BABI NA SABA'IN DA UKU
Bai kai zauren farko ba, yaji an yi sama da shi tare da rufe mishi kai, akayi wani hanya da shi, a yadda ake tafiyar bai nuna musu wani abu ba, haka suka wuce da shi har gidan Chiroma.
Suna kai shi aka ajiye shi a kujera sannan suka cire abin kan shi. Hango Chiroma yayi a hankali ya zube akan gwiwar shi,
"Na tuba na bi Allah na bika, wallahi duk abinda kace shi zan bi"
Dariya yayi yana kallon shi tare da cewa.
"Don Allah dube shi sabida hakuri da biyayyar shi, Matashin da ya dace ya zama Sarki yau shine a gaba na, tashi d'anan,ka saka a ranka ni nan zan dawo maka da mukamin ka"
Girgiza kai yayi cikin kwantar da hankali ya ce.
"Gadon hari sau fanna ramin kura sai y'ay'an ta, bige sai bige babban goro sai magogin karfe, Daka yau adaka gobe dai mai gaskiya, Kainuwa dashen Allah, Giwa me tafiyar kasaita, birnin da babu kai ba birni bane hankaka me da dan wani naka. Me zance? Ai wannan wurin na jarumai ne, ni da takobin ma tsoron shi nake ji, Baba Chiroma wurin can bana Yara bane ya zaka ji idan aka ce kai ne a wurin mulki sai jarumi masani wanda yaga jiya ya ga yau, aka jima ana bugawa da shi. Amma ka gafarce ni idan nayi wauta"
Kallon juna suka yi su uku, wato tun cire mishi abin fuskar shi ya gane akwai Sarkin gida a cikin su, sai Yakubu.
"Kun ji me yace?" Chiroma ya tambaye su.
"Eh Chiroma amma kai Husaini me yasa baka son mulki?"
"Tun ina Yaro marubuci ne ni, idan nace zan yi mulkin ba zan iya ba, sannan shi kuma Hassan mayaki ne" Yakubu ya tambaye shi.
"Toh yanzu ta wani hanya zaka taimake.mu?"
"Baba Chiroma ina tare da ku, kuma zan tsaya muku a kowani fuska, sai dai ina tsoron cin amana domin Yaya waziri ya kira ni yanzu "
"Jeka zamu yi nazari babu wanda ya isa cin amanar ka, yadda kake da hankalin nan"
"Nagode "sannan ya bar su nan suna musu,akan abinda ya gaya shawaran da ya gaya musu, sannan ya. Nufi gidan Waziri. Cikin kunya da girmamawa ya zauna tare da cewa.
"Barka da hutawa Yaya Waziri."
"Ni ba zaka ce min Baba Waziri bane kamar yadda dan uwanka yake gaya min" hàdiye yawu yayi sannan ya ce mishi.
"Allah ya huci zuciyar ka Baba Waziri"
Murmushi yayi sannan ya ce mishi.
"Dama na kiraka ne muci abinci da kuma tsarin mulkin zamu tattauna akai."
"Toh gashi ni a koshe nake,yanzun naci abinci a wurin Haimah " d'ago kai yayi tare da murmusa mishi.
"Ya take?"
"Tana lafiya "
"Da fatan bata maka zancen shirme ba?" Ya tambayi Gidado,
"A'a Baba Waziri"
"Toh muci mana, ban tab'a ganin mutumin da bai da mu da mulki irin ka ba, naso kwarai da Lamido yayi dogon zamani, muga irin tashi mulkin, ga wasu abubuwan da nake son a ce da ya ciki-cika."
"Allah sarki dan uwana, haka Allah ya nufa, me kake so ya ciki-cika?"
Jim yayi sannan ya ce mishi.
"Manta kawai, mu ci mana " babu musu ya fara tab'awa yana gyada kai, kallon juna suka yi kafin Waziri ya ce mishi.
"Sam baka sha'awan mulki ne?"
"Haba ina me zan yi da shi a matsayina na Galadima ya iso ma, sai dai Baba Waziri ina ganin daga amsar damar aiki naga kamar ana yawan tab'a kayan Baitul Mali amma kayi hakuri kar haka ya zama babban damuwa xan gayawa mai Martaba a shawo kan abin"
"Ikon Allah kaji kwazo, har ka gane haka? Toh yanzu ya za ayi domin bana son ka gayawa Mai Martaba ni na dace da sanin kome "
"Idan da hali duk wani abinda yake shigowa ta hannun mutane ya koma hannun ka, sannan zai zama karfin da kake samu ya zarce na kowa daga lokacin da dukiyar Baitul Mali ya shiga hannunka, ni ina gefenka ga sarki a gefen ka kana tsammani masarautar da mulkin ba zata koma taka Ba ce?"
Cikin tsannanin mamaki yake kallon Gidado, tunda yake bin bokaye da malamai babu wanda y gaya mishi zai iya mallakar kowa sai Gidado.
