BABI NA HAMSIN CIF
___________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah.________________________
"Idan ka gama mafarkin ka na kullum sai kayi magana akwai wata bazawara a gefen mu ta yamma sai a mata magana ko" girgiza kai yayi domin ba sabon abu bane mafarkin shi, amma kuma yana da kyau ya bawa zuciyar shi hutu. Domin idan ya cigaba da haka zai samu matsala.
--
Sai da suka yi tafiya me nisa, kafin Sarkin gida ya ce mishi.
"Akwai rudaden mafarki mara tabbas, akwai boyayyen al'amari mara iyaka, akwai damar da zaka bincika me yasa ake bibiyar? Dama ne gare ka, na zama namiji ko kuma ka tabbatar a lusari har abada"
Kallon fuskar Sarkin gida yayi ran shi ya b'aci, amma kuma sai ya dauke kai kamar bai ji zafin maganar ba, asalima kamar bai damu ba, ya ce mishi.
"Zaka iya juyawa. Ka gayawa Baffa'm Nagode"
Ya kada dokin shi ya shige masarautan da gudu, murmushi sarkin gida yayi yana kara ji a ran shi Tabbas tarkon su ya kama kurciya.
**
Kano
Hannun shi a goye a bayan shi, Fulani Zainabu itama tana zaune a gefe sai Fulani Dijah da take ta dirzan kuka, kamar ranta zai fita.
"Ni kika watsawa kasa a idanu? Saboda wani sakarai can da na bashi kudi ya manta dake? Ni kika wulakanta kika wurge ni da takalmi a saman fuskanta? Na zata ko kare na kawo nace a zarga mishi igiyar ya zame miki ado dawa zaki Amince da shi ashe bakin ba haka ne, hasashena ne, lallai na yarda ka haifi mutum baka haifi halin shi ba, Abuh fita da ita bana son ganin fuskar ta."
"Abba kayi hakuri ba zan kuma, na shirya maka biyayya shima zan mishi biyayya"
Girgiza kai yayi yana faɗin.
"Ba zan kuma wannan kasadar ba, kije Allah ya miki albarka ba zan tab'a tirsassaki bin umarni na ba" sake rushewa tayi tana kuka, tana bashi hakuri amma fir yaki sauraron ta sai ma bata mishi rai da take yi.Babban tashin hankali shi guda daya ne bai san me Lamido zai gayawa Sarkin Borno ba.
Hankalin shi yayi mugun tashi, hmm bai san waye lamido ba, shi mutum ne da magana bata dame shi ba, balle har ya kai gaba, kuma matuka gaya ran Sarkin Kano ya b'aci dan haka ya zauna shi da wazarin shi, suka tattauna akan batun tare da alkawarin zasu tura dan sako ya tafi har can ya basu hakuri domin kuwa babu dad'i abinda Yar su tayi.
*
Tafiyar kwanaki biyu, yayi bai tsaya ba dan ran shi yayi mugun ɓaci sallah kawai yake tsayar da sho, sai da yaga ciwon shi yana zubda jini ne yasa shi yada zango, sannan ya gyara ko ina ya kafa tantin. Sanan yayo itacce, ya hura sallah kawai yake yi ya dawo ya zauna, dare na fara rabawa ya koma tanti shi ya kwanta.Bai jima ba Biyuna ya shigo cikin tantin ya kwanta a gefen shi, suka shiga barci. Domin ya gaji sosai dan haka ba tare da wani dogon abu ba, barci yayi gaba da shi.
**
Tafiya yake bai san inda yake jefa kafar shi ba, kawai yana tafiyar ne amma zuciyar shi a cunkushe yake, daga dan nesa ya hango wata mace zaune a kasar bishiya, tana mika mishi hannu,
Kafin ya isa gare ta, wasu abubuwan da ba zai ce gadu ba. Sun dabaibaye ta kafin jini ya wanke ta tun daga sama har kasa, gefen ta gawarwakin mutane ne.
YOU ARE READING
KALLABI..! A tsakanin Rawuna...
Historical FictionThe gap between Love and Hate is not the same as the gap between Death and Life ... But to be killed or to win is one thing ... you are nothing .. in terms of Drawing Fate .. To die or not to live must be shared on two things ... Love and Destiny...