BABI NA SABA'IN DA HUDU

405 101 17
                                    

BABI NA SABA'IN DA HUDU
ko zan samu sassauci a wurin Ubangijin mu na ci amana matuka gaya'
"Ba zan maka kome ba, ka je an yafe amma zaka biya laifin ka da wanke hannunka" inji Gidado,
A ranar da kyar yayi barci domin koran Bintu yayi a dakin shi baya son takura, kawai kan shi zafi yake mishi, me yasa ma bai mutu ba, ya bar Lamido da wannan tashin hankalin, zama yayi a tsakiyar gadon shi bayan sallah asuba, shigowa Bintu tayi, mika mata hannu yayi domin tun daren shi da ita na farko yau sati Daya kenan vai kuma niman ta ba,sai shiga dakin ya hargitsa mata lissafi amma baya niman wuce haka,
Hawa gadon tayi tana kallon shi, kafin ta ce mishi.
"Kayi hakuri na dame ka ko? Bana jin dadin yadda kake shiru shiru nan" janyo ta yayi tare da cire mayafin ta, kanshi ya kifa a kirjin ta, sannan ya shiga ya motsa ta kamar zai cinye ta.
Sai da ya birkita mata lissafin sannan ya samu nutsuwa, rungume ta yayi a kirjin shi yana shafa bayanta.
"Idan aka yi addu'ar arba'in zamu tafi borno ki ga iyayen ki zan barki anan na raka su Anum zuwa Somaliam"
Gyara kwanciyar ta tayi a jikin shi.
Kallon shi tayi sannan tace mishi.
"Amma Anum ba zata kuma dawowa ba ko?"
"Eh zata dawo kodan abin cikin ta" kasa tayi da kai bata kuma magana ba, haka kawai gaban ta yake yawan faduwa, tunda taji batun cikin Anum sai baki daya ta kasa samun nutsuwar,
Haka ya zare jikin shi yaje yayi wanka ya nufi fada, bai isa can ba aka ce mishi Baba waziri na kiran shi..
Nufar gidan waziri yayi, ya same shi kamar zai yi hauka, dan haka ya nufe shi.
"Me yasa kake haka?"
"Gidado ya ba zan yi ba, Chiroma ya juya min hankalin Barkindo, ban isa kome ba yanzun, tsoro nake ji karsu kashe shi "
"A ina zasu kashe shi? Idan kuwa haka ne ya kamata ka dakatar da su, daren yau, Wayyo don Allah kar ka yi amfani da abinda na gaya maka wallahi hankalina ne ya tashi shi yasa na sake baki "
"Ba sake baki bane shawara ne me kyau dole na kashe su da hannuna, jeka don Allah ka saka idanun ka akan shi kar wani abu ya same shi "
"An gama ranka shi dade," sannan ga fita hana jin kwalla na cika idanun shi. Su da aka tab'a su babu wanda yayi magana, sai shi da yake wurin kar a taba shi. A hanyar shi na wucewa ya hadu da Mandiya yasan ta da mugun son abin duniya, san haka ta cire silallar zinari ya mika mata a jaka, cikin murna ta zube sannan ya wuce itama zata yi nata aikin yau.
Yana shiga fada ya samu ana fadanci, zama yayi yana kallon dogaran fadar, ranar Litinin Lamido xai yi arba'in kafin wannan ranar yana son ta karkabe ko ina, dan haka ya gama karantar kowa a fadar matukar zaka bashi abin duniya zaka saye shi.
Bayan an tashi fada, da kan shi tayi ta turawa ana kiran dogarai yana basu kyaututtukan abubuwa masu kyau sannan ya ce musu.
"Marigayi lamido Hassan saura kwana uku ya cika kwanaki arba'in shine na raba sadaka daga cikin abinda na mallaka, nasan bai muku kome ba bai zalince ku ba don Allah ku mishi addu'a Allah ya gafarta mishi". Sunkuyar da kai suka yi sannan suna amsa da Insha Allah.
*
Bayan tafiyar su da Gidado ta turawa Chiroma boyayyen sako ta hanyar gaya mishi Waziri zai zo daukar fansa. Dan haka shiga shirin ko ta kwana, ya haɗa kansu fada sannan ya koma gefe yana kallon su,haka ce ta faru ranar a daren Waziri ya kai hari gidan Chiroma, sannan Sarkin gida suka kai hari gidan Barkindo. A hankali yake Bin tsarin, da idanun shi yana jin yadda masarautan ya kaure sannan ya zuba dakarun da suka yi mishi mubaya'a, kafin ya koma ya zauna yana jinjina kome da ya tsara.