Dariya yayi sannan.ya ce mishi.
"Anya wannan shawara ne?"
"Ka zuba idanu xaka ga dalilina na cewa haka "
Sun jima suna hira bai yarda ya kawo mishi hiran Chiroma ba, har suka gama ya tafi.
Sai da ya shiga cikin gida ya samu Baffa'm,.yana dakin nazarin Lamido.
Suna nazarin wasu abubuwan.
"Ya kome yake tafiya?"Baffa'm ya tambaye shi.
"Alhamdulillahi kome na tafiya dai-dai"
"Kana cusa kanka cikin hatsari fa!" Baffa'm ya gaya mishi.
"Baffa'm babu hatsari ku taya ni da addu'a kawai Allah ya cika min burina ranar da lamido zai cika kwana arba'in ranar kowa zai biya zunubin shi"
"Meye shirin ka?"
"Yana dayawa tsare tsare na!"
"Shi kenan ka duba Anum taki cin Abinci sai Saraki yazo" tsigar jikin shine ya mike, ya tashi a hankali ya nufi hanyar cikin gidan, bin shi da Idanu Baffa'm yayi sam yanayin shi tafyyar shi.maganar shi bata tab'a nuna zallar bacin ran shi, kullum fuskar a sake take, amma shi din ruwan sanyi ne dafa mod'a.
A hankali ya shiga babban zauren inda suka sakata a gaba ta ci abinci, tana musu bori, zama yayi a gaban ta. Sannan ya wanke hannun shi da ruwan da yake cikin akushi.
"Ahaam" ya fada mata, bude baki tayi tana son yi kuka.
Sake cewa yayi Ahaam,
Ammyn ta mike zuwa ɗakinta, kuka take son yi amma ta kasa sai salati, wannan abun da yake yi lamido ne yake mishi lokacin suna yara idan yaki cin abinci.
A hankali kome yake dawo mata sabo, ta'aziyar da kuma abubuwan da tayi ta gani a mafarki,. Bata fasa kiran sunan Allah ba sai da taji zuciyar ta yayi sanyi sannan ta kwanta.
A waje kuwa abinci ya bata yana gamawa, ya kalli Innayoh sannan ya ce mata.
"Ki kula da ita zan tafi na kwanta" ya mike tare da barin sashin, ai kuwa ta saka kuka zata bi saraki ne. Dakyar suka rarrasheta amma kamar wacce ake kara mata kuka, har Innayoh ta kaita dakin tare da taimakon iyayen ta.
Yana shiga sashinsa wanka yayi sannan ya nufi dakin Bintu da take barci, hawa gadon yayi ya janyota jikin shi.
Ajiyar zuciya ta sauke ajiyar zuciya, juyata yayi suna kallon juna,gyara mata kwanciya yayi a jikin shi barci yayi gaba da ita.
**
Washi gari bayan sun fito sallah asuba, suna tafiya da Barkindo.
"Yaya Barkindo! Ina son ka saka idanu da mutanen da sune zagaye da kai,"
Cike da mamaki yake kallon shi domin kusan abinda ya gayawa Lamido kenan wancan lokacin, bai kula shi ba.
"Ban gane ba?" Ya kuma tambayar shi.
"A'a kawai dai ka saka idanu akan kowa"
Daga haka yayi tafiyar shi, bai kuma bin ta kan Barkindo ba, a hankali Allah da ikon shi ya toshe musu basirar su, sannan ya kuma bawa Gidado damar shiga cikin su a cikin kwanaki biyar kacal, kamar yadda suka cutar da su, sai gashi yadda ya shiga jikin su da barnan da yake musu Allah kadai ya sani.
Ya cika zuciyar Waziri da son abin duniya, sannan ya haɗa shi manyan mutanen fada, rikici a hankali suka fara darewa a jikin Waziri suna komawa jikin Chiroma, a nan jikin Wazirin kuma ya cigaba da zama yadda yake abun shi ba zaka tab'a kawowa zaka iya saka mishi hannu a baki har ya ciza ba, sai dai kawai da ya tashi ya haɗa Waxiri da BARKINDO. Inda yayi tawa BARKINDO hannunka me sanda a yadda yake tare da waziri yayi a hankali da shi, ranar wata Laraba ana fadanci dama tun jiya talata Gidado ya gaya mishi abinda waziri yayi na rubda ciki akan dukiyar masarautar.
"Don Allah ka rufa min asiri kar ka cutar dani idan na gaya maka gaskiya yanzu haka ana shirya kashe ka, Chiroma da sauran mutanen fada idan baka sauke rawanin Waziri ba, don Allah kar ka gayawa kowa"
"Insha Allah ba zan fada ba"
Ana zaman fadan kuwa barkindo ya kalli waziri ya ce mishi.
