kasa da kan shi.
"Ya shugabana! Ka kuma nazari akwai wani abu ne?" Lati ta fada yana kallon shi.
"Duk abinda na saka a gabana ban tab'a jin shakka ko tsoro ba, amma wannan karon yakin kamar ba nasara, dan haka zan tafi ne domin biyayya ba wai dan na samu nasara ba"
Cikin gamsuwa Lati ya gyada mishi kai yayi yana kallon shi kafin ya ce mishi.
"Toh ya zamu yi da sauran dakarun!" Mikewa yayi yana me d'aga labulen ta tantin.
"Ba zan so su rasa rayuwar su ba, ni daya zan tunkari yanki idan yi nasara ba sai ku juya" ya fada yana kallon lati da yayi shiru shima yana sauraron shi. Murmushi yayi sannan ya ce mishi.
"Karka damu lati zamu yi nasara amma ka sani tafiyar da zamu yi da komawar mu"
"Kawai ina tsoron abinda zai faru domin Sarkin Arkhan ba zai tab'a hakura da burin shi ba, kawai muje koda zamu mutu ne gara mutuwar mu ta isa gare shi da ace Mun koma babu yarinyar."
Shiru yayi yana nazari abinda lati ya fada yana kallon Shugaban su.
"Lokaci ne zai nuna haka, idan yayi toh zabe yana gare mu ko mu juya ko mu tsaya a kashe mu amma tabbas masarautar da zamu tunkara ba karamar masarauta bace da zamu iya murkushe ta a lokaci guda, masarauta ce me cikin gashin kanta, idan har muna son galaba akan su dole sai mun tsaya ka'in da na'in mu yake su ba dare ba rana"
"Na gamsu da bayanin ka. Amma karka manta idan har muna son muci galaba akan masarautan sai mun samu hadin kan wasu babu wata alkaryar da za a ginata babu kalubale, imma na kishi ko na hasadda shine kawai zai bamu damar fahimtar haka."
**
*Shashin Ajuji*
"Allah ya baki nasara uwar Sarkin goben, takawarki lafiya gaba salama baya salama. Na samu labarin Mai Martaba ya tafi kilisa da Fulani Aminatu" cak ta tsaya daga taunar soyayyen naman da take ta ajiye shi, sannan ta kalli Jakadiya Rama.
"Ki kawo min lantana da Zulai" ta fadawa Jakadiya.
"Allah ya baki nasara,an gama" ta fita tana fita ta harari kofar shashin Ajuji, tsabar jin Haushin sannan ta fita zuwa can wurin bayin ta sami Innayoh da Sarkin Gida.
"Sarkin gida ya gaya min yanayin da kuke ciki,sannan insha Allah zamu duba, kuma za a tura kome wurin mai Martaba ko za a gyara shashin ku baki daya"
"Hahhhhh" suka ji dariyar Jakadiya Rama tana faɗin.
"Ki tsaya daga inda kike nan mallakar matan tsohon sarki ne! Kuma masu fatan sake samun sabon Sarki nan gaba" murmushi Innayoh tayi sannan ta ce mata.
"Sarki goma zamani goma, duk sarkin da yazo da nashi tsarin mulkin wannan tsarin sarki Bello. Ki iya harshen ki kar bakin ki ta janyo miki magana"
"Innayoh meye nufin ki?" Inji Jakadiya Rama,
Murmushi Innayoh tayi sannan ta kalli bayin sannan ta ce musu.
"Daga yau za a gina babban madafin girki, a shashin Fulani Aminatu daga yau abincin ku na safe da na rana da na dare zai fito daga can. "
"Godiya muke, a mika mana sakon godiya ga Fulani Aminatu"
Har ta juya zata tafi ta ce musu.
"Sarkin gida zai duba abinda kuke bukata, ka kawo min kome a rubuce yadda xan bawa Fulani Aminatu ta mika ga Mai Martaba kasan gobe laraba."
"Insha Allah" ya fada yana me take mata baya. Shan gabanta Jakadiya Rama tayi tana faɗin.
"Ke kin zata zamu amshi wannan lamari ne? Baki isa ba, nice Jakadiyar masarautar Gobir tun iyaye da kakanni, sai na hana ki motsi" murmushi Innayoh tayi tana me nade hannun ta,tana faɗin.
"Karki damu, nasan darajar farin gashi bana son wata rana a min haka. Jakadiya ko Mai Martaba bai gaya miki ba ai ya kamata ki fahimta." Wani irin zaro idanu tayi tana me kai hannun ta zata shake wuyar Innayoh. Da sauri sarkin gida ya shiga tsakanin.
"Jakadiya ki rike matsayin ki, ƙarki yi abinda zai saka mai Martaba ya Kore ki a masarautan nan domin kowa yasa kananun magana da yake yawo kece kike fitar da shi da taimakon wasu munafukan kusa dake" shiru tayi tana kallon Innayoh jikinta baki daya rawa yake.
"Na rantse da Allah ba zan bar matsayina ba, akan me nice haifaffiyar masarautar Gobir taya."
"Muje Sarkin gida" suka wuce abin su, cikin tashin hankali Jakadiya ta nufi sashen Gambo ta zube a gaban ta.
"Uwar ɗakina ki min rai Mai Martaba ya nad'a Innayoh a sabuwar Jakadiyar shi, matsayin nan gadar shi nayi tun iyaye da kakanni yau daya a ture ni. Dariya duniya zata min" ta fada cikin matsanancin kuka da tashin hankali. Waziri Zakaria da yake zaune yana shan kindirmo, mara tsami domin zuwan Fulani Aminatu yasaka su koyan shan madara kindirmo da dai wasu abubuwan.
Ajiye ƙwaryan yayi sannan ya zuba mata ido.
"Jakadiya matsayin ki bai sauya ba, kina nan a Jakadiyar Ajuji da Yarimar Gobir, sai dai gamu da muka yi mubaya'a ga sarki Bello ba zamu dauke ki a matsayin Jakadiya ba, sai kiyi hakuri, abinda kike aikatawa kamata yayi a yanke miki hukuncin kisa, amma dake dattako yana jinin shi ya zab'i a barki ki rayu kawai bata shugaban bayi yayi kika firgita idan kuma ya bata Jakadiyar da? Wani lokaci muna son abu muke hakura da shi. Amma kin kasa gane haka shi yana wurin ne ba dan ran shi naso ba, ku kuma kun dauka yana zaune ne domin yana jin dadin rayuwar shi. Haka ya tsara mulkin shi bai san izza ds d'agawa. " Daga haka ya mike ya fita a dakin.
YOU ARE READING
KALLABI..! A tsakanin Rawuna...
Ficción históricaThe gap between Love and Hate is not the same as the gap between Death and Life ... But to be killed or to win is one thing ... you are nothing .. in terms of Drawing Fate .. To die or not to live must be shared on two things ... Love and Destiny...