Sai da aka kusan ritsa Barkindo sannan ya shiga bangaren su ta kofar baya yayi kokarin ceton su, sai da aka yanke shi a damtse suka samu guduwa, kafin dakarun shi suka kama su Sarkin gida.
A gaban Barkindo aka gurfanar da su.
"Waye ya aiko ku?"
"Waziri Zakaria, yana gidan Chiroma ya tafi kashe su"
"Gidado zaka iya zuwa?"
"Allah ya baka nasara me zai hana?"
A tare da wasu dakaru suka tafi gidan Chiroma, suna zuwa suka samu an cinnawa gidan wuta, waziri Zakaria da wasu dakarun shi.
"Ku kashe su, shi kuma ku kama shi"
"A'a Barkindo, karka min haka sabida kai nayi haka."
"Kuje a kai shi haramtacciyar sashi a daure shi, sannan nan da gobe zamu gurfanar da shi a cikin fada "

Sannan ya wuce. Koda suka koma gida Bingel da bata da wadataccen lafiya, tana ganin shi ta ce mishi.
"Basu maka kome ba?"
"Eh muje" kallon ta Gidado tana karantar razanar ta, tun farko haka baffa'm shima yaso yayi amfani da Barkindo, amma ganin Lamido sai yayi tunanin zai iya nasarar akan su, da salon yaki lumshe idanun Gidado yayi cikin tsannanin tsana ya kalli Waziri ya girgiza mishi kai lokacin da aka tafi dashi.
Luuuu Gidado yayi zai fadi suka tare shi suka nufi masarautan da shi.
Zaka dauka da gaske ciwon ne nan kuwa duk cikin salon aikin ne, haka suka shiga da shi, hankalin Baffa'm ya tashi, dakyar ya raka Barkindo sashin su da aka gyara ko ina, shi kuma ya dawo ya samu abin mamaki.
"Na wanke masarautar daga daud'a gobe Insha Allah akan idanun Zakaria zai amshi hukuncin shi, Baffa'm mutum Mugu ne" nan ya labarta mishi abinda ya faru,zama yayi ya fashe da kuka, kamar ran shi zai fita. Dakyar ya rarrashe shi.

Haka suka kwana a wurin qashin gari ana sallah asuba, aka nufi fada musamman wadanda basu san kome ba, haka suka tattauna har gari ya waye, aka koma sai da hantsi aka taru a fadar nan anan aka shigo da Sarkin gida da Waziri, Lumshe idanun Gidado yayi yana jin wani irin tsanar su kamar ya saka takobi ya sare yan banza, dauke kai yayi sannan ya cigaba da sauraron kafin ya mike tare da kawo wasu bayanai da suka kusan girgiza fadar har shi kan shi barkindo ya mike na kome bane ya faru sai shigowar wasu mutane uku maza biyu mace daya, suka zube a gaba kowa.
"Allah ya baka nasara, shekaru talatin da biyu lokacin da aka gyara dakin da zaa saka Fulani Aminatu, wadanna bayin Allah sune suka yi aikin, ko Baffa'm, sarkin gida, Galadima marigayi waziri Zakaria! Galadima baya raye ko ha haka aka yi ba bayin Allah?"
"Haka ne yarima Hussain!" Mutanen.suka bada amsa.
Damke hannun shi yayi yana jin wani irin daci a ran shi.
"Malam barau gaya min me ya faru?"
"Allah ya baka nasara, bayan an mu gama kome ne aka sarkin gida ya fita damu daga masarautar har mun fita sai aka tare mu, a cikin mu shida da muka yi aiki aka kashe uku sannan suka ce inji Sarki Bello tare da waziri"

Wani boyayyen murmushi Gidado yayi sannan ya ce.
"Ina jin ka ai ba a nan ya kare ba!"
"Sai suka ce zasu taimaka mana mu dauki fansa, amma sai mun bar garin, anan muka bar garin na tsawon shekaru uku, muka dawo a lokacin an kawo farmaki za a tafi da Aminatu muka dawo amma sarki Bello ya kare ta daga sharrin waziri da Sarkin Gida, domin a lokacin me gaskiyar da yake tare da shi Galadima, kuma Alhamdulillahi ya kare shi "
Lumshe idanun Baffa'm yayi hawaye na zuba a idanun shi.
"Malam Sani ina jinka?" Inji Gidado,
"Wato duk wani sharrin da ake kullawa a masarautar nan Waziri ne, shi ya hada kai da mutanen Sahil su dauke Amunatu sannan ya kashe Jakadiya rama, ya kashe sankira da Sanda, abu me ciwo shine kashe mahaifin shi da yayi, domin shi ya kashe mahaifin shi sannan ba zan iya fadar kome na wannan matar zata fada "
"Muna jinki tabawa!"
"Wato Allah ya kiyashe mu da aikin danasani Ubangiji ya kare zuciyar mu daga aikin asha ko shi sarkin Bello yasan kome shi da Fulani Aminatu, amma saboda rashin haihuwa yasa suka dauki haka a matsayin kyautar da ba zasu iya mai dawa ba, Amma abin da tashin hankali na iya fadin Sarki Barkindo Yazidu shege ne domin ba jinin Bello ba ne dan Waziri...
KUYI HAKURI MUNA BIKI NE INSHA ALLAH ZAMU KARASA

KALLABI..! A tsakanin Rawuna...Where stories live. Discover now