"Ma'aji ya gaya min ka amshi kome na Baitul Mali ka dawo da shi,"
"Eh na amsa domin barnan dukiyar ake haka kawai tunda bikin yar shima sa dukiya al'umma yayi hidimar".
"Waye ya baka izinin amsa?"
"Ya kake min magana kamar dan ka ko sa'anka?" Waziri ya tambayi Barkindo. Cikin fushi Barkindo ya daka mishi tsawa.
"Gaya min waye ya baka izinin taɓa dukiyar Al'umma? Ku cire rawanin shi daga an Kore shi na dakatar da shi ba, kuma dawo da kome da ya tab'a idan ba haka ba ku wulakanta shi "
"Ka san waye Ni kake tozartawa? Ka san waye yake tsaye a gefen ka ba dan ni ba waye zai yarda da Lusari irin ka"
Ran Barkindo ya gama ɓaci san haka yasa aka fitar da shi daga cikin fadar, murmushi Gidado yayi, sannan ya shiga bawa Barkindo hakuri tare da cewa ya kula domin xa a iya kashe shi.Bayan an tashi fada, ya fita Inda Sarkin gida yake ya Kalle shi.
"Kace zaka iua bada rayuwar ka domin fadar gaskiya? " Gidado ya tambayi Sarkin gida.
"Eh na fadi haka "
"Yau ku kaiwa barkindo hari bayan sallah isha, sannan ku tabbatar da Waziri ne ya aiko ku"
"An gama ranka shi dade, ya batun Chiroma?"
"Kowa zai biya abin ya shuka jeka kawai "
A hankali ya juya abin shi, kowani me hannu a cikin masarautar sai ya biya zunubin da yayi da hannun shi, kowani me ruwa da tsaki sai ya fanshe abinda ya biya da hannun shi, ranar da Lamido zai cika kwana arba'in su kuma zasu biyo shi da zunubin su.
Shi yasa ya zama wawa a tsakanin su,ya hana kan shi magana akan mulki ya hana kan shi fushi akan.kome ya ke mu'amalar su kamar ya yafe musu kamar ya manta da jinin biyun shi.
Shi yasa yake ganin Anum a cikin laluran xaucewar tunanji,yake dauke kai kamar bai damu ba, shi yasa ya jingine Haimah kamar bai damu da abinda uban ta yayi mishi ba, yaki gayawa Baffa'm kome ne, kamar yadda galadima ya ce yabi kadin kome a sannu yana bin su, tsarin kome yana ajiye a kan shi tun ranar da Lamido yace idan ya samu lokaci su tsara yadda zasu karkabe. mugun iri, shi da kan shi ya rubutawa Lamido yadda za ayi kome amma bai kawo a ran shi lamidon ne zai tafi ya bar shi ba,
A ranar da Sarkin Gida ya dawo abinda ya gaya mishi cewa yayi zaka yi aiki domin fadar gaskiya amma da sharadi, sai ka gaya min me yasa ja tsani Baffa'm?
Sunkuyar da kai yayi cikin takaici da kunya ya ce mishi.
"Sabida Amunatu! Ina son Aminatu, ina son matar Abokina, ni na hanata daukar cikin Mahaifin ku, domin duk lokacin da zai kasance da ita Ni nake zuwa na amso abincin shi anan nake zuba musu garin maganin da zai hana ciki zama a jikin ta. Ni na kawo mutumin da aka ce kwarton ta ne, sannan na tsira da rayuwar shi ga shi nan, na ce ya kafe akan cikin na shi ne, ban san da wani ido zan kalli Bello ba, a farkon ganin ka da nayi jikina ya bani kai ne zaka iya kawo karshen mu, daga baya sai muka fahimci baka da amfani, koda akazo kashe ku ni nace kar su har ba maka kifiya me guba. Domin mulkin aka baka ba zaka iya ba, Tun farko naso kashe Baffa'm amma Allah bai nufa ba, muka bar shi a araye! Naso kwarai hakan sai ga lamido shi yaki yasani da ɗaukar fansa, bai san yadda zai shiga jikin kowa ba domin yasan za a iya cin amanar shi.
Shi yasa sai muka kara shiga jikin shi sannan muka kashe shi, Gidado ka yanke min hukuncin da ya dace..*Yau kam daya zaku samu bamu da wuta wallahi idan kuma mun samu wuta zaku ji ni! Wadanda suka biya Zayn Malik kuyi hakuri an kusan rufe Kallabi sai mu daura ko kafin kwanakin Zulhajj Insha Allah 😍❤️🥰🔥*
#Mai_Dambu
YOU ARE READING
KALLABI..! A tsakanin Rawuna...
Historical FictionThe gap between Love and Hate is not the same as the gap between Death and Life ... But to be killed or to win is one thing ... you are nothing .. in terms of Drawing Fate .. To die or not to live must be shared on two things ... Love and Destiny...